HADIZA Maikano tana ɗaya daga cikin mawaƙa na sahun farko a Kannywood, waɗanda suka yi tashe a shekarun baya. Ta yi waƙoƙi masu yawa tun a da, kuma har zuwa yanzu ana damawa da ita.
A cikin tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, fitacciyar sha’irar ta bayyana yadda harkar waƙa take a da da kuma yanzu da aka samu sauyi na ci-gaban zamani. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
FIM: Hadiza Maikano, kina ɗaya daga cikin mawaƙa da suka shafe tsawon lokaci suna sharafin su a Kannywood. Ko ya kike ganin yadda harkar take a yanzu da kuma da?
HADIZA MAIKANO: To, an samu ci-gaba, tunda kullum ci-gaba ake samu. Kuma an samu ƙaruwa a cikin harkar, tunda a da mata ba su da yawa, yanzu kuma an samu ƙaruwar mata da ba a san adadin su ba. Sai dai kawai dai abin yadda yake a da kamar ya ɗan fi tsari.
FIM: Tsari kamar ta wane ɓangare kenan?
HADIZA MAIKANO: Kamar a da mawaƙan an san adadin su, amma a yanzu kowa mawaƙi ne, sai ka gama yawon ka ma ba ka san iya adadin mawaƙan ba. To za a iya kiran sa ci-gaba ta wani fannin.
FIM: A da, mawaƙa mata sun fi rubutun waƙa da kuma rera ta, amma a yanzu ana ganin kamar masu amshi sun fi yawa.
HADIZA MAIKANO: E, a da ɗin ma hakan ne, ko a da ɗin ana rubutawa kuma ana yin amshin, tunda mafi akasari sai ka fara da amshin sannan kai ma ka zo ka goge ka fara rubutawa. Kusan ma dai a yanzu masu rubutawar ba su da yawa kamar masu rerawar.
FIM: Da yake kin jima a harkar, masu karatu za su so jin waƙoƙin da suka fito da ke tun a wancan lokacin.
HADIZA MAIKANO: To waƙoƙi ka san yadda suke, akwai waƙoƙin ‘Gambiza’, ‘Man Taiga’, ‘Zabari’, ‘Jamila Ta Iya Ɗaura Zane’, suna dai da yawa gaskiya.

FIM: A yanzu waɗanne irin waƙoƙi kika fi yi?
HADIZA MAIKANO: A yanzu gaskiya na fi yin waƙoƙin siyasa, amma ba lallai ba ne ka san su saboda ban cika yin waƙar siyasa a Kano ba, amma ni dai a yanzu na fi yin waƙoƙin siyasa.
FIM: Yaya yanayin cin gajiyar waƙa yake tsakanin na siyasa da na fim?
HADIZA MAIKANO: Ita waƙar siyasa tana kawo kuɗi, saboda za ka samu alheri, za ka san manyan mutane. Ita kuma waƙar fim suna take sawa; za ka yi suna a waƙar fim amma ba kuɗi.
FIM: Wace irin gudunmawa kuke bai wa al’umma a matsayin ku na mawaƙa?
HADIZA MAIKANO: To ita gudunmawa a ɓangaren waƙa ba yau muka fara bayar da ita ba, an daɗe ana bayar da ita, tunda kusan abubuwan da ake faɗa a waƙar ana amfana da su, tunda ko a da an san waƙoƙin mu ba na batsa ba ne, waƙoƙi ne na faɗakarwa.
FIM: Wane irin jan hankali za ki yi ga mawaƙa, musamman na wannan lokacin?
HADIZA MAIKANO: E to, haɗin kai da riƙe mutuncin juna. Hassada a cire ta, a dunƙule waje ɗaya a amfana da juna. Shi ne jan hankalin da zan yi.
FIM: To madalla, mun gode.
HADIZA MAIKANO: Ni ma na gode.