A daidai lokacin da taron bajekolin finafinai da kalankuwa na Afirka (KILAF 2024) yake gabatowa, masu ruwa da tsaki akan shirya taron sun yi zama da wakilan Gidan Buɗe Ido na Ƙasa wato (NGA) don tattauna batutuwan haɗin-gwiwa wajen shirya taron na wannan shekarar.
A taron ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwar da aka gudanar a ranar 17 ga Oktoban 2024 a ofishin Movie Image dake kan titin Zaria a birnin Kano, an tattauna kan yadda haɗin gwiwar zata kasance tun daga farkon taron har zuwa ƙarshen sa da kuma irin rawar da NGA ɗin za su taka a wajen gudanar da taron.
Abdulkareem Mohammed wanda shine Shugaban shirya taron a duk shekara, ya bayyana tattaunawar da cewa ta cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu don gudanar da wannan gagarumin taron KILAF da za a yi daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2024 a Kano.
Ya ƙara da cewa “Kawo yanzu KILAF da NGA sun cimma matsayar inganta harkokin al’adu da wasu sana’o’in hannu da al’umma suka dogara dasu, domin ilimintar da mahalarta taron da za su zo daga ƙasashe daban-daban na duniya.”
Aƙalla dai baƙi daga ƙasashe 66 ne ake sa ran za su halarci wannan bikin don bajekolin al’adunsu a yayin taron inda za a ɗauki tsawon kwanaki biyar ana yi.
Wannan dai wata alama ce dake nuna cewa KILAF na samun cigaba ta fuskar ayyukanta da kuma inganta harkokin al’adu a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya.