• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sirrin Abdul D. One, yaron Umar M. Shariff

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 26, 2019
in Mawaƙa
0
Abdul D. One a cikin ofishin sa a Kaduna

Abdul D. One a cikin ofishin sa a Kaduna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
ABDULƘADIR Muhammad, wanda aka fi sani da Abdul D. One, a ya na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Hausa a yau.
 
Mawaƙin mai haskawa a Kannywood ya na da nasibi matuƙa, domin kuwa tun daga lokacin da aka fara jin waƙar sa ta fim ɗin ‘Mansoor’ mai taken ‘Abin Da Ya Ke Rai Na’ ake tambayar wanene ya rera ta? Tun daga lokacin Abdul ya samu karɓuwa.
 
Haka kuma Abdul ya na da ladabi da biyayya, ga girmama na gaba da shi. 
 
Wakilin mujallar Fim ya samu zantawa da shi kwanan nan a Kaduna, inda ya yi masa bayani a kan sirrin rayuwar sa da mutane ba su sani ba – misali tarihin sa da yadda ya fara waƙa da nasarorin sa, da waƙoƙin sa da batun aure da yadda ya haɗu da ubangidansa, wato shahararren mawaƙi kuma jarumin nan Umar M. Shariff, da dai sauran su, kamar haka:
 
FIM: Ka faɗa wa masu karatu tarihin ka a taƙaice.
 
ABDUL: Assalamu alaikum. Suna na Abdulƙadir Muhammad, amma an fi sani na da Abdul D. One. An haife ni a garin Funtuwa ta Jihar Katsina. Na yi karatu na firamare da sakandire duk a Funtuwa. Zan iya cewa harkar waƙa ita ta kawo ni Kaduna.
 
FIM: Me ya ja hankalin ka ka shiga harkar waƙa?
 
ABDUL: Gaskiya ni tun ina makaranta ba ni da wani da ya wuce nishaɗi, sannan ko a aji na kan tashi na yi waƙa ana yi mani kiɗa. To, wannan lamarin nawa ya samo asali tun daga makaranta ne. Tun daga wannan lokacin na fara sha’awar waƙa, na fara tara kuɗi, na fara zuwa situdiyo.
 
FIM: A Funtuwa ka fara waƙa ko sai da ka zo Kaduna?
 
ABDUL: A Funtua na fara waƙa, don a yanzu zai kai shekara goma.
 
FIM: Ya aka yi ka tsinci kan ka a Shariff Studio?
 
ABDUL: To, tsintar kai na a Shariff Studio wani lamari ne na Allah, domin duk inda Allah Ya so ya aje ka, in-sha Allahu a sannu zai kai ka wurin. Allah shi Ya kawo ni, babu tsimi, babu dabara ta.
 
Ba zan manta ba, wata rana Umar ya je Sokoto, ya na dawowa sai ya tsaya a Funtuwa zai ci abinci. A nan mu ka fara haɗuwa da shi. Haɗuwar da mu ka yi da shi a nan, sai ya ji waƙoƙi na har mu ka yi hoto da shi.
 
Sai wata rana ni da Baban Chinedu mun zo Kaduna, sai aka ce mani ai ofishin sa ya na can wurin kusa da inda za mu je. Sai na tsallaka mu ka gaisa. Da na je, ya yi mamakin gani na. A nan mu ka yi wata waƙa da aka saka ta a ‘Best of Jinin Jiki Na’ mai taken ‘Da Son Ki Na Taho’. A wannan ranar da mu ka haɗu da shi, a ranar mu ka yi waƙar ni da shi.
 
Cikin yardar Allah shi ne fa har ya dawo da ni nan wurin, ga shi har na zama ɗan Kaduna yanzu.
 
FIM: Bayan waƙa, ka na kiɗa. A Funtuwa ka koya ko sai da ka zo Kaduna?
 
ABDUL: Na fara koyon kiɗa tun daga Funtuwa, a wurin maigidan mu ana ce masa Hassan Crown; shi ma abokin su Umar ɗin ne. Da na dawo nan na ƙarasa rayuwa ta a nan ne.
 
FIM: Wace waƙa ka fara yi a rayuwar ka?
 
ABDUL: Wata waƙa ce ta wani kamfanin fiyawata. Waƙa ce ta talla haka.
 
FIM: Ka yi waƙoƙi nawa zuwa yanzu?
 
ABDUL: Gaskiya ban san adadin su ba, duk da dai ba su da yawa.
 
FIM: Duk da yake ka ɗan jima ka na waƙa, amma da waƙoƙin da ka yi na fim ɗin ‘Mansoor’ aka san ka. Me za ka ce?
 
FIM: Gaskiya ne waƙoƙin ‘Mansoor’ su ka fitar da ni, har su ka kai ni inda ma ni ban taɓa zuwa ba. Babu abin da zan ce zai dai yi wa Allah godiya, kasancewar abin da ka daɗe ka na jira ne kuma Ya ba ka.
 
FIM: Wace waƙa ce bakandamiyar Abdul D. One?
 
ABDUL: Bakandamiya ta ita ce waƙar ‘Abin Da Ya Ke Rai Na’. Wannan waƙa da ita duniya ta san ni, kafin sauran waƙoƙi na su biyo baya.
 
FIM: Me za ka ce game da wasu masu sayen waƙoƙin mawaƙa su je su yi bidiyo su fitar, har wasu mutane su na tunanin waƙoƙin su ne, wanda hakan ya taɓa mawaƙa da dama?
 
ABDUL: Gaskiya wannan lamari ya taɓa masana’antar fim sosai. To amma waɗanda su ke yin hakan su na buƙatar tallafi. Sai dai kuma masu tallafawan ne Allah bai kawo su ba. Amma daidai bakin gwargwado ana yi. Ka ga kamar Sarki Ali Nuhu ya na yin irin wannan taimakon, domin babu wanda ya kai shi fitar da sababbin jarumai a Kannywood.
 
To masana’antar ce ta na buƙatar gyara, kuma ana kan hanyar gyaran. Wata rana ma mai hawa waƙar zai tsinci kan shi a fim.
 
FIM: Ka na da ra’ayin zama jarumi kamar maigidan ka Umar?
 
ABDUL: Ina da sha’awar zama jarumi, domin in ka gan ni ma na yi kalan jaruman! Amma yanzu lokaci ne bai yi ba. So, ba a sauri, in Allah Ya so ya kai ka matsayin za ka je. In kuma Allah Ya ga dama ya ce ba za ka yi ba ma gaba ɗaya shi kenan babu yadda ka iya. Amma in Allah Ya nufa na zama jarumin sai ka ga na zama.
 
FIM: Wace ƙasa harkar waƙa ta kai ka?
 
ABDUL: Harkar waƙa ta yi mani komai. Amma dai a yanzu fita waje ban a wuce ƙasar Nijar, sai kuma a nan Nijeriya na je wurare da dama sosai. Bayan nan ban je wata ƙasa ba, amma ban a cire rai da zan je in-sha Allahu.
 
FIM: Ɓangaren nasarori da ka samu fa?
 
ABDUL: Nasarori ga su nan a zagaye a ofishi na kamar yadda ka ke gani.  Na samu awad da dama. Waɗannan ba ƙananan nasarori ba ne a wuri na.
 
Sannan babbar nasara ta a rayuwa, zama da iyaye na lafiya da na ke yi.
 
FIM: Ƙalubale kuma fa?
 
ABDUL: Gaskiya ƙalubale ana kan fuskanta a halin yanzu. Duk hanya ta nasara in babu ƙalubale ba a wucewa. Duk abin da ka ke yi in babu ƙalubale a cikin sa ka haƙura da shi kawai, ka canza wani. Saboda mai imani shi ke fuskantar ƙalubale don gwada imanin ka. Duk sana’a ta na da ƙalubale. Allah Ya fitar da mu lafiya.
 
FIM: Ka faɗa wa masu karatu fitattun waƙoƙin ka da za ka iya bugun ƙirji da su a ko ina.
 
FIM: Na farko zan iya bugun gaba da ‘Abin Da Ke Rai Na’, ‘Kar Ki Manta Da Ni’; babbar kuma wadda ta danne su ita ce ‘Mahaifiya’, ina bugun gaba da wannan waƙar sosai, sakamakon duk saƙwannin da ke cikin ta abin da ke faruwa yanzu ne.
 
FIM: Ka taɓa yin kundin waƙoƙi (album)?
 
ABDUL: Na taɓa yi, amma ba su wuce guda uku ba. Sai wanda mu ka yi da su Umar M. Shariff. A cikin su akwai ‘Na Riƙe So’, ‘Ke ce Tawa’, ‘ Saƙo Daga Zuciya’, sai kuma ‘Tushen Alƙawari’ da zan yi yanzu.
 
FIM: Ka taɓa yin bidiyo?
 
ABDUL: Ban yi bidiyo ba, amma zan yi nan ba da jimawa ba.
 
FIM: Yaushe za ka yi aure?
 
ABDUL: Zan yi aure in-sha Allah. Ina roƙon masoya su taya ni da addu’a, Allah Ya ba ni mata tagari, ba irin waɗanda su ke zagi na a soshiyal midiya ba.
 
FIM: A kasuwa ka ke ko kuma akwai ta a ƙasa?
 
ABDUL: (Dariya) Gaskiya ni ba a kasuwa na ke ba. Ina da wacce zan aura a ƙasa a yanzu haka. Lokaci kawai mu ke jira.
 
FIM: A ƙarshe, me za ka ce wa masoyan ka?
 
ABDUL: A kullum ina kira ga masoya na da mu rinƙa haɗuwa da su a shafukan sada zumunci na zamani. Kuma su rinƙa haƙuri da mu, musamman wurin kira. Kuma su ci gaba da saka mu a cikin addu’o’in su. Ina godiya a gare su matuƙa.

Loading

Previous Post

Samira Saje: Abin da ya sa na daina fim na kama sana’a

Next Post

Waƙar “Ƙarangiya” Ta Malam Mudi Sipikin

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Alhaji Mudi Sipikin a cikin 1980

Waƙar "Ƙarangiya" Ta Malam Mudi Sipikin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!