A JIYA Talata aka tura shahararriyar ‘yar Tiktok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya gidan yari a Kano a bisa umurnin kotu.
Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaman ta a unguwar Gama PRP, Kano, ta ce a tsare ta ne bisa tuhumar da Hukumar Hisbah ta shigar inda ta zarge ta da aikata laifuffukan da suka haɗa da kawo ɓata-gari cikin dare, aikata baɗala, tada hatsaniya da kuma razanarwa.
Laifuffukan sun saɓa wa sashe na 341, 275 da 227 na kundin finalkod.
Tun da farko dai, jami’an Hukumar Hisbah sun cafke Murja bayan wasan ɓuya da suka yi da ita a sakamakon shelar neman ta da suka yi, sakamakon wasu ƙorafe-ƙorafe da wasu mazauna unguwar Tishama a Kano inda Murja ɗin take da zama suka yi kai wa Hisbah.
A kotun, an karanta wa Murja tuhumar zargin, ita kuma ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.
Lauyan da ke kare ta, Barista Aliyu Umar, ya roƙi kotun da ta bayar da belin ta, dogaro da sashe na 35 da 36 na dokokin ƙasa, da kuma sashe na 168, 172 da 173 na finalkod.
‘’A sanya ta a hannun beli saboda hurumi ne na kotun, sannan idan ta bayar da belin ta ba za ta gudu ba ko aikata wani laifi da ya saɓa da doka,” inji shi.
Lauyan gwamnati da ya wakilci Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Aminu Umar, bai yi suka a kan roƙon lauyan wadda ake tuhumar ba.
Ya ce, “Ba mu da suka a kan wannan roƙo domin bayar da beli hurumin kotu ne,’’ inji shi.
Sai Mai shari’a Malam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadda ake zargin a kurkuku har zuwa ranar 22 ga Fabrairu domin ci gaba da shari’ar.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Hukumar Hisbah ta gurfanar da Murja a gaban ƙuliya, domin ko a shekarar da ta gabata ma sai da ta gurfana a gaban kotu inda a wancan lokacin har aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari tare da horo na aikin yin sharar masallaci.