BAYAN an shafe tsawon kwana biyar ana gudanar da tarurruka da shagulgula, a jiya Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022 aka kammala Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), kashi na 5.
An kammala bikin tare da raba kyaututtuka ga masu finafinan da su ka yi nasara a gasar tare da karrama wasu fitattun mutane da su ka bayar da gudunmawa ga cigaban al’umma da kuma al’adun ƙasashen Afrika.
Tun daga rana ta farko da aka buɗe taron, wato talata 22 ga Nuwamba, aka shiga jerin abubuwan da aka tsara a bikin.
Daga cikin abubuwan da aka gudanar, an yi horaswa kan dabarun ayyukan da su ka shafi harkar fim kamar ba da umarni, rubutun labari, ɗaukar hoton fim, editin da kuma tace murya.
An yi tsawon kwana uku ana yi a Digital Bridge Institute da ke Titin Filin Jirgin Sama.
Bayan haka, an gudanar da taron sanin makamar aiki na kwana biyu a otal ɗin Tahir, wanda aka kira da ‘Master Classes’, inda a nan ma ƙwararru a kan harkar fim na duniya su ka bayar da ilimi a game da sana’ar.

An gudanar da babban taro a Sashen Koyar Da Aikin Jarida na Jami’ar BUK inda masana su ka gabatar da maƙaloli da laccoci.
Sannan an shirya baje-kolin abincin gargajiya na Afrika, wato ‘African Kitchen’, inda aka baje abinci kala-kala domin mahalarta tare kuma da wasu zane-zane da kayayyakin gargajiya na nahiyar.
A tsawon kwanakin da aka yi ana gudanar da wannan taro, an ware lokaci na kallon finafinan da su ka shiga wannan gasar inda a ke zuwa Film House da ke Shoprite daga misalin ƙarfe 7 na yamma a kowace rana domin kallon da kuma yin tambayoyi ga masu fim ɗin a kan abin da mutane su ka gani a fim ɗin.
Sannan an shirya yawon buɗe ido ga mahalarta taron, inda aka zagaya da su domin su ga yadda garin Kano ya ke ta fuskar addini, al’adu da kasuwanci.
A daren jiya da aka yi taron kammala bikin an gabatar da waƙoƙin al’adun Ibo, Yarabawa da Hausawa.
A raba kyaututtuka ga masu finafinan da su ka yi nasara da kuma mutanen da su ka samar da cigaban masana’antar finafinai ta Afirka.
Da ya ke jawabi a wajen rufe taron, shugaban shirya taron, Malam Abdulkareem Muhammad, ya nuna farin cikin sa da kuma godiyar sa ga Allah da ya bayar da damar da aka gudanar da taron har karo na 5 ba tare da tsayawa ba.”
Ya ce: “Tsawon shekaru biyar da mu ka yi, duk da a shekaru biyu aka yi na korona, mun yi taron ne ta allon ga ni ga ka, amma dai an samu nasarori, don haka ne ma abin ya kawo har yanzu.”
Ya ci gaba da cewa, “A can baya duk da yake mun kira taron na Afrika, sai ya zama na gida Nijeriya su ke shiga. Amma a yanzu an samu cigaban da ƙasashen Afrika da dama sun shiga cikin wannan taron wanda a yanzu mu na da baƙi daga ƙasashen Afrika da dama.
“Saboda haka mu na godiya a gare su da kuma dukkan mutane da ƙungiyoyi da kamfanoni da su ka bayar da gudunmawa don ganin wannan taron ya kammala.”
Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, wanda Turakin Bichi Alhaji All Ado Bayero ya wakilta, ya yi kira ga jama’a da su koyi ɗabi’ar riƙo da al’adun su da kuma yaren su.
A cewar sa, “A yanzu an kai wani lokaci da yara su na tashi da Turanci; sai ka ga yaro ɗan sakandare, amma ya kasa faɗar wani abu da Hausa.

“Don haka dole sai mun dawo yin amfani da yaren mu ta hanyar koyar da matasa a cikin littattafai da finafinan mu. Don haka ina kira ga wannan taro da ya samar da wani tsari na koyar da matasa yin amfani da al’adu da kuma yaren Hausa.”
An kammala taron lafiya yayin da mahalarta ke fatan wanda za a shirya a shekara mai zuwa ya fi wanda aka yi a bana.

