• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista ya buɗe taron horas da ‘yan jarida kan yaƙi da aƙidun ta’addanci

by WAKILIN MU
June 25, 2024
in Nijeriya
0
Minista ya buɗe taron horas da ‘yan jarida kan yaƙi da aƙidun ta’addanci

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana buɗe taron a Abuja a ranar Talata

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da taron horas da ‘yan jarida na kwana biyu kan inganta rahotannin su domin daƙile aƙidar ta’addanci.

An buɗe taron ne a ranar Talata a Abuja a Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA), Malam Nuhu Ribadu.

A jawabin sa, Idris ya yaba wa Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) da ONSA bisa irin ingantattun matakan da suka ɗauka na yaƙi da ta’addanci, ciki har da ayyukan ceto da dama da ba a bayyana ba.

Ya bayyana muhimmancin sadarwar da kafafen yaɗa labarai da suke yi a kai a kai, wanda hakan ke taimaka wa jama’a su fahimci al’amuran ta’addanci da tsaron ƙasa.

Ya ce: “Kafofin yaɗa labarai na da ƙarfi sosai wajen yin tasiri ga mutane da kuma inganta zaman lafiya.”

Ministan ya jaddada cewa ko dai ‘yan jarida na iya cutarwa ko kuma su taimaka wajen yaƙi da tsauraran aƙidu inda ya ƙara da cewa kyakkyawan rahoto zai iya ilimantar da jama’a domin su guje wa ta’addanci.

Ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa ba da sahihan labarai da ke cin karo da saƙwannin ‘yan ta’adda da kuma nuna nasarorin shirye-shiryen NCTC da ONSA waɗanda ke taimakawa wajen hana tayar da zaune tsaye da sake dawo da tsofaffin ‘yan ta’adda.

Ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su yi aiki tare da masana harkokin tsaro, masana ilimin zamantakewa, masana ilimin halayyar ɗan’adam, da shugabannin al’umma don samar da ra’ayi mabambanta game da ta’addanci da hanyoyin sa.

Idris ya ce yin amfani da bayanai da bincike na iya sa labaran su su zama abin dogaro.

Ya sake jaddada goyon bayan Gwamnatin Tinubu ga aikin jarida, tare da yin alƙawarin ci gaba da bayar da sahihan bayanai, bayanai na yau da kullum, da damarmarkin horaswa.

Daga nan sai ya buɗe taron tare da yi wa mahalarta fatan alheri da addu’ar a yi tattaunawa mai albarka.

Loading

Previous Post

Aikin bututun gas na AKK zai bunƙasa tattalin arzikin Arewacin Nijeriya – Minista

Next Post

Ibrahim Yala: Duk cikin mata na uku babu mai haƙurin uwargida ta Nafisa

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ibrahim Yala: Duk cikin mata na uku babu mai haƙurin uwargida ta Nafisa

Ibrahim Yala: Duk cikin mata na uku babu mai haƙurin uwargida ta Nafisa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!