• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Idris ya jajanta wa al’ummar Neja da iyalan mutum 59 da suka mutu sakamakon fashewar tankar mai

by WAKILIN MU
September 10, 2024
in Nijeriya
0
Gwamnati ba ta musanya sunan Titin Murtala Muhammed da na Soyinka ba, inji Minista

Ministan Yaɗa Labarai Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a ranar Litinin ya jajanta wa al’ummar Jihar Neja bisa rasuwar mutane 59 a wani haɗarin mota da ya ritsa da su a hanyar Bida-Agaie-Lapai ranar Lahadi.

A cikin saƙon ta’aziyya da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya sanya wa hannu, ministan ya ce lamarin ya girgiza Jihar Neja da ƙasa baki ɗaya.

Ya yi addu’ar Allah ya ba iyalan mamatan ikon jure wannan babban rashin.

Idris ya ce: “Ina miƙa ta’aziyya ta ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja da iyalai, abokai da ‘yan’uwan mutane 48 da suka rasa rayukan su a wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Bida-Agaie-Lapai a Jihar Neja da sanyin safiyar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024.

“Wannan mummunan lamari ya girgiza ɗaukacin Jihar Neja da ma ƙasa baki ɗaya kuma ina yi wa duk waɗanda abin ya shafa a wannan lokaci mai zafi addu’a. Don haka ina taya al’ummar Jihar Neja da ma Nijeriya baki ɗaya alhinin wannan babban rashi.

“Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma Allah ya bai wa iyalan su juriyar wannan rashi mara misaltuwa.”

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), reshen Jihar Neja, Mista Kumar Tsukwan, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa dukkan waɗanda abin ya shafa maza ne, kuma da ba a iya tantance motocin da abin ya shafa ba saboda tsananin ƙonewar su.

Tsukwan ya bayyana cewa lambar mota ɗaya kacal ce aka iya tantancewa, yayin da ba a gane lambobin sauran ba.

Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 4:30 na safe kuma an kai rahoton lamarin ga sashin Lapai na FRSC da ƙarfe 4:40 na safe.

Ya ce: “Motar tankar man da ke ɗauke da mai daga Legas zuwa Kano tana gudu sosai, inda ta ƙwace ta faɗi ta kama da wuta yayin da wutar ta shafi wata tirela da ke ɗauke da shanu da mutane tare da wasu motoci biyu a baya. Dukkan motocin guda huɗu sun ƙone ƙurmus.”

“An ruwaito cewa sai da ɗaya daga cikin fasinjojin tirelar da ke ɗauke da mutane da shanun ya ankarar da direban cewa akwai wuta fa a gaban su amma sai direban ya amsa da cewa taya ce kawai ke ƙonewa, kuma da isa wurin tankar da ke ci da wuta, wutar ta kama tirelar da kuma wasu motoci biyu.”

A cikin wani ƙarin bayani, Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru daga 48 da aka bayyana da farko zuwa 59 saboda an gano wasu gawarwaki wajen ci gaba da ceto yayin da ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa da ya ƙone sosai ya mutu a Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya da ke Bida.

Loading

Tags: haɗarin motajajeMohammed IdrismutuwaNeja
Previous Post

MOPPAN ta kafa kwamitin zaɓe da masu ba da shawara

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Borno kan ambaliyar ruwa

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Borno kan ambaliyar ruwa

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al'ummar Borno kan ambaliyar ruwa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!