Shawara zuwa ga Mai girma Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Gida-Gida.
Assalamu alaikum H.E.
DA farko, ina taya ka murnar cika shekara ɗaya a karagar mulki.
Muna godiya da irin kamun ludayin jagorancin da ka ke yi a wannan jiha ta Kano.
Shawara ta 1. Kamar yadda Gwamna ka ƙaddamar da State of Emergency a kan harkar ilimi ranar Asabar a farfajiyar Gidan Gwamnatin Kano tare da ɗibar sabbin malamai na Besda, haɗa da biyan kuɗin qualifying, al’ummar Kano sun yaba maka, kuma su na godiya.
A sakamakon haka na ke ba da shawarar Gwamna ka yi ƙoƙari wajen saka State of Emergency a kan harkar hauhawar farashin kayan masarufi da ƙwacen waya da harkar daba, domin hauhawar farashin ba gaira ba dalili ya ragargaza tattalin arzikin Jihar Kano.
Mai girma Gwamna, wallahi al’ummar Kano da ƙananan ‘yan kasuwa su na cikin wani hali na matsi da rugujewar jari, su na cikin halin wayyo Allah. Al’amarin ya ya wuce misali fiye da yadda ka ke samun labari.
Kullum mu na shiga cikin kasuwanni, mu na zama a majalisu da mutane, mu na jin koken su. Gwamna al’ummar Kano na cikin wani yanayi. Wallahi rubutu na ba zai iya fayyace maka irin raɗaɗin da Kanawa da sauran al’ummar arewacin ƙasar nan ke ciki ba.
Ina ƙara ba da shawara cewa a taka wa ‘yan kasuwa birki cikin gaggawa, a yi doka a kan ƙarin farashin ko a kafa wata hukuma da za ta dinga kula da wannan al’amari a kowace Ƙaramar Hukuma.
Babu wani abu da ya fi ƙarfin gwamnati, kuma gwamnati komai-da-ruwan-ka ce. Za ka iya, na tabbata da haka.
Kamar yadda mai girma Gwamna a kwana biyu kacal aka yi wata doka kwanan nan a Kano, to ina ba da shawara da Majalisar Kano a cikin kwanaki ƙalilan su yi dokar ta-ɓaci dangane da hauhawar farashin kayan masarufi da ƙwacen waya da harkar daba.
Waɗannan al’amura na ci wa kafatanin al’ummar Kanawa da maƙwabtan su tuwo a ƙwarya fiye da tunanin masu tunani. Ko kuma ku yi haɗin gwiwa da sauran gwamnonin Arewa da ƙasa baki ɗaya domin shawo kan wannan matsala. Ko kuma dai a nema wa jama’a mafitar da ta fi wannan.
Mai girma Gwamna, na fahimci irin ƙoƙarin da ka ke yi a fannonin lafiya, na ga ka mayar da hankalin ka sosai. Mu na godiya. Amma akwai buƙatar yadda ka ke yawan ziyartar Asibitin Hasiya Bayero domin inganta shi da ganin komai na tafiya yadda ya kamata, to ka dinga ziyartar sauran asibitocin, musamman manyan asibitocin Kano.

Wallahi akwai matsaloli masu ɗimbin yawa waɗanda ba dole ne shi kan sa Kwamishinan na Lafiya ya san da su ba, amma na fi so ka yi ziyarar ba-zata a kai a kai, wata ran za ka fahimci irin saƙon da na ke so in nusar maka.
Akwai shawarwari masu ɗimbin yawa a tattare da ni. Na yi iya ƙoƙarin ganin ka domin ba da su kai-tsaye amma ganin ka ya yi wuya, ya gagare ni. Wannan ya sa na ce bari in yi buɗaɗɗiyar wasiƙa a matsayi na na wanda ya yi ƙoƙarin ganin ka samu nasarar hawa wannan kujera ta gwamna domin yaƙini da na ke da shi cewa kai adali ne kuma mai sauraren jama’ar ka ne birni da ƙauye.
A kullum ‘yan’uwan mu ‘yan adawa idan mun haɗu muna samun shaguɓe da ƙananan maganganu cewa gwamnatin mu ta gaza. Ni kuma na san ba ka gaza ba, ka na iya ƙoƙarin ka, amma jama’a ba sa gani. Ina addu’ar Allah ya ganar da su, amin.
Sai Kuma maganar ‘yan jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya da su ka ba da gagarumar gudunmawa wajen zaɓen ka da sauran kujerun sanatoci da ‘yan majalisa. A nan ɓangaren ma ana ƙorafi mai yawan gaske. Da yawa a yanzu sun shiga halin ha’ula’i.
Akwai sunayen wasu cikin kwamitocin kanfen ɗin ka sun yi ƙoƙari sosai, sun ba da lafiyar su da dukiyar su da lokacin su, wasu kuma da ƙwaƙwalwar su a lokacin kamfen, amma yanzu su na kamfen sosai. Wasu su na fitowa rediyo su na nuna ɓacin ran su cewa ganin ka ya gagare su ko da kuwa da gaisuwa, ku gaisa ku ɗauki hoto don su nuna ku na tare, amma haƙar su ta ƙi cimma ruwa. Wasu kuma sun yi zaton tun a ɗibar fari za a tafi da su, amma sun ji shiruuuuu!
Duk inda na tsaya sai kuka ake kaka-kala. Mai girma Gwamna, ka kafa wani kwamiti da zai zaƙulo maka irin waɗannan mutane da su ka so ka – so na hakika – domin fara zaman tattaunawa da su, domin su na shan gorin cewa an tura mota…
Mai girma Gwamna, mu gani a ƙasa ka ƙaryata abokan adawa, ka nuna ka na sane da mutanen ka. A taimaki waɗanda su ka taimaka, domin ni buri na Allah ya ba ka ikon yin tenuwa biyu har ka kafa wani gwamna da zai ɗora a kan ayyukan ka.
Allah ya sa wannan saƙon ya zo gare ka cikin fahimta da gane me na ke nufi.
A nan zan tsaya cak sai kuma wani jiƙon domin maganganun da ke baki na da yawa.
Ni ne dai wannan masoyin wannan gwamnati ta NNPP kuma kai ƙaunar Gwamna da cigaban gwamnatin sa.
Alh. Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama
Kano Nigeria.
![]()







