• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin ba manoma da mata ‘yan kasuwa 4,000 rancen shirin GEEP 2.0 a Bauchi

by DAGA WAKILIN MU
September 12, 2022
in Nijeriya
0
Minista Sadiya tare da wata mata da aka ba agaji a wajen taron a Bauchi

Minista Sadiya tare da wata mata da aka ba agaji a wajen taron a Bauchi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SAMA da manoma da mata ‘yan kasuwa 4,000 ne su ka fara karɓar bashi maras ruwa a ƙarƙashin kashi na biyu na Shirin Haɓaka Kasuwanci, wato ‘Enterprise Empowerment Programme’ ko ‘GEEP 2.0’ na Gwamnatin Tarayya a Jihar Bauchi.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da ba da rancen a ranar Litinin a garin Bauchi. 

Masu cin moriyar shirin sun karɓi kuɗaɗe da su ka kama daga naira dubu hamsin (N50,000) har zuwa naira dubu ɗari uku (N300,000), kuma ana sa ran su biya rancen ba tare da wani ruwa da aka ɗora ba a cikin wa’adin shekara ɗaya.

A jawabin ta a taron, ministar, wadda kuma ta rarraba agajin tsabar kuɗi ga mutum 5,679, ta yi kira a gare su da su yi amfani da kuɗaɗen wajen yin ƙananan sana’o’i masu riba don inganta rayuwar su.

Ta ce: “Wannan shiri ana aiwatar da shi ne tare da cikakken haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi a matsayin wata kyakkyawar shaida tare da nunin cewa mai girma Shugaban Ƙasa ya sadaukar da kan sa wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa da dukkan matakan gwamnatoci don tunkarar matsalar fatara da yunwa wadda ta zama babban ƙalubalen gina ƙasa da mu ke fuskanta a yau.

Nakasassu a wajen taron ba da tallafi da aka yi a Bauchi

“Mun taru a nan ne a yau domin ƙaddamar da shirin Ba Da Lamuni Ga Mutane Mabuƙata  (GVG) a Bauchi, Azare da Darazo. 

“Shirin na GVG shiri ne na cika alƙawarin Manufofin Buhari  ga dukkan mutane mabuƙata, domin a ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen Gwamnatin Shugaba Buhari ga kan talakawa, wanda ya yi daidai da tsarin sa na tausayawa na tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga fatara da yunwa a cikin shekara out.”

An ɗauki ma’aikata ‘yan sa ido kan shirin su 380 waɗanda ake kira ‘Independent Monitors’, kuma an ba su takardun kama aiki nan-take tare da na’urori na musamman da za su yi aikin sa-idon da su domin inganta aikin su.

Bugu da ƙari, an tsara bai wa ‘yan gudun hijira mutum 600 kuɗi N50,000 kowannen su, waɗanda a cikin su akwai naƙasassu da tsofaffi.

Hajiya Sadiya ta ƙara da cewa, “Za a biya kuɗin agaji N50,000 sau ɗaya ga kowane ɗan gudun hijira a ƙarƙashin shirin Agaji da Haɓaka Rayuwar Matasa, wato ‘Youth Empowerment and Social Support Operations’ (YESSO), wanda manufar sa ita ce a inganta ƙwarewar su a ayyukan kasuwanci domin sama wa kai aikin yi, sama wa kai dukiya da kuma sama wa wasu daban aikin yi.

“A Jihar Bauchi, masu cin moriyar shirin mutum 600 ne za a ba agajin tsabar kuɗi N50,000 kowannen su.”

A taron, an ƙaddamar da komfutar biyan kuɗi ta shirin Bayar da Tsabar Kuɗi Bisa Sharuɗɗa, wato ‘Conditional Cash Transfer (CCT) Programme’.

A cewar mai tallafa wa ministar a fagen aikin jarida, Miss Nneka Ikem Anibeze, muhimmancin wannan shiri shi ne a samar da matattarar bayanai mai inganci, ta gaskiya, kuma mai sauƙin sarrafawa domin biyan kuɗaɗe ga masu cin moriyar shirin na Bayar da Kuɗi Bisa Sharuɗɗa, wato ‘Conditional Cash Transfer (CCT) Programme’.

Loading

Tags: 'yan sa idoagajiagaji da inganta rayuwaBauchiConditional Cash Transfer (CCT)GEEP 2.0Independent MonitorsMinistar Harkokin JinƙaiMuhammadu BuhariNneka Ikem AnibezeSadiya Umar FarouqShirin Agaji da Haɓaka Rayuwar MatasatsofaffiYouth Empowerment and Social Support Operations
Previous Post

Shugabannin baya ba su bar wa MOPPAN ta Kaduna ko sisi a asusu ba, inji Sha’ani

Next Post

Abin da ya sa za mu yi gangamin taron mawaƙan Arewa – Rabi’u Dalle

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Rabi'u Dalle

Abin da ya sa za mu yi gangamin taron mawaƙan Arewa - Rabi'u Dalle

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!