WATA ran mu na tafiya da ɗa na a mota, ina jin ƙauye za mu, akwai wata Ayatulkursiyyu a rataye, irin wadda ake ratayewa a madubin duba baya na tsakiyar motar. Ɗa na sai ya kalle ta, ya ce, “Abba wai me ya sa ake sa wannan?”
“Ayatulkursiyy ce.”
“Me ya sa ake sa ta a mota?”
“Laya ce.”
“Laya fa Abba?”
“E, laya ta zamani ba! Ka san an hana mu ɗaura irin ta fatar nan, an ce kafirci ce. Shi ne aka shigo da dabarun zamani aka dawo da ita ta wannan salon. Ba ka lura ana yin ‘frames’ na ayoyin Falaƙi da Nasi da su Ayatulkursiyyu ba? Ai duk layu ne na zamani!
“A zamanin da, ana rubuta Falaƙi da Nasi a yi laya da su a kafe a soron gida domin neman tsari. Ana samun duma a fasa shi, duk ‘ya’yan da aka samu a cikin sa za a dinga ɗauka ana tofa Ayatulkursiyyu ƙafa ɗaya Laƙad Ja’akuma ƙafa ɗaya a tofa a jiki. Idan an gama za a haƙa rami a tsakiyar gidan a binne ‘ya’yan gaba ɗaya. Yanzu ka ga duk a falo ake sawa; ga su ya Allahu da ake layar maganin tsafi da jifa. Yanzu za ka ga wani ‘frame’ mai Allahu Muhammadu.”
Shi dai yaro ya yi shiru, ya ji karatun ya shige sanin sa.

Na tuna wannan labarin saboda jiya mun je da yaya ta wani wajen sayar da kayayyaki. Sai ga wani ‘frames’ na Suratul Falaƙ. Kuɗin shi naira dubu ɗari da hamsin. Ka ga maimakon Alaramma ya karɓi ‘yar ɗari biyu, baduku ya karɓi ɗari na rufa layar, ga shi za mu ba Larabawa ɗari da hamsin kuma ‘services’ ɗin ɗaya ne.
Na taɓa faɗa wa wani wannan maganar cewa laya ce da dabara. Ya kama musu.
Na ce masa, “Wanene ya sa ka yi ado da ayoyi a ɗaki ko ka rataya a mota ko kuma ka sanya a ofis? Ofis nawa za ka shiga ba ka ga Alƙur’ani ba, amma sai ka ga an rataye wata aya? Kuma duk ayoyin da za ka ga ana kafewa ko ratayawa, ayoyi ne da su ke alaƙa da tsari ko kariya. Ayoyi ne irin dai waɗanda alarammomi masu laya ke yin laya da su.
“Idan har rataya laya zai zama kafirci, to rataye ta a mota ko bangon ɗaki ko na ofis ya kamata ya zama kafirci.
“Ina maganar ratayewa da kafewa ba ta’allaƙa samun nasarar a layar ba. An kori kare daga bakin ɗinya!”
* Malam Auwal Garba Ɗanborno marubuci ne mazaunin Kano