Tsawon shekaru 19 ga samuwar abu lallai abin alfahari ne kuma abin a jinjina wa duk wanda ya tsaya ya na gudanar da abin ba tare da gajiyawa ba. A wadannan shekaru yaron da aka haifa a watan da aka fara yin mujallar yanzu shi ma karfin sa ya kai; idan kuma mace ce, ta sami miji aka yi mata aure, to za ta iya kasancewa ta haihu, don haka ta tashi daga yarinya ta koma uwa. To ita ma haka mujallar ta zama ga duk wata mujallar Hausa da aka yi.
Duk da cewar ba da ni aka fara mujallar ba, amma dai alaka ta da ita ta bangaren na saya na karanta da kuma alaka ta da ma’aikatan ta a matsayin abokai ya sa ina da abin fada dangane da mujallar.
Na samu kai na a cikin Fim tun daga shekarar 2008 – shekara tara bayan an kafa ta. Wannan ma zai iya ba ni damar fadar wani abu dangane da mujallar, don kuwa a zama na a mujallar a kai na na ga abubuwa da dama. An zage ni, an dungure min kai, an lakace min hanci. Akwai wani ma da ya fesa min mari a fuska. Kai, na kwana a ofishin ‘yan sanda amma duk a yawon neman labari. Ko da yake ba labarin na ke so na bayar ba, ina so na nuna irin gwagwarmayar da ake sha wajen neman labari.
Amma idan mu ka duba ta wajen jajircewa ta mawallafin Fim, Malam Ibrahim Sheme, to za mu ga cewar duk mu namu mai sauki ne domin kuwa sai ya tsaya tsayin daka wajen ganin an buga mujallar sannan za mu kai ga neman labarin. Doron bayan sa kawai mu ke hawa mu rinka kallon mutane su na kallon mu har ma mu zama abin alfahari.
Duk tsawon lokacin nan, Sheme ba ya gajiyawa. Shi ya ke nemo kudin sa ya zuba a yi mujallar a ci riba ko a fadi, a wata na gaba ma ya kara. Shi dai ya na nan a kan manufar sa, bai taba gajiyawa ba. An shiga yanayi kala-kala da ba a taba tunanin mujallar za ta tsallake ba, amma bisa taimako na Allah da kuma tsayuwar mawallafin sai ka ga mujallar ta wuce kamar ba a yi ba. Sai ka ga an dawo an ci gaba da tafiya.
Haka ake ta fafatawa har zuwa yau da kowa ya san yanayin fatara da ake ciki a Nijeriya amma dai a haka din ake tafiyar da ita.
Tuni mujallun industiri da aka kafa don neman kudi ko don neman suna su ka dade da mutuwa, sai dai a shafin tarihi; wasu ma ko a shafin tarihin ba za a same su ba saboda ba su yi wani abu da tarihi zai adana su ba. Amma bisa karfin ikon Allah mujallar Fim kadai ce ta zamo kundi na adana tarihin masana’antar finafinai ta Kannywood daga kafuwar ta zuwa yau.
Bayan haka, mujallar ta zama wata makaranta ga masu koyon aikin jarida, domin kuwa ta yaye dalibai masu yawan gaske da a yanzu su ka zama manya a gidajen wasu jaridun. Aikin su da aka gani a mujallar Fim ne ya sa aka dauke su a wajen da su ke har su ka zama masu fada a ji. Hakan ya samu ne saboda kwarewa ta aikin jarida da shi ma wallafin Fim ya ke da ita a kasar nan.
Ba ya ga kwarewa, Sheme bai da rowar ilimin sa, domin kuwa duk wanda ya ke aiki da mujallar, Sheme ya kan koyar da shi tsari da yanayin aikin jarida ko tsara rahoto da yadda ake hira da mutane. A kan haka, ba shi da gajiyawa, zai tsaya ya na ta koyar da kai cikin tsawon lokaci har sai ka yi yadda ya dade da salon aikin jarida na zamani. Ko wani sabon tsari ne ya shigo, sai ya koya maka yadda ya ke da kuma hanyar da za ka bi ka iya cikin sauki.
Sannan ya na da hakuri da juriya wajen gyara labarin da mu ka rubuta ta yadda zai fito ya dauki hankalin mutane, su rinka sha’awar sa. Domin wani lokacin haka mu ke kwaba rubutu ta yadda babu yadda zai karantu, amma haka zai zauna ya gyara ya tsara shi a buga a mujallar, idan ya fito a rinka jinjina mana, ana kallon mu a matsayin wasu gwarzaye, nan kuwa shi ne ya rufa mana asiri. Shi ya san irin faman da ya ke da mu da kuma irin wahalar da mu ke ba shi.
A takaice dai, a tsawon shekarun nan duk da tabarbarewar lamurra na kasuwanci da kuma shigowar soshiyal midiya, har yanzu mujallar Fim kadai ce hanyar samun labarai masu inganci game da ‘yan Kannywood da ma abubuwan da su ka shafi al’adun kasar Hausa. Idan har akwai wani abu da mujallar za ta kalla a matsayin riba da ta samu, ni a tawa mahangar, ita ce cimma manufa da kuma samar da horo ga ma’aikata da su ke cin gajiyar abin har zuwa ‘ya’ya da jikoki. Hakan zai zamo sadakatul jariya ga duk wanda ya samar da hakan.
A kan batun cimma manufa, zan iya cewa Ibahim Sheme ya yi nasarar samar da wani kundi na adana tarihin Kannywood, wanda in ba domin mujallar Fim ba to da a yanzu babu shi. Don haka da zan yi aron kalmomin wani baiti na Bakandamiyar Alhaji Mamman Shata, sai in ce Ibrahim Sheme “har yau dai shi ne, ba a samo canji nai ba, balle ya huta, ya dan samu ya sarara. A’a, wane hutu kai ma? Mu buga mu gani, ‘yan’uwa na!”
Ya Allah, mu na rokon Ka da Ka kare mujallar Fim da mawallafin ta da sauran masu taimaka masa daga dukkan abin ki, Ka raba mu da ‘yan gangan da masu ganganci, Ka ba mu karfin hali da karfin arzikin da za ta dore har zuwa lokacin da Ka debar mata, albarkacin farin jakada, Annabin rahama, da iyalan gidan sa shiryayyu, masu shiryarwa, amin.