• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

by MUKHTAR YAKUBU
September 29, 2025
in Tattaunawa
0
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

Hajiya Maryam Sulaiman (Maryam CTV)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN ɗan samu lokaci ba a ganin fuskar jarumar Kannywood, Hajiya Maryam Sulaiman (Maryam CTV) a harkar aikin fim, wanda hakan ya sa mutane suka fara cigiyar inda ta shiga.

Jarumar da ta yi fice a fitowa a matsayin uwa a gidan manyan masu kuɗi a cikin fim wadda har ake yi mata laƙabi da “Matar Manya” ko “Hajiyar Falo”, ta daɗe ana damawa da ita, kuma har yanzu tauraruwar ta tana haskawa.

Wakilin mu ya nemi jin ta bakin Maryam CTV dangane da rashin ganin ta, kamar haka:

FIM: Hajiya, a ‘yan kwanakin nan ba a ganin ki a cikin harkar fim, don haka ne ma mutane suka fara tambayar ko ina kika shiga?

MARYAM CT : To, alhamdu lillah, ko da ba a gani na ba na daina harkar ba ne. Ka san kana taka ne Allah yana nasa, don haka ba na daina harkar fim ba ne, ba kuma hutu na tafi ba. Abin da ya faru ka san kusan shekara kenan na samu karaya a hannu, a lokacin aka yi ɗori na gida, to ashe hannu bai gyaru ba. Wannan ya sa na tafi Nijar aka ɗauki hoton hannun don a tabbatar mini da abin da yake faruwa, wannan kuma ya sa aka gano tsakanin ƙashi da ƙashi tsoka ta shiga kuma dole sai an yi mini aiki. To shi ne da na dawo na sake yin shiri na koma, aƙalla sai da na yi wata uku zuwa huɗu a Nijar, kuma alhamdu lillah a yanzu sauƙi ya samu na dawo har na fara ci gaba da aiki.

FIM: Ko ya kika ga sauyin rayuwa a zaman jinyar ki?

MARYAM CTV: To rayuwa alhamdu lillah Allah ya rufa mini asiri, domin tun kafin na tafi Nijar zaman jinya, ai na yi zaman jinya na shekara guda a nan, kuma Allah ya rufa mini asiri duk abin da nake yi lokacin ina aiki na buƙata ina yin sa a lokacin zaman jinya, babu abin da ya canza.

Kuma da na tafi Nijar zaman jinya, a can Yamai na zauna, kuma ina da aminan arziki, a wajen su na zauna na yi jinya, don kulawar da na samu ko a nan garin mu iya abin da za a yi mini kenan.

FIM: A yanzu kin samu darasi a zaman jinyar da kika yi ko yaya kike kallon rayuwa musamman ta fuskar harkar fim?

MARYAM CTV: Ka san ita jarrabawa haka take, kowa da kalar tasa, don haka da jarrabawa ta zo mini sai na karɓe ta da hannu biyu, domin ita jarrabawa, duk wani mumuni da Allah yake so, sai ya jarrabe shi. Don haka na yi wa Allah godiya na karɓi jarrabawar hannu biyu, kuma na samu taimakon sa, na samu kulawar jama’a, kuma na samu sauƙi fiye da yadda nake tunani. Don haka babu abin da zan ce sai godiyar Allah. Haka su ma jama’a da suka ba ni kulawa tsawon shekara guda da na shafe cikin rashin lafiyar nan, Allah ya saka musu da alheri.

FIM: A yanzu dai kin dawo harkar fim gaba ɗaya?

MARYAM CTV: Haka ne, don kuwa ban daɗe da dawowa ba sai na koma aka tabbatar mini da hannu ya yi kyau. Kuma da man Ina yin fim ɗin, amma dai ba sosai ba, tunda hannu idan bai gyaru ba to ba za a samu yadda ake so ba, domin shi fim ba a zaune ake yi ba, dole ana yi ana motsa hannu, idan ta kama ma a ce ka kai wa wani mari ko duka, ko ka yi wani abu da zai taɓa hannun. Don haka sai na rage, na ke yin wanda na san ba zan samu matsala a hannu ba. Amma a yanzu babu abin da ba na yi da hannu na.

FIM: Kina cikin matan fim da ake ganin masu kwarjini saboda irin rol ɗin da kika fi takawa na babbar mace. Ya kike ganin yanayin mu’amalar ki da jama’a ta wannan fuskar?

MARYAM CTV: Gaskiya alhamdu lillah, masoya na suna nuna mini ƙauna. Kuma mutuntaka da kamala mutum ne yake jawo wa kan sa, duk da yake abu ne daga Allah, amma ita rayuwa yadda mutum ya ɗauki kan sa haka mutane za su ɗauke shi, idan kana kiyaye mutuncin ka, sai mutune su gan ka da mutunci. Don haka ina ƙara godiya ga masoya na, don na samu kulawar su ta hanyar addu’o’i da kiran waya da zuwa har inda nake. Don haka babu abin da zan ce wa masoya sai dai Allah ya saka da alheri. Lokacin da na yi zaman jinya a gida na kullum cika yake da mutane da suke zuwa duba ni. Haka ma zaman da na yi a Yamai na ga tarin masoya, don haka sai godiya da fatan alheri tsakani na da masoya.

Kowa ya san ni ba ni da matsala ko da wani jarumi ko kamfanin shirya fim, don ita rayuwa idan ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi, kuma shi abokin sana’ar ka kamar ɗan’uwan ka ne. Kuma da na samu kai na a rashin lafiyar nan na san da hakan, domin kafin kowa ya zo kai na a cikin ‘yan uwa na su suka fara tsayawa a kai na, don akwai Sadiya Gyale ita ta fara tsayawa a kai na a asibiti, duk da dai ‘yar’uwa ce ta jini, amma hidimar da ta yi mini ko ɗan’uwa na bai yi mini ba. To saboda haka ni kowa ɗan’uwa na ɗauke shi a cikin harkar fim.

Hajiya Maryam CTV a wurin wani biki

FIM: Akwai wani kallo da ake yi wa ‘yan fim na cewa ba ku da tarbiyya. Ko ya kike ganin wannan maganar?

MARYAM CTV: Wannan shi ne abin da yake ɓata mini rai. Domin ko a gida ɗaya kuka taso, to kowa fa da irin halin sa, wani na kirki wani ba na kirki ba, kuma a haka nan za a haƙura a zauna. Don haka bai kamata ba a rinƙa haɗawa ana yi mana kuɗin goro ba, har da mu manya. Saboda mu dai iya yin mu idan muka ga yarinya ta yi abu ba daidai ba muna ƙoƙarin mu tsawatar mata. Idan ka ga mun kawar da kai, sai wadda muka ga ta zo da fitsara, to ka ga wannan ba ji za ta yi ba. To amma bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba.

Don haka ina kira ga jama’a idan an ga mun yi wani kuskure, to kamata ya yi a yi mana nasiha, a ja hankalin mu, don mu ma mutane ne kamar kowa, za mu iya yin daidai, kuma za mu iya yin ba daidai ba. Kuma ina ƙara yin godiya ga dukkan masoya na na duniya dangane da irin kulawar da suka ba ni. Allah ya saka wa kowa da alheri.

FIM: Madalla, mun gode.

MARYAM CTV: Ni ma na gode sosai

Loading

Tags: Maryam CTV
Previous Post

Tsohuwar jarumar Kannywood, Jamila Gamdare ta yi auren bazata

Next Post

Rasuwar Hauwa Lawan Maiturare ta girgiza marubuta

Related Posts

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje
Tattaunawa

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

December 14, 2025
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Next Post
Rasuwar Hauwa Lawan Maiturare ta girgiza marubuta

Rasuwar Hauwa Lawan Maiturare ta girgiza marubuta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!