SANANNEN jarumi, mawaƙi kuma furodusa T.Y. Shaban ya bayyana cewa nasarar da ya samu ta zama mataimakin gwarzon jarumi (supporting actor) a gasar zakarun mawaƙa da jarumai ta Afrika ta Yamma (West African Music and Movie Awards, WAMMA Awards) ta bana ta ƙara masa azama wajen shirya finafinan da kowa zai yi alfahari da su.
An yi bikin gasar ne a babban ɗakin taro na Palais des Congress da ke Yamai, babban birnin ƙasar Nijar, a ranar Lahadi, 19 ga Satumba, 2021.

Taron na ‘WAMMA Awards’, karo na 7, ya samu halartar ƙasashen Afrika kimanin 17.
T.Y. Shaban, wanda kuma shi ne jagoran kamfanin Blue Sound da ke Kano, ya samu wannan lambar ne ne sakamakon rawar da ya taka a fim ɗin ‘Tauraron Ɓoye’ inda ya fito a matsayin mai taimaka wa jarumi.
Da ya ke ƙarin haske kan wannan nasara da ya samu, jarumin ya shaida wa mujallar Fim cewa, ”Mu na gode wa Allah da ya ba mu wannan nasarar. Wannan WAMMA ɗin na shekarar nan ya zama na musamman saboda akwai karon batta tsakanin ƙasashe 15 wanda ya haɗa da Nijar, Ghana, Nijeriya, Cameron, Togo, Benin da sauran su, to an shiga.
“Idan ka na ma taƙama kai jarumi ne, ka je ka ga jarumai. Kuma an shiga da finafinai wanda aka yi su da tunani wataƙila ba irin naka tunanin ba ko tunanin wani ba irin nasu ba. To an gwabza an yi zube-ban-ƙwarya.
“Kuma mu da mu ka fito daga Nijeriya, Allah ya ba mu sa’a mun ci ribar wannan tafiyar.

”Ni kai na, kamfani na na Blue Sound Multimedia ya samu lambar karramawa har guda huɗu, wanda ni kai na na samu gwarzon mai taimaka wa jarumi da fim ɗi na na ‘Tauraron Ɓoye’, sannan fim ɗin ‘Tauraron Ɓoye’ ya samu karramawa a matsayin wanda ya fi zayyanar sutura da aka sa a cikin sa.
“Sannan akwai waƙar ɗa na, wato Freiiboy Shaba, mai suna ‘Amarya’, ta samu karramawa kan bidiyon da ya fi tsaruwa. Sannan daraktan da ya bada umarnin wannan bidiyon shi ma ya samu karramawa. Kuma ban da mu akwai waɗanda su ka fito daga wasu garuruwan da ke cikin wannan ƙasa.
“To a taƙaice dai mu ‘yan Nijeriya mu ne mu ka fi samun nasara a cikin wannan gasa wanda kuma ƙasar Togo su ke biye mana, wato na biyu, sai kuma Benin da Ghana da su ka biyo mu.”
Ya ƙara da cewa wannan nasara za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukan sa tare da inganta su yadda za su yi daidai da zamani.

TY Shaban ya kuma ce a shirye su ke a duk lokacin da dama irin wannan ta samu su shiga domin su ƙaro ilimi da yadda da a yi jihar su da ƙasa baki ɗaya su yi alfahari da su.
Daga nan ya ja hankalin ‘yan Kannywood da su tashi su ƙara jajircewa wajen neman ilimi domin ta haka ne kawai za su tsallake duk wani ƙalubale da ya ke gaban su.

Jarumin ya gode wa abokan sana’ar sa bisa taya su murna da goyon baya da addu’o’i da su ka dinga yi musu kan wannan abu har zuwa samun nasarar su.