TSOHUWAR jaruma a Kannywood, Maryam Musa Waziri, wadda aka fi sani da suna Laila a ciki shiri mai dogon zango na ‘Labari Na’, da mijin ta tsohon ɗan ƙwallon Nijeriya na Super Eagles, Tijjani Babangida, sun yi mummunan haɗarin mota a Zariya, Jihar Kaduna.
Mujallar Fim ta samu labarin cewa haɗarin ya auku ne a yammacin yau Alhamis a unguwar Ɗanmagaji da ke Zariya.
Haɗarin ya ritsa da Maryam da Tijjani Babangida da ɗan su Muhammad (Fadeel), da mai aikin su da kuma ƙanen mijin Maryam, wato Ibrahim Babangida (Aruza), wanda shi a take ya rasu.

Yanzu haka Maryam, Tijjani da Fadeel da mai aikin nasu su na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, Zariya, ƙarƙashin kulawar likitoci.
Wani hoto da aka wallafa a soshiyal midiya ya nuna yadda fuskar Maryam duk ta daddauje, musamman a gefen hagu. An daura mata bandeji kuma da alamun idon ta na hagu ya fashe.

Marigayi Aruza shi ma ya taɓa zama ɗan wasan Nijeriya a shekarun baya.
Allah ya jiƙan shi da rahama, su kuma sauran mutum huɗun Allah ya ba su lafiya.