HAUSAWA dai na cewa in ka san abin da za ka faɗi, ba ka san abin da za a mai da maka ba.
A cikin kwanakin nan jarumi a Kannywood kuma mai ba gwamnan Jihar Kano shawara a kan farfaganda, Mustapha Badamasi (Nabraska), ya taso mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) a gaba a kan matsalar da ke tsakanin sa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ɗan takarar zama gwamnan jihar a jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.
Rikicin da ke faruwa tsakanin Rarara da gwamnatin Kano ta sa aka cire sunan mawaƙin a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu.
Daga jiya zuwa yau an ga wasu tagwayen bidiyo na yawo a soshiyal midiya. A na farkon an ga Nabraska na yabon Dakta Gawuna, ya na cewa, “Bai taka maka ba, bai zubar maka ba, hasali ma mutumin nan ɗan takarar gwamnan Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, kamilin mutum ne, mai ƙima da mutunci da martaba, wanda kuma babu ƙarya, babu son zuciya, bai taɓa faɗa da kowa ba a siyasance a zahiri da mu ka sani.”
A ɗayan bidiyon kuma an ga Nabraska ya na cin mutuncin Gawuna a lokacin ya na ɓangaren Kwankwasiyya.
A ciki, Nabraska na cewa, “Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a yau jami’an tsaro su damƙe ka, su saka ka a mota, ka na roƙon su don girman Allah su buɗe ka ka fita, don ka yi ta’annati, ka yi ɓarna. Wannan abu abin baƙin ciki ne, abu ne wanda ba iya Jihar Kano za a zaga ba, arewacin Nijeriya ma za a zaga, za a ce mu na da shugabanni daƙiƙai, jahilai, wanda ba su san me su ke yi ba.
“Me ya sa mu ke da ɗabi’a, wasu su ke da ɗabi’a ko wani ya ke da ɗabi’a irin ta dabbobi da tinkiyoyi?”
Waɗannan ba su ba ne iya bidiyoyin da Nabraska ya yi ya na yabon gwamnan Kano da ɗan takarar zama gwamnan ba. Haka kuma ba iya bidiyon da ya yi ya na cin mutuncin su ba a lokacin da baya tare da su a siyasance.
A duk lokacin da jarumin ya saki bidiyo ya na magana a kan Rarara ko gwamnan Kano da ɗan takarar gwamna, sai an fitar da wanda ya ci mutuncin su a baya.
Wannan kuma na fitowa ne daga shafukan mai taimaka wa Rarara a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, wanda shi ke maida wa Nabraska da martani a duk lokacin da ya taɓa ubangidan sa.
Hakan na nuna cewa a yanzu Nabraska ya samu damar da zai lashe dukkan aman da ya yi a baya.
![]()





