Wannan waƙa ta Sarkin Kiɗa Hamisu Caji, Alhaji Magaji Galadima ne ya rubuto ta daga faifan waƙar a ranar 15/7/2014, saboda farin jinin ta. Bayan haka, Ibrahim Sheme ya yi ‘yan gyare-gyare a ciki. A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo, Hamisu ya ce yawancin labarin da ya bayar a waƙar, duk ƙirƙira ce.
*
Dawan da kututturai!
Dawan da mutsa-mutsai!
Inda magori ya shekara,
Can ya shekara ɗiban magani, Sabo!
(Kirari):
Kai kwaure na Iya Baba!
Ka ji dare na Iya Baba!
Kai baƙin ciki na Iya Baba!
(Jagora:)
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
Domin ka suke yin tauri,
Saboda kai aka nan saɓani,
Kuma har aka nan kaskaifi,
Da ba-duhu, layar zana,
Domin ka maza ke cin sagau.
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
Kai Sabo ko ibilishi ne kai?
Sabo ko shaiɗani ne kai?
Kan ba ibilishi ne ba,
Kan ba shaiɗani ne ba,
Kana da baƙin aljan,
Ko baƙin rauhani,
Da shi ka ke gama wannan magani.
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
A ran da an yi farautar kura,
An fashe an bash shi,
Arnen ya kwan a cikin darbejiya.
Ya kwana a ɗakin kura,
Kura ta gudu ba ta nan,
Da safe da sassafe,
Mai abin mamakin,
Ya sungumo wata mesa sai ya ci!
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
Mai abin mamaki,
Ɗan Falgore na ƙarshen zamani.
Sabo kwauren ƙirya ne kai:
A shekara sarawa amma a samu na girkawa da kyar.
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
A ran da an yi farautar kura,
Sai yai sulke da baƙin warki,
I yafa baƙin kurtu,
Sai ya murɗa baƙin kambu nai,
Ya ɗau wata laya Sabo,
Ya cunkusa a cikin baki nai,
Mai abin mamakin, da ya gan ta ta gan shi kura, arnen sai ya yiwo fito ta zo!
Na raɓe da kai ko Sabo,
Ba ya rasa girken magani.
Mai abin mamaki Sabo,
Mutan Arewa suna fatan ya je.
Sabo kwauren ƙirya ne kai:
A shekara sarawa amma a samu na girkawa da kyar.
Haliƙul dayyanu,
Allah mai yi wa bawa arziki.
Dakata ka ji, mai roƙo na,
Akwai magana a baki na,
Da za ka tsaya da na faɗa!
Amma Sabo Wakilin Tauri,
Ni ban daɗa tsinkewa ba,
Ban ƙara yin mamaki ba,
Sai a cikin kwanan can Sabo,
Sabo yai tafiya ran nan,
Da ya tad da masu farauta arna,
Ga waɗansu da gitta a hannu,
Da gatari da baƙar adda,
Sai aka danna uwar kora,
Kora tai kora!
Naman ya hwaɗi,
Mai abin mamaki Sabo,
Da ya murɗa baƙin kambu nai,
Ya danne naman,
Sai saran sa suke ba ya taɓo!
Sabo kwauren ƙirya ne kai:
A shekara sarawa amma a samu na girkawa da kyar!
Ayye Sabo Wakilin Tauri!
Shi yai magana ran nan,
Shi ne ya faɗa ran nan,
Bakwai ga watan gobe,
Za a samo zarto Sabo,
A samu mutum metan,
Ga ɗari bayan sa,
Ɗari a gaban sa Sabo
Mai abin mamaki,
Ya tashi ya ɓalle durwa,
To du ya yi tsarki su sha!
Marga-margan dutse Sabo,
Ɗanwaire na ƙarshen zamani.
Ayye karon mu na ƙofar Binni,
Abin da sukai ran nan,
Ran nan Ubangiji Allah ya tsare!
Ranar karon su a ƙofar Binni,
Ran da sun yi gumaza Sabo,
Ran Allah doki shi Sabo,
Ran Allah ba su wuya ran nan,
Shi kuma sun doko shi Sabo,
Ran Allah ba su wuya ran nan,
Ni makaɗin ganga ina cikin bukka na rakaɓe.
Abin da akai ran nan,
Ɗanbalaya na ƙofa,
Saboda Rasulallah rannan na yaba wannan ɗan gajere!
A ran Allah kakkare ni ya tare a lungun nan,
Ni ran nan na yaba wannan ɗan gajere!
Abin da akai ran nan,
Ni na yi jugum ran nan,
Na rakaɓe a jikin garu,
Na rage fitila ran nan
Nai tsuguno ran nan
Ran nan na yi salati yai ɗari!
Ayye karon mu na ƙofar Binni,
Kiɗan da mukai ran nan,
Ni na rantse da Rasulullah,
Han na kuma rantsewa,
Da du irin ka muke da sai mu shiga.
Ayye abin da akai ran nan,
Na ga an buga ƙato har ƙas,
An kuma raraki ƙato ya kai,
Sai na tashi da ‘yar ganga ta,
To, da na ɗau riga ta,
Sai na ce wa da ‘yan amshi ni nai gaba!
Na figi kwari ran nan,
Sai na tsallaka ta cikin haure,
Ni kuwa ban shiga mota ba,
Da sawu da sawaye na,
Da safe da sassafe,
Ran nan mutan Bichi ni baƙon su ne.
Ɗanbala ‘yan amshi na,
Albishirin ku kuma,
Albishirin ku kuma,
Ranar karon mu a ƙofar Binni,
A cikin ku cikin ku ba ni na ɓuya a taskar ƙofa ba.
Abin da akai ran nan,
Ubangiji Allah ya sauwaƙe!
Haba! ‘Yan amshi na gaishe ku da aiki,
Don kun taɓa kun saba kun gani,
Marga-margan dutse,
Jaki sha duka,
Ɗanwaire na ƙarshen zamani.
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
Iya da baƙin kambu,
Da zuciyar sa ta ɓaci Sabo,
Sai ya murɗa baƙin kambu,
Gwauron Dutse ta narke,
Ya ɗauki Dala ya kai Panshekara!
Mai abin mamaki,
Ɗan Falgore na ƙarshen zamani,
Dutse na Iya Baba,
Kai dutse kake ba ka fargaba!
Sabo kwauren ƙirya ne kai:
A shekara sarawa amma a samu na girkawa da ƙyar!
Ayye Sabo Wakilin Tauri,
Shi ya ci mana reza Sabo,
Ya cinye baƙin kwaɗo,
Sannan ya fidda wuta mai balbali.
Sallau kam ba kai ba wa zai ci kunama,
Wa zai ci gam farar tumfafiya,
Auliya’a maza Sallau,
Irin sha’anin Sallau ba duka ‘yan tauri kan yi shi ba.
* Alhaji Magaji Galadima shi ne Kachallan Kano