• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 10, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tinubu ya amince da biyan kuɗin kafa Cibiyar Yaɗa Labarai ta UNESCO

by WAKILIN MU
December 4, 2024
in Nijeriya
0
Tinubu ya amince da biyan kuɗin kafa Cibiyar Yaɗa Labarai ta UNESCO

Daga dama: Alhaji Mohammed Idris, Dakta Tawfik Jelassi, da Dakta Hajo Sani a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da kuɗaɗe domin kafa Cibiyar Yaɗa Labarai ta UNESCO (Media and Information Literacy Institute, MIL) a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da suka yi da Mataimakin Darakta-Janar na UNESCO, Dakta Tawfik Jelassi, a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Idris, wanda ya bayyana hakan a gefen ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai ƙasar Faransa, ya bayyana irin goyon bayan da Shugaban Ƙasar ke bai wa aikin.

Ya ce:“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da goyon baya sosai ga aikin, kuma ya amince da fitar da duk wasu kuɗaɗen da ake buƙata domin cibiyar ta fara aiki nan take, wadda za ta kasance a Babban Birnin Tarayya.”

Ministan ya nuna jin daɗin sa ga UNESCO da ta bai wa Nijeriya haƙƙin kafa Cibiyar ta MIL, wadda ita ce kaɗai irin ta a duniya.

Ya tuna ganawar da ya yi da Dakta Jelassi a shekarar 2023, tare da jaddada aniyar Nijeriya na ganin cibiyar ta samu nasara.

Jelassi ya bayyana jin daɗin sa game da kafa cibiyar a Nijeriya tare da nanata muhimmancin sa wajen magance matsalolin da suka haɗa da yaɗa labaran ƙarya, da kalaman ƙiyayya. Ya kuma bayyana ƙoƙarin UNESCO na samar gidan yana mai aminci.

Har ila yau, ya gabatar da shirin UNESCO MIL Cities, wanda ke haɗa ilimin yaɗa labarai a cikin ayyukan birane, waɗanda suka haɗa da harkokin sufuri da al’adu.

Idris ya yi maraba da manufar MIL Cities kuma ya yi alƙawarin cewa Nijeriya za ta taka rawar gani ta hanyar zaɓar wani birni don aiwatar da matakin farko na shirin.

Ministan ya kuma ba da tabbacin cewa Nijeriya za ta yi amfani da ƙa’idojin UNESCO don Gudanar da Kafafen Gidan Yana, wanda ke da nufin inganta tunani da gaskiya tare da kare ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Idris ya samu rakiyar Jakadiyar Nijeriya kuma Babbar Wakiliya ga UNESCO, Dr. Hajo Sani, zuwa taron da aka gudanar a hedikwatar UNESCO.

Loading

Tags: aikin jaridaHajo SaniMILMohammed IdrisTawfik JelassiUNESCO
Previous Post

Tsohuwar jaruma a Kannywood, Rasheeda Maisa’a ta cika shekara ɗaya cif a ɗakin mijin ta

Next Post

Mawaƙi a Kannywood, El-Mu’az Birniwa ya riga mu gidan gaskiya

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Mawaƙi a Kannywood, El-Mu’az Birniwa ya riga mu gidan gaskiya

Mawaƙi a Kannywood, El-Mu'az Birniwa ya riga mu gidan gaskiya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!