• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Labarin dukan malamar Islamiyya: Ƙullalliya aka shirya mani a unguwar mu – Baba Ari

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
October 11, 2022
in Labarai
2
Aminu Baba Ari cikin shigar sa ta dirama

Aminu Baba Ari cikin shigar sa ta dirama

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN barkwanci Malam Aminu Baba Ari ya bayyana cewa dukan malamar Islamiyya da ake zargin sa da aikatawa wata ƙullalliya ce wani gungun mutane su ka kitsa a unguwar su.

Ya ce bai san abin da ya sa su ka tsane shi ba.

Baba Ari ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke ƙarin bayani kan labarin cewa ya doki malamar Islamiyyar da ‘yar sa ke halarta har ta suma.

Idan kun tuna, mujallar Fim ce ta soma buga labarin, bisa wani bincike da ta yi kan zargin da ake masa.

A labarin, wanda mu ka buga a ranar 6 ga Oktoba, 2022, mun ruwaito wata malamar makarantar Islamiyya da ke unguwar Mubi, kusa da Ƙofar Nassarawa a cikin birnin Kano, ta zargi Baba Ari, da yi mata dukan tsiya kuma yi barazanar zai taka ta da takalmi.

Malamar, mai suna Zainab, ta shaida wa mujallar Fim cewa wasu yaran makarantar ne su ke karatu, a cikin su har da ‘yar Aminu Baba Ari, inda su ka yi laifin da za a hukunta su. To amma kuma da hukuncin ya zo kan ‘yar Baba Arin sai ta riƙe bulalar, ta hana a dake ba. 

A yunƙurin dukan ta ne har ta faɗi ƙasa, aka ce “aljannun ta ne  su ka tashi.”

Baba Ari: “Ba na faɗa da kowa”

Zainab ta ce: “Bayan shi Aminu Baba Ari ya samu labarin, sai ya zo ya rufe ni da duka, har na faɗi ƙasa. Sannan ya yi ƙoƙarin taka ni da takalmin sa.”

A lokacin, Baba Ari ya ce bai yi mata irin dukan da ake cewa ya yi ɗin ba, illa iyaka ya daki ɗankwalin ta baya ne.

A ƙarin bayanin sa kan labarin, Baba Ari ya faɗa wa mujallar Fim cewa akwai ƙarya a labarin da ake yaɗawa.

Ya ce: “Duk da dai na ɗan yi magana a baya, amma a yanzu ina so na yi maka bayanin yadda abin ya faru tun da farko saboda na ji yadda ake ta yaɗa labarai na ƙarya a kai na.

“Ina ganin labarai kala-kala, wasu su ce na yi mata dukan da na sumar da ita, wasu su ce na karya ta, da sauran labarai na ƙarya.

“To, a gaskiya abin da ya faru, ni ban san wannan yarinya malamar Islamiyyar ba ce, domin ƙawar ‘ya ta ce ita wadda aka daka ɗin. 

“Na zo gida na zauna ina cin abinci, sai aka sanar da ni ana faɗa da ‘ya ta A’isha a makarantar, don haka sai na yi sauri na fita na je makarantar. 

“Kuma ina zuwa sai ga wannan yarinya riƙe da bulala, ta na dukan ta, har ta kumbura mata gefen ido. Wannan ya sa na bi wannan yarinya na buge ta ta baya don ta daina. Kuma tabbas na san na bugi gefen mayafin ta.

“Amma ban yi mata dukan da ake cewa na yi mata dukan tsiya na sumar da ita na taka ta da takalmi ba.

“Kuma ni ban yi zaton ta na a matsayin malamar Islamiyyar ba ce; na zata faɗan su ne na yara idan malamai ba sa kusa.”

Baba Ari ya ce wata maƙarƙashiya ce aka ƙulla domin a ɓata masa suna, kuma ‘yan bangar unguwar su ne su ka kitsa maganar.

Ya ce, “To amma duk bayan an yi magana an gama, sai ‘yan bijilanti na unguwa su ka shigo harkar saboda su na da wata ƙulalliya da ni, don haka su ka kira ‘yan jarida su ka tsara mata abin da za ta faɗa tare da kai maganar ga ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam, wai dai su ɓata mini suna.

“Wannan ya sa aka je ofishin ‘yan sanda na Ƙwalli da uban yarinyar, aka kashe magana.”

Ɗan wasan ya ce ba tun yau ba ne ‘yan bangar unguwar tasu su ka kafa masa ƙahon zuƙa, kuma bai san dalili ba.

Ya ce, “Ni ban san abin da na yi wa su ‘yan bijilantin unguwar mu ba su ka tsane ni, saboda sun yi ta ƙokarin yi mini haka a baya ba su samu hanya ba, saboda ina zaune da kowa lafiya. Ga wani nan da aka kama ya doki matar aure har gida ba su yi komai ba; an samu wani ya na luwaɗi, ba su yi komai ba; ga masu laifuka nan. 

“Don ko Mai’unguwar mu da ya ji maganar ya ce abin ya ba shi mamaki, don ba na faɗa da kowa.

“Kuma ita wannan makarantar Islamiyya ina cikin masu ba ta gudunmawa, don a satin da ya wuce makarantar ta ba ni takardar karramawa a taron da ta shirya don karrama masu ba ta gudunmawa.

“Saboda haka, wasu ne dai da su ke da wata manufa da ni su ka shirya yaɗa labarin don a ɓata mini suna. Amma kowa ya san ba ni da rigima a unguwar mu ko a wajen harkar fim da na ke yi.”

Loading

Tags: Aminu Baba AribarkwancibijilantidukaIslamiyyaƘwallimaƙarƙashiyamalamataƙaddama
Previous Post

Kyakkyawar mu’amala da mutane ce ginshiƙin nasara ta a fagen waƙa – Hajara S. Umar

Next Post

Yadda rubutun littafi ya buɗe mini hanyar kasuwancin soshiyal midiya – JUT

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Jamila Umar Tanko (JUT)

Yadda rubutun littafi ya buɗe mini hanyar kasuwancin soshiyal midiya - JUT

Comments 2

  1. Pingback: Kan dukan malamar islamiyya: kullalliya 'yan unguwar mu suka shiryamin, cewar Baba Ari - Kyauta Blog
  2. Pingback: Kan dukan malamar islamiyya: kullalliya ‘yan unguwar mu suka shiryamin, cewar Baba Ari - Mr ATG News.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!