• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rikiɗar Ibrahim Musa Ɗanƙwairo daga waƙa zuwa attajirin mawaƙin da ba a taɓa yin kamar sa ba a ƙasar Hausa

by DAGA ASHAFA MURNAI BARKIYA
July 20, 2022
in Mawaƙa
0
Alh. Ibrahim Musa Ɗanƙwairo

Alh. Ibrahim Musa Ɗanƙwairo

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALLAH ya albarkaci  Jihar Zamfara da mashahuran mutanen da a zamanin su sai da su ka yi tashen da kowane babu kamar sa a fannin da ya sa gaba. A cikin Zamfarar kan ta, Ƙaramar Hukumar Bakura ta ciri tutar ƙyanƙyashe mutane uku, waɗanda tarihin ƙasar Hausa ba zai taɓa mantawa da su ba.

Daga yankin Bakura mashahurin ɗan damben da har yau ba a sake yin kamar sa ba, wato Abubakar Shago, ya fito. Daga Bakura Ahmed Sani Yarima ya fito, gwamnan da ya ƙaddamar da Shari’ar Musulunci a jihar sa, har ta kai a lokacin ya girgiza dimokiraɗiyyar Nijeriya da siyasar duniyar Musulmi. Haka nan kuma a  yankin Bakura, cikin ƙauyen Ɗankado, aka haifi marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, wanda a tarihin ƙasar Hausa ba a taɓa yin mawaƙin da ya kambama sarautar gargajiya da ƙara mata kwarjini da karsashi a idon jama’a kamar sa ba. Ɗanƙwairo ya yi wannan shahara ta hanyar karaɗe sarakunan Hausa da maƙwabta da waƙoƙi a rayuwar sa.

Da yake Ɗanƙwairo a yankin Maradun ya tashi, can ya yi rayuwar sa har ya rasu a cikin 1991, ya bar duniya, amma kuma za a iya yin wani zaurance a ce “har yanzu ya na duniya.” Saboda me? Musa Ɗanƙwairo ya rasu ya bar ‘ya’yan sa da su ka gaje shi. Sai dai daga cikin su, autan sa, Alhaji Ibrahim Musa Ɗanƙwairo, ya kafa nasa tarihin,  wanda a ƙasar Hausa ba a taɓa yin attajirin mawaƙi kamar sa ba.

Ka fara lissafi tun daga zamanin irin su Ibrahim Gurso har ta zo ga sauran mawaƙa irin su Salihu Jankiɗi, Musa Ɗanƙwairo, Mamman Shata, har ta zo kan irin mawaƙan Hausa masu amfani da basirar kayan kiɗan zamani, wato irin su Dauda Kahutu Rarara da Naziru M. Ahmad, bambancin su da Ibrahim autan Musa Ɗanƙwairo tamkar ruwa cikin bokiti ne da ruwa cikin cokali.

RIKIƊAR MAWAƘI ZUWA ATTAJIRI 

An haifi Ibrahim Musa Ɗanƙwairo a cikin 1970 a ƙauyen Tungar Makaɗa a cikin Ƙaramar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara. Ya tashi   ya iske kiɗa da waƙa ne sana’ar gidan su. Ibrahim bai kai ga fara yin amshi ba, saboda ya yi firame da sakandare, sai mahaifin sa ya rasu.

Ibrahim ƙanen marigayi Garba Daudun Kiɗi da marigayi Sani Zaƙin Murya ne.

Bayan da yayan su, Alhaji Garba, wanda aka fi sani da Daudun Kiɗi, ya karɓi ragamar waƙa, sai Ibrahim ya shiga cikin sahun ‘yan amshi, har ya shekara biyar zuwa shida ya na amshi.

‘ADDU’AR ƊANƘWAIRO CE SILAR ARZIKI NA’

“Kafin mahaifin mu, Alhaji Musa Ɗanƙwairo, ya rasu, akwai shekarar da ya yi wa ‘ya’yan sa rabon gonaki, amma bai ba ni ba. Na je na ce, ‘Alhaji, ka ba kowa amma ni ka hana ni.’

“Sai ya ce min, ‘Ibrahim, ai kai gonar da zan bar maka ba za ka iya nome ta ko ka iya cinye ta ba’.

“Ɗanƙwairo ya ce min, idan ka bar kiɗa, duk sana’ar da ka kama, sai ka yi arzikin da kai za a riƙa zuwa ana yi maka waƙa, ana roƙo a wurin ka’.”

Bayan Ibrahim ya daina amshin waƙa, sai ya kama kasuwanci, inda ya fara da sana’ar sayar da hatsi. Ya riƙa yawon neman ‘yan kwangiloli daga wannan ofis zuwa wancan. Daga nan kuma ya koma harkar sayar da gwanjo.

“To maganar gaskiya, daga sana’ar gwanjo ce na samu nasibin kasuwancin da tun daga lokacin har zuwa yau sai dai ci gaba na ke samu, ba raguwa ba.

“Asali kuma wani ubangida na ne ya yi muƙamin Mataimakin Kwanturola Janar na Kwastan. Shi ne ya sa aka ba ni gwanjon kaya cikin tirela guda, na sayar na samu riba mai yawa. Sai na je Tafa a Jihar Neja, na gina babban masaukin baƙi.”

Daga nan ƙofar arziki ta ci gaba da buɗe wa Ibrahim autan Ɗanƙwairo, ta yadda sana’o’i su ka ƙaru sosai.

“Ina harkar gina gidajen haya da gidajen saukar baƙi sosai. Gidajen saukar baƙin a Jihar Neja ne da kuma cikin Jamhuriyar Nijar. Ina harkar ɗinki na teloli masu yawa. Ina da gidajen sayar da abinci a Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Ina da wuraren yin ruwa na roba (bottled water) da kuma na leda (pure water).” 

Ibrahim ya na da wasu hanyoyin shigowar kuɗi aljihu da dama ban da waɗannan sana’o’i.

Duk da cewa sana’ar gina gidajen saukar baƙi ce ya fi maida hankali, Alhaji Ibrahim ɗan kasuwa ne, domin ya na da kantin sayar da atamfa a Suleja. Ya na da shagunan gyaran gashin mata, wato salun, da shagunan askin matasa ‘yan zamani.

Bincike ya tabbatar Ibrahim ya mallaki tsakanin gidajen haya da gidajen saukar baƙi a Tafa za su kai hamsin. Kuma ya na da gida a garin Lambata, inda har masallaci ya gina a garin, ya ce ya sadaukar da ladar ga mahaifiyar sa, Hauwa’u.

Ibrahim ya na da wurin shan madarar askirim da sauran tanɗe-tanɗe. Kuma ya na da kantamemen zauren shagalin biki, wato ‘events centre’, inda ake biya a yi taro.

Alhaji Ibrahim ya na harkar safarar motoci. Ya na da motocin haya bas-bas masu yawa. Da wakilin mu ya tambaye shi ko sun kai nawa, sai ya kada baki ya ce, “Sai an ƙirga!” Ya sake tambayar sa, “Ko sun kai ashirin?” Sai ya ce, “Idan ashirin ne kaɗai zan ce sai an ƙirga?”

A cikin garin Suleja a Jihar Neja, Ibrahim na da manyan otal-otal guda biyu. A Jamhuriyar Nijar kuwa gidajen saukar baƙin sa su na da yawa. Har masallacin Juma’a ya gina a garin Maimujiya, inda harkokin sa su ka fi ƙarfi a Nijar, ya sadaukar da ladar ga mahaifin sa, marigayi Musa Ɗanƙwairo. Masallacin, wanda aka buɗe a cikin 2021, Gwamnan Zindar ne babban baƙo na musamman a wurin buɗe shi.

IBRAHIM ƊANƘWAIRO A FAGEN SIYASA

“A gaskiya ina siyasa, amma ka san mu sai dai mu goyi baya, ko kuma na tsayar da ɗan takara. Na taɓa tsayar da ‘yan takarar shugaban ƙaramar hukuma har mutum uku a Jihar Neja, kuma duk sun yi nasara.”

DANGANTAKAR IBRAHIM ƊANƘWAIRO DA MAWAƘA A YANZU

“Ni ba zan taɓa daina tutiya da asali na ba. Kai, ni na ma fi so ka yi min kallon mawaƙi ko makaɗi. Idan ka ce min ‘Ibrahim’ ba ka haɗa da ‘Musa Ɗanƙwairo’ ba, to ba na jin daɗi.

“A yanzu haka ni ne uban Ƙungiyar Makaɗa Da Mawaƙa. Shi ya sa duk inda na ga wani maroƙi, ko a hanya ne, ban yi masa kallon wulaƙanci.

“Na taɓa ganin wata intabiyu da aka yi da Bill Gates, inda ya ce asalin mahaifin sa tela ne, shi duk da ya zama attajirin duniya, ba ya raina sana’ar ɗinki. A take ya zaro allurar ɗinki ya nuna wa wanda ke masa tambayoyi.”

TSAKANI NA DA ƊANƘWAIRO A YANZU

“Baya ga taimakon da na ke wa ‘yan’uwa bakin gwargwado, duk bayan wata uku ina sa a karanta Ƙulhuwallahu zuwa ƙarshen sura ƙafa 70,000, sadaukarwa ga Musa Ɗankwairo da Hauwa’u. Na gina rijiyoyi don ladar ta je wurin su. Na gina masallatai don ladar ta je wurin su.

“Yanzu haka ina shiri zan yi situdiyo, wurin shirya waƙoƙin da Ɗanƙwairo ya yi, domin a taskace su wuri ɗaya. Kuma ina so na jawo gidajen tsoffin mawaƙan da su ka mutu domin mu raya al’adun gargajiya.”

DAMUWAR IBRAHIM ƊANƘWAIRO A YANZU

“Wani abu ya faru a cikin azumi da ya sa har na zubar da hawaye. Wato ina da ma’aikatan da na ke biya albashi za su kai ɗari biyu. Ranar da na biya su a cikin azumi, na ga yadda su ke murna su na addu’a ga iyaye na, sai hawaye ya riƙa zubo min. 

“Na ce haka Allah ya yi da mu kuma? Wai da mu ne ke yawo mu na roƙo a ba mu, yanzu kuma a wuri na ake zuwa karɓa, har ina biyan albashi na miliyoyin kuɗaɗe!”

Juyin lokaci ko sauyin rayuwa ta kai ga Alhaji Ibrahim kan yi kyauta ga wasu waɗanda a can baya mahaifin sa kan yi wa waƙa su na ba shi kuɗi.

“Abin da kawai ke damu na shi ne da Ɗanƙwairo bai kai lokacin da zai ga rufin asirin da Allah ya yi min ba. Amma da a ce ana dawowa, kuma Ɗanƙwairo ya dawo ya taras takardun kuɗi ake ci, to zan ciyar da shi da kuɗi har ƙarshen rayuwar sa,” inji Alhaji Ibrahim, babban ƙane mahutar manya.

* Ashafa Murnai Barkiya ɗan jarida ne mazaunin Abuja

Loading

Tags: Daudun KiɗiIbrahim Musa ƊanƙwairoMaradunmawaƙaMusa ƊanƙwairoSani Zaƙin MuryaSulejaTafaZamfara
Previous Post

Tugun ‘yan baƙin ciki ba zai kashe mini gwiwa ba – Sadiya Umar Farouq

Next Post

INEC ta sha alwashin zaɓuɓɓukan 2023 za su fi na baya inganci

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Farfesa Mahmood Yakubu (na 5 daga dama) tare da maziyartan

INEC ta sha alwashin zaɓuɓɓukan 2023 za su fi na baya inganci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!