• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kyakkyawar mu’amala da mutane ce ginshiƙin nasara ta a fagen waƙa – Hajara S. Umar

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 7, 2022
in Mawaƙa
0
Hajara S. Umar

Hajara S. Umar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAGWARIYA ce, amma da wuya ka iya doke ta a fagen waƙar Hausa. Hajara S. Umar, ɗaya daga cikin mawaƙa mata da tauraruwar su ta fara haskawa a harkar waƙa yanzu, musamman a Kaduna, ita ce mawaƙiyar da ta fi sauran mawaƙa mata da ke Kaduna yawan samun aikin amshi. Dalili shi ne Allah ya ba ta nasibi, sai kuma ta yi sa’a, sauran manyan mawaƙa mata sun ɗan ba ta fili a Kaduna. Misali, Fati Khalil da ta koma Kano gaba ɗaya da aiki, Hairat Abdullahi da Zubaida Mu’az (Zubby) kuma ba su cika zama a Kaduna ba. Wannan ya ba Hajara damar cin karen ta babu babbaka.

Hajara yarinya ce mai ladabi da biyayya ga duk na gaba da ita. Mujallar Fim ta zanta da mawaƙiyar inda ta yi mana bayani kan yadda ta fara waƙa, wanda ya kawo ta harkar waƙa, waye ubangidan ta da sauran su.

FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin ki a taƙaice.

HAJARA S. UMAR: Assalamu alaikum wa rahamatullah. Ni dai suna na Hajara S. Umar. An haife a garin Kuta da ke Jihar Neja. Ni Bagwariya ce.

Na yi makarantar firamare na a Maitumbi Primary School, sannan na yi sakandare na a Maitumbi Secondary School. Daga nan sai na je na yi difloma a ɓangaren aikin jarida, wato ‘Mass Comm’, a Fati Lami Abubakar College for Legal And General Studies, Minna.

FIM: Ashe dai ke ‘yar jarida ce!

HAJARA: E, ni ‘yar jarida ce.

FIM: Ki na aikin jaridar

HAJARA: Na yi ta nema ban samu ba, kawai sai na shiga waƙa.

FIM: Ya aka yi ki ka tsinci kan ki a harkar waƙa?

HAJARA: Da ya ke ni yaren Gwari ce, amma daidai gwargwado na tashi a cikin Hausa, ina jin yadda ake ‘communicating’, kuma na tashi a cikin Hausawa. A da ba na sauraren waƙoƙin Hausa, to daga baya sai na zo ina sauraren waƙoƙin Umar M. Shareef saboda su na yi min daɗi. A haka sai na fara samun sha’awar abin, kuma da ma idan ina sauraren waƙar ina rerawa, idan ina bi sai in ji kamar da ni aka yi waƙar. Wata rana sai na yi tunanin wataƙila akwai wata baiwa tare da ni a cikin wannan al’amari, bari in je in gwada wannan abu ko zai sa in iya ko za a fafata da ni. Haka na zo na shiga aka fara da ni a hankali.

A nan Kaduna na fara, sannan kuma na koma Kano na zauna na ci gaba da waƙar har dai na kawo wannan matakin.

FIM: Waye ya yi maki jagora don ganin kin samu shigowa harkar?

HAJARA: Da farko dai a nan Kaduna, akwai wani da ake kira Musty, aikin shi cigaban shiri ne a Kannywood. Mu na magana da shi, sai na ke ce masa ko ya na da situdiyo da zai kai ni a nan Kaduna. Kuma da ma na san cewa Umar M. Shareef a Kaduna ya ke; kawai ma sai na ce masa ya kai ni situdiyon Umar M. Shareef don Allah, ina so in fara zuwa gwada harkar waƙa. Sai ya ce min ba matsala. Haka kuwa aka yi. Nan ya kai ni na fara kaɗan-kaɗan. Cikin ikon Allah kuma na ƙara samun wani situdiyon na ci gaba da zuwa. Haka kuma da ma ina da wani a Kano, mu ka yi magana da shi na ce masa ina so in zo Kano in ci gaba da aiki. Shi ma ya ce ba matsala. Kuma da ma harkar a can ma ta fi tafiya. Ina so in ƙara gogewa. A nan ya kai ni situdiyon I.B.Y. a nan Rima House, nan kan Zoo Road. A nan ma dai zan ce na fara ‘voicing’.

FIM: Wanene ubangidan ki a harkar waƙa a yanzu?

HAJARA: Gaskiya ni na ɗauki dukkan wani da ke gaba da ni a harkar nan a matsayin ubangida na. Amma dai ina da ubangida wanda shi ne na fara zama a wurin shi, wato Sani Ceevee. Sai kuma a yanzu Allah ya haɗa ni da Umar M. Shareef, tunda a yanzu ina aiki tare da shi, shi ma zan iya cewa ya zama ubangida na. 

Sannan akwai mutane da yawa, irin su Ibrahim Lankasta, Ibrahim Al-Imash, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Waza-Waza, Lukman, Suleiman Sukus, da dai sauran. 

FIM: Wace waƙa ce ki ka fara rerawa?

HAJARA: Na fara ne da wata waƙar soyayya a Kano. A yanzu ni waƙar ta shige min, ba zan iya tuna sunan ta ba, ba ni da ita ma kwata-kwata. 

Hajara S. Umar tare da ɗaya daga cikin iyayen gidan ta, Ɗanladiyo Mai Atamfa

FIM: A ɓangaren ki kuma fa? 

HAJARA: A ranar da aka ce in rubuta waƙa, sai na fara tunanin ta ina zan fara ƙirƙirar waƙa, zan iya kuwa? A haka dai na yi ƙoƙari har na cire karin amshi. Cikin ikon Allah, sai ban samu na yi waƙar a lokacin ba, amma kuma har an yi min kiɗa.

FIM: Zuwa yanzu kin yi waƙoƙi za su kai guda nawa?

HAJARA: Waƙoƙi nawa na kai na da na yi, zan iya cewa za su kai ashirin.

FIM: Da wane makawaƙi ki ka fi son ki yi waƙa fitacciya?

HAJARA: To, kada dai a ce na yi son kai, amma kuma gaskiya zan faɗa, kuma har cikin zuciya ta Umar M. Shareef, saboda da ma tun farko kamar yadda na faɗa a kan waƙoƙin sa ne na shigo harkar nan.

FIM: Yanzu aƙalla waƙoƙin da ki ka yi amshi na mutane za ki iya faɗin yawan su?

HAJARA (dariya): Gaskiya ban sani ba wallahi, saboda abin da yawa.

FIM: A yanzu a Kaduna ana cewa duk da yake akwai mawaƙa mata, amma babu wacce ta kai ki samun ayyukan amshin waƙoƙi a situdiyo daban-daban. Haka ne?

HAJARA: Alhamdu lillah. Da farko dai dole in yi godiya ga Allah. Tabbas, wannan magana haka ta ke, gaskiya a garin Kaduna a yanzu ni ma ina da shaidar haka. Saboda a duk lokacin da Allah ya yi maka, ka nuna ya yi maka, kuma sai ka gode masa. A garin Kaduna yanzu, ni na ke yawo sosai a cikin mata masu amshi, sakamakon hakan murya ta na yawo, ta na zuwa inda ma ni ban taɓa zata ba. Sanadiyyar hakan kuma ya sa na ke samun haɗuwa da wasu manyan mawaƙa waɗanda su ke cikin harkar nan, su na kira na ina ɗora masu aiki. Gaskiya alhamdu lillah.

FIM: Ta yaya ki ke biya wa dukkan wanda ya kira ki aiki buƙatar sa, ganin cewa ayyukan su na yi maki yawa?

HAJARA: A yawon nan da na ke yi, ka san mutane kowa da irin fahimtar sa, sannan kuma aka ce in ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi. Duk da cewa ba za ka iya yi wa mutum abu ɗari bisa ɗari ba, amma daidai gwargwado mu’amalar ka ta kan janyo maka jama’a. In dai ka san yadda za ka yi mu’amala da mutane, ka na da haƙuri, ka na da fahimta ko kuma ka san yadda za ka yi ka bi kowa ka faranta masa rai, duk da ba za ka iya taɓa iya mutum ba, amma ni ina ƙoƙari in ga na faranta wa kowa, babu wani abu na cin mutunci ko kuma na rashin jin daɗi. In ka kira ni ba ni da lokaci zan ba ka haƙuri, sannan in tambaye ka ko za ka iya jira na zuwa lokaci kaza in zo in ɗora maka aikin ka. Da ma haka rayuwa ta ke; in Allah ya kai ka wani mataki, ya zama dole ka san yadda za ka bi da mutane da kuma yadda za ka yi magana da su.

FIM: An ce a Kaduna ba a biyan ku kuɗin amshi yadda ya kamata. Ya ki ke yi wurin biya?

HAJARA: Alhamdu lillah, zai iya yiwuwa haka ɗin ne ba a biya ɗin kamar yadda ya kamata. Amma kuma ai ba duka ba ne, saboda ba ma a harkar nan kawai ba, a kowane irin harka ana iya samun irin waɗannan matsalolin. Misali, ko aikin gwamnati sai a ɗauki wasu watanni ba a biya albashi ba, haka abin ya ke faruwa. To amma na ɗauke shi dai ‘normal’, duk da dai wani lokacin za ka ji ka na buƙatar kuɗin, sai ka je kuma ba haka ba, wani ma za ka iya zuwa ya ba ka haƙuri ba shi kuɗi, wani ma tun kafin ka zo zai sanar da kai, amma dai zai ba ka kuɗin mota. Amma abin da na ke so mutane gaba ɗaya su gane, idan ka kira mai aiki ko ba a cikin wannan harkar ba ma, in ka kira mutum tunda ka san haƙƙin sa ne za ka ba shi idan ya yi maka aiki, za ka iya faɗa masa tun a waya kafin ya iso: “Wance ina so ki zo ki min aiki, amma ba ni da kuɗi.” Ai an ce magana mai daɗi ma sadaka ce. In ka faɗa wa mutum haka, zai fahimta. Wani kuma idan ya kira ka zai riƙa nuna maka gadara, ba zai maka magana mai daɗi ba, sai ma ya riƙa ya na nuna maka shi taimaka maka ya ke yi. Ko da a ce koya maka ya ke yi bai kamata ya yi maka haka ba. Sai ka yi wa mutum magana mai daɗi. A haka za ka ga komai na tafiya yadda ake so.

FIM: Waɗanne irin ƙalubale ki ka fuskanta daga lokacin da ki ka shigo harkar nan zuwa yanzu?

HAJARA: Alhamdu lillah ƙalubale kam sai dai a ce Allah ya ƙara tsare gaba. Amma ƙalubale a kowane irin harka dole mutum ya fuskanci ƙalubale. Da ma ƙalubale in dai mutum ya zama mai jajircewa dole ya fuskanci ƙalubale. Amma dai mutum kawai ya manta da shi, domin ƙalubale a rayuwa jarabta ce daga Allah. Amma idan na zo ina cewa abu kaza da kaza sun faru, kamar ina ja da Allah ne.

FIM: A ɓangaren nasarori fa?

HAJARA: Masha Allah. Da farko mu’amala ta da mutane, wannan shi ne babban nasara ta a rayuwa. Yadda Allah ya ba ni hikimar zama da mutane lafiya, duk da dai ba ka iya wa mutum, amma wannan ita ce nasara ta ta farko. Na biyu, ina yin aiki na hankali na kwance. Na uku, ban shiga haƙƙin wani ba, kuma ba zan ce wani ya shiga haƙƙi na ba. Waɗannan abubuwan su ne nasara na na farko, kuma su ne za su kai ni gaba, kuma ga shi su na kai ni gaba, domin ina haɗuwa da mutanen da ban taɓa tsammani ba.

FIM: Ga ki Bagwariya, ki na waƙa da yaren ki?

HAJARA: Gaskiya ba na yi, amma dai na taɓa yin guda ɗaya.

FIM: Ke ma rubuta maki waƙa ake yi kamar yadda ake yi wa sauran mawaƙa mata ko ke ki ke rubutawa da kan ki?

HAJARA: Gaskiya ina ƙoƙarin rubutawa da kai na, idan na rubuta sai in kai wa waɗanda su ke gaba da ni su duba min, in da kuskure a yi min gyara. Amma kuma akwai waɗanda ba ni na rubuta su ba, rubuta min aka yi.

FIM: Wace waƙa ce a cikin waƙoƙin ki ki ka fi so?

HAJARA: Wata waƙa ce ta ‘Mahaifiya’. Har yau waƙar nan ta na cikin rai na, kuma ba zan taɓa mantawa da ita ba.

FIM: Mun gode.

HAJARA: Ni ma na gode.

Loading

Tags: amshiBagwariyaƊanladiyo Mai AtamfaFati KhalilGwariHairat AbdullahiHajara S. UmarKadunamawaƙaMinnamu'amala.Umar M. ShareefZubaida Mu'az.
Previous Post

Ali Nuhu, Daddy Hikima da Ali Jita sun zama jakadun kamfanin sufuri

Next Post

Labarin dukan malamar Islamiyya: Ƙullalliya aka shirya mani a unguwar mu – Baba Ari

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Aminu Baba Ari cikin shigar sa ta dirama

Labarin dukan malamar Islamiyya: Ƙullalliya aka shirya mani a unguwar mu - Baba Ari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!