• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sai hamdala da aka naɗa ni Sarkin Waƙar Marafan Yamman Zazzau – Albashir Yareema

by ABBA MUHAMMAD
February 8, 2024
in Labarai
0
Sai hamdala da aka naɗa ni Sarkin Waƙar Marafan Yamman Zazzau – Albashir Yareema

Albashir Hamza Yareema tare da Marafan Yariman Zazzau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘIN Kannywood, Albashir Hamza Yareema, ya yi godiya ga Allah (s.w.t.) bayan naɗa shi Sarkin Waƙar Marafan Yamman Zazzau da aka yi a ranar Lahadi da ta gabata.

Marafan Yamman Zazzau, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullahi, shi ya naɗa shi tare da wasu mutum uku.

A yayin da ya ke zantawa da mujallar Fim, Albashir ya ce, “Ina yi wa Allah (s.w.t.), Maɗaukakin Sarki, Mamallakin Sammai da Ƙassai, Mai Kowa Mai Komai, godiya. Sannan kuma ina yabo da samun karamci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (s.a.w.).

“Ina godiya ga Allah a bisa wannan al’amari na karamci da ni’ima da ya yi a gare ni.

“A gaskiya, na ji daɗin wannan naɗin sosai, ta yadda babu wani abu da zan iya misaltawa da shi, domin tabbas na samu natsuwa a kan sana’a ta ta waƙa. Na ji cewa ina yin abu ne, kuma abin da ya dace.

“Na ƙara samun tabbacin abin da na ke yi abu ne wanda yake na lura da kuma daidai. Na kuma ƙara samun natsuwa a kan sana’a ta ta waƙa. Saboda yau ta dalilin waƙa ne na samu abin da na samu a ce rawanin da na ke hangen shi a wurin sarakuna iyayen mu, yau ga shi darajar waƙa na samu rawanin sarauta, sarauta kuma babba ta sarki.

Albashir bayan an naɗa shi Sarkin Waƙa

“Ka ga wannan abin godiya ne ga Allah, kuma ƙara samun yaƙini ne, ba zan iya misalta irin daɗin da na ji na samun wannan nasara ba.

“Amma na yi farin ciki matuƙa. A duniyar waƙa, a lokacin da ake naɗa min wannan rawanin, na ji cewa tabbas tamkar tsuntsu ne da aka saki daga cikin keji.

“Abin da ya sa na kawo wannan misalin, kamar cewa da ina yin waƙa ne a ɗaure a cikin keji babu wata daraja, babu wata kima. Amma ranar da ake yi min wannan rawanin na san cewa an fitar da ni daga cikin wannan kejin. To ka ga abin godiya ne, abin kuma ƙara zage damtse ne da biyayya ga na gaba da mu, domin biyayya da nuna ƙauna ta kawo haka, da kuma rage son abin duniya da kwaɗayi.

Sarkin Waƙa Albashir Hamza Yareema a kan ingarman doki

“Daga ƙarshe, ina mai jan hankali ga mawaƙan mu da su zama masu yarda da abin da su ke yi da kuma fahimtar cewa lallai ba su da wani abin da ya fi masu waƙa, ita ce baiwar da Allah (s.w.t.) ya yi masu.

“Su ɗauki sana’ar da daraja da kuma kima da sakankancewa da cewa Allah shi ne mai yin komai, ba wanin Allah ba.

“Haka kuma ina mai miƙa godiya da jinjina ga mai martaba Marafan Yamman Zazzau, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullahi. Allah ya saka masa da alkhairi, ya kare shi daga sharrin maƙiya. Allah ya ƙara wa rawanin sa girma, ya kuma ƙara kare mutuncin sa da darajar sa.

“Ina kuma miƙa godiya ga ɗaukacin ‘yan’uwa da abokan arziki da su ka halarci taron naɗin da aka yi min. Allah ya saka da alkhairi.

Dandazon jama’a a lokacin da Albashir ya ke jawabin godiya

“Sannan ina godiya da irin karamci da kara da ‘yan’uwa na, Abdullahi Abbas, Sadiq Ɗan Sudan, Raliya Muhammad, Maryam da kuma Rabi’at (Maama), su ka nuna min. Na gode ƙwarai da gaske.”

An dai yi taron naɗin sarautar ne ranar Lahadi, 3 ga Fabrairu, 2024 da misalin ƙarfe 12 na rana, a ƙofar gidan Marafan Yamman Zazzau.

Loading

Tags: Albashir Hamza YareemaAlhaji Mustapha Adamu UbaidullahinaɗisarautaSarkin WaƙaZazzau
Previous Post

Furodusa Abdul Amart ya saya wa dattawan jarumai 50 fom don sabunta rajistar su a Kannywood 

Next Post

Za a ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood, Fati KK a gobe

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Za a ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood, Fati KK a gobe

Za a ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood, Fati KK a gobe

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!