FITATTUN mawaƙa mata na Kannywood sun kafa sabuwar ƙungiya ta mawaƙa mata zalla mai suna ‘Muryar Mawaƙa Mata A Yau Progressive Association’.
Ƙungiyar, wadda aka kafa ta a Kano, ta ƙunshi tsofaffin zabiyoyin Kannywood da su ka haɗa da Murja Baba, Maryam A. Baba (Sangandale), Hadiza Maikano, Maryam Fantimoti, Fati Nijar da sauran su.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan ƙungiyar, Hajiya Maryam A. Baba (Sangandale), ta shaida wa mujallar Fim manufofin ƙungiyar, ta na faɗin, “Ita wannan ƙungiyar sabuwa ce, don ba mu daɗe da kafa ta ba. Kuma mun kafa ta ne domin wayar da kan jama’a da kuma haɗa kai da taimakon juna a tsakanin mu mawaƙa mata.
“Kuma ita wannan ƙungiyar, za mu yi amfani da ita wajen wayar da kan mutane da faɗakarwa. Sannan kuma za nemi kuɗi wajen tallata kamfanoni da sauran kayan sayarwa. Don haka wannan ƙungiyar ta taimakon kai ce da kuma taimakon jama’a.”
A game da tsarin shugabancin ƙungiyar, Hajiya Maryam ta ce: “A yanzu mu na ta ƙoƙarin samar da tsarin ƙungiyar ne da kafuwar ta, don haka mu na da tsarin shugabancin riƙo ne wanda Murja Baba ta ke a matsayin Shugaba ta riƙo, sai kuma Fati Nijar a matsayin Mataimakiyar Shugaba.
“Ku ma mu na fatan wannan ƙungiyar ta zama ta bayar da gudunmawa domin cigaban mawaƙan Kannywood mata har ma da mazan da duk al’umma baki ɗaya.”