JARUMIN Kannywood kuma furodusa, Ali Rabi’u Ali (Daddy), ya aurar da babbar ‘yar sa, wato Saudat.
An ɗaura auren Saudat (Islam) da abin ƙaunar ta, Abdulbasid Salisu Abdullahi, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a jiya Lahadi a masallacin Khalifa Sheikh Ishaq Rabi’u da ke Goron Dutse, Birnin Kano, a kan sadaki N70,000.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alh

aji Abba El-Mustapha, jarumi Alhassan Kwalle, mawaƙi Mudassir Ƙasim, Ahmad Bifa da Isma’il Khaleel Ja’en.
Kamar yadda mahaifin amaryar ya shaida wa mujallar Fim, ba su yi wani taro da ya haɗa maza da mata ba.
A ranar Alhamis an yi karatun Alƙur’ani tun daga safe har dare, a ranar Juma’a kuma an yi gaɗa, sannan a ranar Asabar kuma aka yi kamu.
Bayan an ɗaura auren, mahaifin amaryar da kan shi tare da mahaifiyar ta su ka ɗauke ta zuwa ɗakin mijin ta.
Ali Rabi’u ya yi wa ‘yan’uwa da abokan arziki godiya, inda ya ce, “Assalamu alaikum wa rahmatullah. Alhamdu lillah! Ina miƙa saƙon godiya da bangajiya bisa taya ni murnar auren ‘ya ta.
“Ina godiya ga waɗanda su ka halarci ɗaurin auren, da fatan kun koma gida lafiya. Haka waɗanda su ka turo da saƙo da waɗanda su ka yi addu’ar fatan alkhairi.

“Na gode ƙwarai. Allah ya saka da alkhairi ga waɗanda su ka bani gudunmawa ta lafiyar su ko addu’a ko kuɗi, Allah ya sa a mizani, Allah ya bar zumunci. Na gode ƙwarai. Amarya da mahaifiyar ta na ƙara yi muku godiya.”
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.