BABBAR Kotun Tarayya mai lamba ta 1 da ke Kano ta yanke wa shahararren ɗan TikTok ɗin nan Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, fitacce mawaƙi Hamisu Sa’idu Breaker Ɗorayi hukuncin ɗaurin watanni biyar ko biyan tara ta N200,000 kowanne su, bisa samun su da laifin wulaƙanta takardar naira.
Shi dai G-Fresh, Hukumar Yaƙi Da Almundahanar Kuɗi (EFCC) ta gurfanar da shi ne a gaban kotun bisa zargin watsa takardun naira dubu-dubu a cikin wani shago mallakin sananniyar jarumar TikTok Rahama Sa’idu da ke unguwar Tarauni, Kano, yayin da suke nishaɗi.
Bayan an karanta masa tuhumar, ya amsa laifin sa nan take, lamarin da ya sa Mai Shari’a Sale Musa Shu’aibu ya yanke masa hukuncin ɗauri ko tara.
Kamar yadda ta faru da G-Fresh, shi ma Hamisu Breaker, EFCC ɗin ce ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Sale Musa Shu’aibu bisa zargin wulaƙanta kuɗi.
Shi ma bayan an karanto masa laifin, nan take ya amsa, kotun kuma ta yanke masa hukuncin ɗaurin wata biyar ko biyan tarar N200,000.
An kama Breaker ne da watsa takardun naira ‘yan ɗari biyu-biyu har na naira dubu talatin a gidan biki a Haɗeja, Jihar Jigawa.
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi ke ƙara ɗaukar matakai na hana take haƙƙin naira da kuma yaɗa abubuwan da ke rage mata kima a idon al’umma.