• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kiran mawaƙi Auta Waziri ga abokan sana’ar sa: kada mu dogara da waƙa ita kaɗai

by DAGA ABBA MUHAMMAD
July 28, 2023
in Mawaƙa
0
Abdullahi Abubakar (Auta Waziri)

Abdullahi Abubakar (Auta Waziri)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘI a Kannywood, Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Auta Waziri, ya yi kira ga abokan sana’ar sa da kada su dogara kacokam da harkar waƙa, amma su riƙa haɗawa da ‘yan sana’o’i.

Auta ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke bayyana wa mujallar Fim dalilin sa na buɗe gidan ɗaukar hoton kati da kuma wurin shaƙatawa.

A tattaunawar sa da wakilin mu, fitaccen mawaƙin wanda ke zama a Kaduna ya ce: “Gaskiya, alal haƙiƙa duk wanda ya san ni, ya san ina da sha’awar kasuwanci, saboda mahaifi na ɗan kasuwa ne. Ya yi karatu duk irin karatun da ake so, digiri da sauran su, amma kuma ɗan kasuwa ne. To kuma Allah ya yi masa rasuwa. 

“Don haka kasuwanci ina jin sa a jiki na ne, shi ya sa ka ga ina yi. Wannan wurin shi ne na biyu, domin mu na da ‘Diamond Star Photos’, sannan sai kuma ‘Diamond Star Resort’. Ni haka na ke, ina da plan ɗin bizines gaskiya.

Wajen cin abinci (a sama) da kuma ɓangaren wasan sunuka na Auta Waziri a Kaduna

“Wannan wuri da mu ka buɗe, mun buɗe shi washegarin Babbar Sallah ne, inda aka yi kwanaki uku ana wasan Sallah a harabar wurin. Manya da ƙananan mawaƙa da ‘yan fim sun halarci wasan Sallar.”

Ya lissafa abubuwan da ake yi a ‘Diamond Star Resort’ kamar haka: sun haɗa da gidan abinci, wanda ana yin kifi, shayi, chifs da ƙwai, kaza, indomie, abubuwan sha dai duk wasu kayan maƙulashe.

“Sannan akwai ɓangaren da ake wankin mota, wurin wasanni irin sunuka, ana yin taron bikin aure, bikin suna, murnar zagayowar ranar haihuwa da sauran ‘shows’.  Za kuma mu ƙara buɗe wasu wuraren a nan gaba da za mu kawo sababbin abubuwa.

“Zuwa yanzu akwai ma’aikata a ƙasa na daga ‘Diamond Star Photos’ zuwa ‘Diamond Star Resort’, sun kai mutum goma sha biyar.

“Wurin ɗaukar hoto na Ƙofar Gamji, wurin shaƙatawar kuma na nan a kan Titin Swimming Pool, kafin ka ƙarasa Ƙofar Gamji.”

Wajen wankin mota na mawaƙi Auta Waziri

A nan ne Auta Waziri ya yi kira ga abokan sana’ar sa da kada su mayar da hankali a kan harkar waƙa kawai. 

“Mu yi ƙoƙari mu na haɗawa da kasuwanci, domin da harkar waƙar za ka taimaki kasuwancin ka,” inji shi.

Ɗan kasuwa kamar wani sarki! Auta Waziri

Loading

Previous Post

Gwamnatin Kano ta soke lasisin duk masu gudanar da harkar fim

Next Post

‘Yan Kannywood sun kaɗu kan mutuwar auren Hafsat Idris da na Zahra’u Shata

Related Posts

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Next Post
Hafsat Idris (a hagu), da Zahra'u Shata

'Yan Kannywood sun kaɗu kan mutuwar auren Hafsat Idris da na Zahra'u Shata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!