• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mun kammala duk shirye-shiryen gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, inji INEC da ‘yan sanda

by DAGA WAKILIN MU
January 26, 2023
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da rundunonin ‘yan sanda na jihohin Edo, Delta da Bayelsa sun bayyana cewa sun kammala dukkan wani shiri domin gudanar da manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023 ba tare da wani cikas ba.

Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe na INEC (REC) da ke waɗannan jihohin su ne su ka bayyana haka a hirarrakin da su ka yi a lokuta daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).

A cewar su, ƙarin hare-haren ta’addanci da ake kai ofisoshi da kayan aikin su a faɗin ƙasar nan bai sa sun karaya ba kan ƙudirin su.

Mista Monday Udoh-Tom, wanda shi ne Kwamishinan Zaɓen INEC a Delta, a yayin da ya ke bayyana cewa hukumar ta gama shirya wa zaɓen, ya yi bayanin cewa sun gama dukkan tsare-tsaren da su ka kamata don tabbatar da cewa an yi zaɓe cikin lumana.

Ya ce: ”A cikin watanni takwas da su ka gabata zuwa yau INEC ta yi gagarumin aikin wayar da kan jama’a, domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe sahihi, karɓaɓɓe kuma a cikin adalci.

”Daga cikin ayyukan da hukumar ta gudanar akwai aikin sabunta rajista da kuma karɓar katin shaidar rajistar zaɓe wanda ake kan ci gaba da karɓa a yanzu haka.

Utom ya ce INEC ta riƙa tuntuɓar ƙungiyoyi, hukumomin tsaro, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar da zaɓe domin zaburarwa zuwa ga gaggauta shirye-shiryen gudanar da zaɓe.

Ya ce INEC ba za ta miƙa wuya ga duk wata barazana ba, don haka sai ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su bai wa hukumar goyon baya domin tabbatar da an yi zaɓe lami lafiya a cikin kwanciyar hankali.

Ba za mu bari a yi cuwa-cuwar cinikin ƙuri’u ba – Rundunar ‘Yan Sanda:

Dangane da irin tanade-tanaden da ta yi a fannin tsaro, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo ta ce ta daɗe da yin shiri domin ganin cewa an yi zaɓe a cikin kwanciyar hankali a Jihar Edo.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Mohammed Ɗanƙwara, ya ce sun fito da wani shirin samar da cikakken tsaro, wanda su ka raɗa wa suna ‘Operation Order’, wanda ya ce gaba ɗayan ‘yan sandan jihar kowa na ciki.

Ɗanƙwara, wanda Kakakin Yaɗa Labaran ‘yan sandan Edo, Chidi Nwabuizor ya wakilta, ya ce a zaɓen 2023 masu sayen ƙuri’u da dillalan su ba za su ci kasuwa ba.

“Ba za mu gani, ko mu ji labarin ana cuwa-cuwar cinikin ƙuri’u a ranar zaɓe ba,” inji shi.

Su ma kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Delta da Bayelsa sun bayyana irin na su shirye-shiryen da su ka yi, domin tabbatar da samar da tsaro, wanda hakan zai sa a gudanar da zaɓukan 2023 cikin kwanciyar hankali.

Loading

Tags: 'yan sandaINECkwamishinonin zaɓeRECsshirye-shiryeZaɓen 2023
Previous Post

Zan daɗe ina tunanin rasuwar ɗa na Khalid – tsohon shugaban MOPPAN, Abdulkareem Muhammad

Next Post

Yadda ɗaurin aure da taron bikin jarumin Kannywood Abale ya gudana

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ango Adam Abdullahi Adam (Abale) tare da amarya Maryam Faruq Sale

Yadda ɗaurin aure da taron bikin jarumin Kannywood Abale ya gudana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!