A KULLUM ‘yan fim su na ƙara samun daraja a cikin al’umma, duk da irin mugun kallon da wasu ke yi masu. Masarautu na zaƙulo wasu daga cikin su su na ba su sarauta.
Wasu daga cikin masu sarauta a cikin ‘yan Kannywood sun haɗa da Aminu Ladan Abubakar (ALA), Sani Mu’azu, Ibrahim Mandawari, Sani Musa Danja, Fati Nijar, Adamu Hassan Nagudu, Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a), Maryam Giɗaɗo, da sauran su.
To a wannan karon kuma abin alkhairin ya shigo Jihar Kaduna, domin kuwa masarautar Bichi ta Jihar Kano ta gama shirin naɗa fitacciyar furodusa Hajiya Fatima Ahmed Ibrahim (Lamaj) sarauta.
Za a naɗa ta Jakadiyar Matasan Nijeriya a ranar Juma’a, 20 ga Mayu, 2022 a fadar Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, a garin da ke Jihar Kano.
Majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa Sarkin ne da kan shi zai naɗa ta.
Don haka Hajiya Fatima ta na gayyatar ‘yan’uwa, abokan arziƙi da kuma abokan sana’ar ta.
Allah ya kai mu ranar da rai da lafiya, kuma ya taya riƙo, amin.