HAJIYA Fati Khalil ta na cikin sahun farko na mata mawaƙa da ake yayin su a yau. Duk kuwa da daɗewar da ta yi a cikin harkar waƙa, har yanzu tauraruwar ta ta na haskawa. Mujallar Fim ta zanta da zabiyar, wadda a yanzu aka sani da Fati Khalil Zabiya, domin jin tarihin ta da kuma wasu abubuwa da su ka shafi harkokin ta na waƙa, kamar haka:
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
FATI KHALIL: To, kamar dai yadda aka sani suna na Fatima Ibrahim Khalil wadda a yanzu an fi kira na da Fati Zabiya. Kuma ni haifaffiyar garin Kaduna ce. Na yi karatu na na firamare da sakandire duk a garin Kaduna. A yanzu kuma ina garin Kano da zama.
FIM: A wacce shekara ki ka fara waƙa?
FATI KHALIL: To na fara waƙa ne a 2003. Waƙa ta ta farko kuma amshi ne na yi wa wani mawaƙi ana ce masa Abubakar Yarima; waƙa ce ta matar gwamnan Zamfara na lokacin, Ahmad Sani Yarima. Sai kuma waƙa ta biyu wadda ni na yi ta, tawa ce ta kai na, ita ce waƙar aure da na yi na wata ƙawa ta, Fauziyya sunan ta, da mijin ta Nasir. Sai kama amshin waƙar da na yi, ita ce ta ta’aziyyar Shehu Hadi ɗan wajen Sheikh Ɗahiru Bauchi. Daga kan ta ne na fara jin murya ta a gidajen rediyo da sauran wajen jama’a saboda a lokacin ka ga babu soshiyal midiya sai Facebook, kuma ba a ɗora murya sai dai hoto.

FIM: Wanene ubangidan ki na farko a waƙa?
FATI KHALIL: To, ubangida na na farko wanda aka kawo ni wajen sa shi ne wanda aka damƙa amana ta a wajen sa, kuma gwargwadon hali ya riƙe amana. Shi ne Ahlibaiti Ɗan Usmanu wanda mawaƙi ne na siyasa; a Kaduna ya ke da zama. Ya na waƙoƙin siyasa, ya na waƙoƙin tallace-tallace na kamfanoni duka ya na yi.
FIM: Ko kin taɓa zama a situdiyo a ƙarƙashin wani mawaƙi?
FATI KHALIL: A’a, ban taɓa zama a situdiyo a ƙarƙashin wani mawaƙi ba, sai dai na taɓa zama a wani situdiyo wanda ya ke ƙarƙashin wani kamfani ne wanda ina ɗaya daga cikin mata mafi girma da su ke waƙa a wannan kamfanin mai suna MDC wanda daga shi kuma ban ƙara zama a wani ba har yanzu. Sai dai a kira ni idan wani ya shirya wata waƙa, ko kuma na zo na yi ta kai na na tafi. Haka na ke yi.
FIM: Za ki iya sanin yawan waƙoƙin ki da ki ka yi?
FATI KHALIL: To na yi waƙoƙi na siyasa da na biki da sauran waƙoƙi da ake yi, in dai ba ta saɓa ƙa’ida ba. Amma dai waƙar da na fi samun kuɗi da ita, ita ce waƙar aure.
FIM: Waɗanne waƙoƙi ne su ka fito da ke duniya ta san ki?
FATI KHALIL: Gaskiya waƙoƙin da su ka fito da ni duniya ta san ni ba waƙoƙi ba ne da na ke yi nawa na kai na ba, waƙoƙi ne da mu ke yi tare da wasu, kuma su ne dai waƙoƙin cikin finafinai da mu ke yi. Ta sanadiyyar wannan duniya ta san ni, don waƙoƙi ne da mu ke yi da su Umar M. Shareef, Adam A. Zango, Abubakar Sani, Baban Chinedu, da ‘yan fim ɗin nan dai haka da su ke yin waƙoƙi. Sai kuma ubangida na wanda shi ne ya ke a matsayin ubangida na tsawon shekaru, mai girma Sarkin Ɗiyan Gobir, Alhaji Dakta Aminu Ala. To waƙoƙin sa da mu ka yi na siyasa da sun fita an san su. To sun zamar mini sanadi, aka san ni. Amma dai waƙoƙi nawa na kai na, gaskiya ba ni ma da lokaci, saboda yawan yawon yin waƙoƙin wasu wanda hakan ya kan hana ni sukunin na yi nawa na kai na. Sai dai akwai wata ta na nan wadda kwanakin baya na fitar da ita, sunan ta ‘Tozali’, wadda na ke cewa:
“Ya Rasulu Ma’aiki, Annabi Abban Zahra. Ɗaha son ka na ke yi.
Baitin yabon ka na ke yi.
Tawassuli da Ma’aiki
Na yi shi sa ni a ceto.”
FIM: Yaya alakar ki ta ke da Aminu Ala?
FATI KHALIL: To, a yanzu Aminu Ala shi ne ubangida na a waƙa, tun tsawon shekaru, za su kai kamar goma. Kuma alaƙa ta da shi alaƙa ce tamkar ta ‘ya da uba, don ya wuce da in kira shi da abokin aiki kaɗai ko yaya na. Don ya kan zaunar da ni ya yi mini nasihohi, ya yi mini faɗa, ya kwaɓa mini, kamar yadda dai mahaifi na ya ke zaunar da ni ya yi mini faɗa. Saboda haka, shi tamkar uba ya ke a waje na. To wannan ita ce alaƙar da ta ke tsakani na da shi. Sannan kuma sai alaƙa ta aikin waƙa da mu ke haɗuwa mu yi. Don haka tsawon shekarun nan ba ni da wani da ya ke uba a gare ni a fagen waƙa kamar shi a yanzu. Babu tamkar sa, domin ya taimaka mini sosai wajen gane hanyoyi da yawa na alheri, don haka ba ni da wani kamar sa, don haka kullum na ke yi masa addu’a ta fatan alheri.
FIM: A Kaduna aka san ki, amma a yanzu kin dawo Kano da zama. Ko menene dalilin dawowar ki Kano?
FATI KHALIL Tabbas, a Kaduna aka san ni, amma yanzu na dawo Kano da zama. Dalili shi ne harkar waƙa ce ta dawo da ni garin Kano. Saboda a nan na fi yin aikin cikin muhimmanci sosai, saboda a nan ne aka fi yin sana’ar da kyau fiye da ko’ina. Don haka harkar waƙa ce ta dawo da ni garin Kano.
FIM: Wane abu ne na alheri da ki ka samu a harkar waƙa da ba za ki taɓa mantawa da shi ba?
FATI KHALIL: To abin da na samu na alheri a harkar waƙa da ba za nan mantawa ba shi ne samun damar sauke farali da na yi da kuma ziyarar Ma’aiki da na yi zuwa Ƙasa Mai Tsarki, wato Makka da Madina. Alhamdu lillahi, wannan ya na daga cikin mafi girman darajar da ba zan manta da shi ba a rayuwa ta.

FIM: Wane buri ki ke da shi a rayuwar ki ta waƙa ?
FATI KHALIL: Tabbas, waƙa ita ce sana’a ta a yanzu da na ke ji da ita. Amma a yanzu ba ni da wani buri da ya wuce na ga Allah ya kai ni lokacin da zan gan ni a ɗakin miji na ina zaune zaman ibadar Allah. Wannan shi ne babban buri na a cikin wannan sana’a, kuma waƙoƙin da na yi wanda na ɗauke su sana’a, su na zamar mini sanadi na rufin asiri na, wanda na kan yi na samu kuɗi na yin buƙatun yau da kullum, kuma har ma na taimaki wani da shi.
Alhamdu lillah, kuma amma buri na yanzu dai in dai shi ake so a ji, na gaskiya da gaskiya babu wani ɓoye-ɓoye, babu abin da ya kai na ga Allah ya yarda ya kai ni ɗakin miji na, in gan ni a ɗakin aure na ni ma ina zama na ibada kamar yadda kowace mace ta ke yi. Ina fatan Allah ya cika mini buri na.
FIM: To, madalla. Mun gode.
FATI KHALIL: Ni ma na gode sosai.

