A YAU, ana zaman ɗarɗar a Nijeriya. Mutane sun samu kan su cikin halin ha’ula’i a wannan zamani na annobar cutar korona (COVID-19).
Ana ta mace-mace ba dare ba rana, musamman manyan mutane da shekarun su su ka kai daga 50 zuwa sama. To amma mutuwar ba ta bar kowa ba.
A nan Arewa, an lura da cewa an fi samun mace-macen a Kano. Wasu sun ce cutar koronabairus ce ke ragargazar rayuka, amma wasu kuma sun danganta rashe-rashen ga wasu cututtuka na daban da su ka yi sanadiyyar rasuwar mamatan, irin su hawan jini, suga ko tsufa.
Mako biyu da su ka gabata an fitar da wani rahoto, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta musanta, wanda ya ce a cikin kwana biyu kacal mutane sama da 300 ne su ka mutu a Kano. Abin ya na ci gaba da wanzuwa har ya zuwa lokacin da mu ke haɗa wannan rahoton.
Mujallar Fim ta binciko cewa a industirin finafinai ta Kannywood, an samu irin waɗannan mace-macen da ɗan dama, inda ‘yan fim su ka yi rashin iyayen su ko wani nasu.
Mujallar Fim ta gano cewa abin ya fara shafar ‘yan fim kai-tsaye ne a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, 2020 lokacin da mahaifin babban furodusan fim ɗin ‘Sangaya’, Auwal Mohammed Sabo, ya rasu.
Alhaji Muhammad Sabo ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya, a gidan sa da ke Layin Kankare, Gwammaja, Kano. An yi jana’izar sa washegari.
Bayan kwana shida, a ranar 21 ga Afrilu, sai mahaifin fitacciyar jaruma Sadiya Gyale ya rasu a Kano.
Mahaifin nata ɗan shekara 85, Alhaji Muhammad Tukur, shi ma an yi jana’izar sa washegari.
Bayan kwana biyu cif, a ranar 23 ga wata, sai kuma labari ya zo na rasuwar mahaifin fitaccen jarumin barkwanci Ali Artwork, a Kaduna.
Gari na wayewa kuma, wato ranar 24 ga wata, sai Allah ya yi wa mahaifiyar fitaccen mawaƙi Ado Isah Gwanja rasuwa.

Shi ma mawaƙi Haruna Chizo Salisu, wanda ke zaune a ƙasar Jamus, mahaifiyar sa ta rasu a wannan ranar ta 24 ga Afrilu. Allah ya ɗau ran Hajiya Umma ne a Zariya, Jihar Kaduna.
Bayan tazarar kwana biyu kuma, a ranar 26 ga wata kenan, aka tashi da labarin rasuwar mahaifin furodusa kuma jarumi Tahir I. Tahir, a Kano.
An yi jana’izar sa a gidan sa mai lamba 784, Kawon Maigari, bayan masallacin Bulama da ke Kwanar Maggi, Hotoro.
Shi ma jarumi Aminu Ilu Dambazau, Allah ya yi wa ƙanen mahaifin sa rasuwa a wannan ranar ta 26 ga wata.
Waɗannan rashe-rashen da ke sama duk a cikin Afrilu su ka faru.
To, shi ma wannan watan na Mayu, 2020, ya zo da nasa, domin kuwa tun a ranar 1 ga wata mutuwa ta soma taɓo ‘yan fim.
A ranar ne jaruma Hajara Isah Jalingo ta yi rashin mahaifin ta.
Malam Isah Tidwa Jalingo ya rasu ne a Jalingo, Jihar Taraba, inda a can aka yi masa sutura.
A ranar kuma, wajen sha ɗayan dare, sai wata mutuwar ta ratsa a Kano. Wannan kuwa ita ce ta jarumi Ubale Ibrahim (Wanke-Wanke).
Mutuwar Ubale (Auwal) ita ce ta farko ta wani ɗan fim a wannan ɗan tsakanin, don haka kusan a ce ta fi girgiza ɗaukacin ‘yan fim.
Wannan lamari dai ya ɗaure wa mutane kai. Duk ɗan fim ɗin da mujallar Fim ta je shafin sa na soshiyal midiya ta taras ba abin da ya ke yi sai du’a’i kawai.
Mu na fatan Allah ya jiƙan waɗanda su ka rasu, ya bai wa iyalai da ‘yan’uwa haƙurin jurewa, kuma ya taimaki masu rai.
Idan kuma mutuwar ta zo, to Allah ya sa mu cika da imani, amin.