FITACCEN mawaƙi Adamu Hassan Nagudu shi ma ya shiga jerin ‘yan fim da aka naɗa sarautar waƙa kamar yadda mawaƙa da jaruman fim su ke rabauta da naɗin sarauta daga wasu sarakunan ƙasar nan.
Mawaƙin ya samu wannan naɗin ne a Masarautar Borgu da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, inda Sarkin Borgu Alhaji Muhammad Sani Haliru Ɗantoro Kitoro IV ya naɗa shi a Sarkin Waƙar Masarautar Borgu.
An yi naɗin rawanin ne a ranar 19 ga Agusta, 2019 a garin Borgu a wani ƙasaitaccen bikin Sallah da masarautar ta saba shiryawa a duk shekara inda ake gayyatar mawaƙa da sauran masu wasannin gargajiya daga ko’ina a faɗin ƙasar nan.
Da mujallar Fim ta tambayi Adamu Nagudu yadda ya ji game da wannan naɗi da aka yi , sai ya ce, “Mai Martaba Sarki ya ce ya yi mini wannan haɗin ne saboda alaƙa ta da masarautar tsawon lokaci, don ina tare da masarautar tun lokacin mahaifin sa ya na sarki, kafin Allah Ya yi masa rasuwa, kuma har yanzu alaƙa ta da masarautar ta na nan, sai ma ci gaba da ta yi. Don haka na kan je na yi gaisuwa, kuma duk Sallah na kan je a yi bikin Sallah da ni. Don haka ina godiya ga masarautar bisa karrama ni da ta yi, ta ba ni sarautar Sarkin Mawaƙan Borgu.”
Da man dai ba wannan ba ne karo na farko da masarautar ta ba wani mawaƙin sarauta, domin kuwa idan kun tuna shekara uku da su ka wuce mun ba ku labarin naɗin Fati Nijar a matsayin Gimbiyar Mawaƙan Masarautar Borgu.