ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta taya Alhaji Ali Nuhu murnar kama aiki a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC).
A cikin wata takardar sanarwa da ya fitar, Shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Habibu Barde Muhammad, ya ce, “Lallai mun yi matuƙar farin ciki da cigaban da aka samu a harkar fim da kuma fitowar ɗaya daga cikin mu, Dr. Ali Nuhu, a matsayin sabon MD/Shugaba na NFC.
“Bayan da ka fara aiki a hukumance jiya a gaban dukkan masu ruwa da tsaki tare da wakilan mu na MOPPAN na ƙasa, mun yi imani da Ali Nuhu a kan karagar mulki, NFC za ta kasance cikin shiri sosai don jagorantar masana’antar finafinai mafi fa’ida a Nijeriya da kuma mafi girman matsayi idan aka yi la’akari da zuciyar sa ta ƙwarewa, ilimi da hikimar sa a cikin ƙasa da kuma na duniya.”
Barde ya taya murna ga Ali, wanda ya kira da “ɗan’uwa mu,” tare shan alwashin za su ci gaba da sadauƙar da kai a gare kai daga MOPPAN ta ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki don taimaka masa wajen tabbatar da masana’antar finafinai ta yi ƙarfi da nasara a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin sa mai ɗimbin cancanta kamar yadda Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi a kwanan nan.
Ya ci gaba da cewa, “A halin yanzu mun karɓi mafi girman girmamawa da la’akari daga ‘MOPPAN National Exco’ da sauran masu ruwa da tsaki yayin da ka fara hasashen sabon lokacin ka mai nasara a Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya.
“Mun amince da ƙarfin kuzarin ka da tsayin daka wajen tabbatar da cigaban masana’antar da ka kasance cikin ta shekaru da yawa a rayuwar ka.
“Allah ya ƙara maka ƙwarin gwiwa yayin da ka ke jagorantar jirgin babbar nasara wanda zai tsaya gwajin lokaci a ciki in-sha Allah.”