• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa BPP kan inganta gaskiya wajen sayen kayayyaki

by WAKILIN MU
January 23, 2025
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa BPP kan inganta gaskiya wajen sayen kayayyaki

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a hagu), tare da Babban Daraktan BPP, Dakta Adebowale Adedokun

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Hukumar Sayen Kayayyaki ta Ƙasa (BPP) kan ƙoƙarin ta na inganta gaskiya da riƙon amana a wajen sayen kayayyaki da bayar da kwangiloli.

A wata ganawa da ya yi a Abuja a ranar Alhamis tare da Babban Daraktan BPP, Dakta Adebowale Adedokun, da wasu shugabannin hukumar, Idris ya jinjina wa ƙoƙarin hukumar na sauƙaƙa tsarin sayen kayayyaki.

Ya nanata jajircewar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata na tabbatar da gaskiya wajen bayar da kwangiloli.

Ya ce: “Kafin yanzu, ana ɓoye-ɓoye wajen sayen kayayyaki sau da yawa. Ina farin cikin cewa kuna bayyana komai yanzu. Babu abin da ya kamata a ɓoye. Idan wannan kamfani ya samu kwangila, a bari kowa ya sani cewa wannan kamfani ya samu kwangilar kuma waɗannan su ne dalilan. Idan aka ci gaba da wannan bayyana gaskiyar da hukumar ku ke yi, to zan iya tabbatar maku da cewa idan mutum ya rasa wata kwangila ba zai yi baƙin ciki ba.”

Idris ya bayyana sabon tsarin BPP na kammala sayen kayayyaki cikin kwana 20 a matsayin wani babban cigaba wanda ke nuna ƙwaƙƙwaran jagoranci da sha’awar kawo gyara.

Ya ƙara da cewa ingantaccen tsarin sayen kayayyaki zai taimaka wajen adana albarkatu don kawar da talauci a ƙasa.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar sa za ta haɗa kai da BPP wajen wayar da kan jama’a kan tsarin sayen kayayyaki da kuma yaƙi da lalata kayan gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa an sauya sunan ma’aikatar sa zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ne domin a mayar da hankali kan wayar da kan jama’a da dawo da ƙimar ƙasa.

Ya ce: “Abin da Shugaban Ƙasa ke ƙoƙarin faɗi shi ne cewa akwai sabon mayar da hankali kan wayar da kai da dawo da darajar ƙasa, kuma Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa nan ba da jimawa ba a madadin ’yan Nijeriya.”

A nasa ɓangaren, Babban Daraktan jukumar ta BPP, Dakta Adebowale Adedokun, ya jaddada ƙoƙarin hukumar na aiwatar da tsarin sayen kayayyaki mai gaskiya da adalci.

Ya bayyana cewa dole ne dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati su kammala sayen kayayyaki kafin ƙarshen rabin shekara.

Dakta Adedokun ya sanar da cewa hukumar tana komawa tsarin sayen kayayyaki na onlayin don bai wa masu kwangila daga sassa daban-daban na ƙasa da ƙetare damar shiga tsarin.

Ya kuma ce an fara tantance masu ba da shawara da masu ba da sabis don taimaka wa ‘yan kwangilar gida su iya yin gasa a yadda ake yi a ko’ina a duniya.

Domin inganta gaskiya, ya ce dole ne ma’aikatu da hukumomin gwamnati su gabatar da rahotannin kwata-kwata na kwangilolin da aka bayar, ciki har da sunayen ‘yan kwangilar, waɗanda za a wallafa su a gidan yanar BPP.

Haka kuma an samar da sababbin ƙa’idojin sayen kayayyakin aikin asibiti, tsaro na abinci, da motoci don tabbatar da daidaiton tsarin.

Loading

Tags: Bureau for Public Procurement BPPDakta Adebowale AdedokunkwangilaMohammed Idrissayen kayayyaki
Previous Post

Ƙasashe 7 sun mara wa Nijeriya baya don kafa Cibiyar Koyar da Ilimin Yaɗa Labarai ta UNESCO – Minista

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jama’a kan ajiye abubuwa masu fashewa don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jama’a kan ajiye abubuwa masu fashewa don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jama’a kan ajiye abubuwa masu fashewa don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!