• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shugabancin ƙasa: Atiku ya yi alƙawarin fara sauya fasalin Nijeriya daga ranar da za a rantsar da shi

by DAGA WAKILIN MU
December 9, 2022
in Nijeriya
0
Hagu zuwa dama: Atiku Abubakar, mataimakin takarar sa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, da Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun a wajen taron

Hagu zuwa dama: Atiku Abubakar, mataimakin takarar sa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, da Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun a wajen taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin fara sauya fasalin Nijeriya daga ranar da ya zama shugaban ƙasa a 2023, idan ya yi nasarar lashe zaɓen.

Atiku, Wazirin Adamawa, ya yi wannan alƙawarin ne a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, lokacin da ya ƙaddamar da kamfen ɗin PDP a can.

Ya ce zai yi amfani da ajandar sa ta sauya fasalin Nijeriya domin ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar nan ta ke fama da fuskanta.

Ya ce daga lokacin da aka gama rantsar da shi zai fara aiwatar da ayyukan raya ƙasa ta hanyar sake fasalin Nijeriya.

Wazirin ya ce: “Babban muradin mu shi ne mu tabbatar mun kawar da dukkan matsalolin rashin tsaro, rarrabuwar kai, kawar da danne haƙƙin tattalin arzikin jama’a da samar da aikin yi ga matasa. Ina ɗaukar maku alƙawarin cewa tun daga ranar da aka naɗa ni shugaba idan na yi nasara a zaɓen 2023, zan aiwatar da su.” 

Atiku ya roƙi al’ummar Osun da su jefa masa ƙuri’un su domin ya cimma burin sa na ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da ya ce mulkin APC ya jefa ƙasar.

Ya ce: “Ba za mu kunyata ku ba, kuma ba za mu ci amanar ku kamar yadda APC ta ci amanar ku ba, saboda mu na da ƙwarewa da irin gogewar da Nijeriya ke matuƙar buƙata.”

Gwamna Ademola Adeleke, wanda aka rantsar kwanan nan, ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin gogagge kuma mai ƙwarewar da zai iya ceto Nijeriya, har ya magance matsaloli da ƙalubalen da su ka dabaibaye ta.

Loading

Tags: Ademola AdelekeAPCAtiku AbubakarIfeanyi OkowaOsogboOsunPDPshugabancin ƙasayaƙin neman zaɓeZaɓen 2023
Previous Post

Batun ‘mutuwar’ Kannywood: Darakta Hafizu Bello ya yi wa Salisu Officer martani

Next Post

Shekara 8 da rasuwa: Hannafi ɗan Ibro ya gode da addu’a, ya nemi a ci gaba da roƙa wa mahaifin sa gafara

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Marigayi Alhaji Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro)

Shekara 8 da rasuwa: Hannafi ɗan Ibro ya gode da addu'a, ya nemi a ci gaba da roƙa wa mahaifin sa gafara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!