• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Wasiƙa zuwa ga Malam Abdallah Gadon-Ƙaya

by DAGA FATUHU MUSTAPHA
January 24, 2022
in Tsokaci
0
Sheikh Abdallah Usman Gadon Ƙaya

Sheikh Abdallah Usman Gadon Ƙaya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAYAN gaisuwa tare da girmamawa, ina maka sallama irin ta addinin Musulunci. Ina fata za ka kalli wannan wasiƙa da idon basira, domin ina da tabbacin za ta yi maka da al’ummar Musulmi baki ɗaya amfani. 

Zan fara da sanar maka ni ba mabiyin ɗarikar Salafiyya ba ne, amma kuma ina ganin girman malamai, saboda ina sane da irin rawar da ku ke takawa wurin yaɗa ilmin Islama. Sai dai kash! Na lura ana neman a yi wa abin gyaran gangar Abzinawa, ko kuma ana neman garin gyaran gira a rasa ido. 

Ina so ka sani cewa muhimmancin malami a al’umma a yau, a kuma Arewacin Nijeriya, a wurin talaka ya wuce muhimmancin dukkan wani mai riƙe da madafar iko a ƙasar nan, domin kuwa mabiyan ka da masu sauraron ku su na ganin cewa duk abin da ku ka faɗa to kawai umarni ne daga Allah, don haka ba su da wani zaɓi illa su bi. Don haka ya kamata malamai irin ka da su ke da ɗimbin mabiya da masu saurare su riƙa taka-tsantsan wurin maganganun su. 

Maganganu biyu da ka yi sun ba ni mamaki, kuma a gaskiya ban zaci su fito daga wurin ka ba. 

Na farko dai, kusan shekara guda da ta wuce, an jiyo ka ka na bada labarin wani ya gaya maka cewa ana zina a cikin gidan sinima na Film House da ke katafaren shagon nan na Shoprite. Ina ganin a ƙa’ida kafin ka bayyana wannan magana ya kamata ka bincika, ka tabbatar da cewa haka ne, kuma ka nemi masu wajen ka sanar da su domin su ɗau mataki wurin hana wannan mummunar ɗabi’a. 

A matsayi na na kolo a karatun addini, ni kai na na san yadda Musulunci ya tsaurara shaidar zina, ya kuma ɗau mataki tsattsaura a kan wanda zai bayar da shaidar zina. To amma sai na ga ka yi amfani da shaidar mutum ɗaya, wanda na yi imanin ba zai iya tsayawa a gaban kotun shari’a ya kare kan sa ba. 

Ni ina ganin ya kamata irin waɗannan labarai da ake kawo wa malam, ya riƙa kallon su da idon basira. 

Illar irin wannan kira naka shi ne in ba a yi a hankali ba, in har kowa zai ɗau matakin doka a hannun sa, to wata rana za a haifi ɗan da ba ido, domin ko da neman budurwa ya haɗa mu da mutum, in na ga zai kasa ni, zan iya tunzura mutane a kan sa, su halaka shi

Amma babban abin da ya tayar min da hankali shi ne maganganun ka da na ji a kan kisan Hanifa Abubakar, inda ka yi kira da a kashe shi wannan mugun iri da ya aikata wannan mummunan abu. Abin tsoron shi ne, a fahimta ta, kira ka yi ga mutane da su kashe wannan mutum, wanda ni a gani na bai kamata malami kamar ka ya yi kalaman tunzura mutane da su ɗau hukunci a hannun su ba. Na so a ce kira ka yi ga gwamnati da ta ɗau mataki cikin gaggawa ta aika da wannan mutum kotu, kuma ka yi kira ga alƙalai da su gaggauta shari’ar, su yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata. 

Illar irin wannan kira naka shi ne in ba a yi a hankali ba, in har kowa zai ɗau matakin doka a hannun sa, to wata rana za a haifi ɗan da ba ido, domin ko da neman budurwa ya haɗa mu da mutum, in na ga zai kasa ni, zan iya tunzura mutane a kan sa, su halaka shi. 

Ko shakka babu,  tsarin shari’a a Nijeriya tsari ne mai wahala da kuma murɗe-murɗe a cikin sa. Hakan ya sa yanke hukunci ke da matuƙar wahala. Hakan ya sanya mutane da yawa sun yanke tsammanin samun adalci daga irin wannan tsari. To amma duk da haka, da babu wawa, gara da wawa. Ko ba komai tsarin dai ya na rage yawan aikata laifuka, kuma a ƙarshe komai daren daɗewa zai yanke hukunci. 

Kila ba ka san lokacin da aka yi shari’ar Sahalatu ba a Kano, wadda ta banka wa mijin ta wuta a sakamakon zai yi mata kishiya. Amma shekara biyu baya, Sahalatu ta gama zaman ta na gidan yari ta fito. Wannan na nuni da cewa ko ma ina aka je aka dawo, a bar wa shari’a aikin ta shi ne abu mafi amfani a cikin al’umma.
Sarkin Zazzau Kwasau ya taɓa yanke hukunci cikin gaggawa, kuma har ya mutu ya na da-na-sani. 

A nuna wa al’umma muhimmancin son juna, da kyakkyawar mu’amala da biyayya ga shugabanni shi ne abin da zai tserar da wannan yanki namu daga fitinar da ya samu kan sa ta kashe-kashe da zubar da jini a tsakanin al’umma. 

Ina fata Malam zai kalli wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa tawa da idon basira. 

Allah ya ƙara wa Malam lafiya da nisan kwana da imani. 

Wassalam.

Naka, 
Muhammad Fatuhu Mustapha.

Loading

Tags: Film HouseHanifa AbubakarmalamaiSahalatuSalafiyyaSarkin Zazzau Kwasaushari'aSheikh Abdallah Usman Gadon Ƙayawa'azi
Previous Post

Zargin satar kuɗin tallafi: Gwamnan Bauchi ya shirga ƙarya, inji Ma’aikata

Next Post

Za mu tsarkake Kannywood, inji sabon shugaban ƙungiyar furodusoshin Arewa Sani Sule Katsina

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Alhaji Sani Sule Katsina riƙe da satifiket ɗin sa na zama sabon shugaban AFMAN

Za mu tsarkake Kannywood, inji sabon shugaban ƙungiyar furodusoshin Arewa Sani Sule Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!