A YANZU an samu cigaban zamani da duk wata harka da mutum ya ke yi idan ya so ya daidaita ta yadda za ta tafi da zamani cikin ɗan lokaci zai samu amfanin abin.
Hajiya Jamila Umar Tanko (JUT) shahararriyar marubuciya ce wadda ta yi amfani da damar da ta samu a harkar rubutun littafi ta zo a yanzu ta zama babbar ‘yar kasuwa ta duniya ta wajen amfani da soshiyal midiya. A kan haka ne mujallar Fim ta zanta da ita domin jin yadda ta fara da kuma matakin da ta kai a yanzu.
Dangane da yadda ta fara, JUT ta ce: “To alhamdu lillah. Kamar yadda kowa ya sani, Jamila Umar Tanko dai ni marubuciya ce ta littattafan Hausa, kuma na rubuta littattafai masu yawa, tun a lokacin da mu ke yin cinikin littattafan a kasuwa wanda a lokacin ko guda dubu nawa ka buga zai ƙare ka haɗa kuɗin ka, in dai ka samu mai kular maka da kayan.
“Wannan ta sa har mata mu ka yi ta buɗe kantin sayar da littafi, mu na yin kasuwancin da kan mu.
“To kuma dai daga baya sai kasuwancin ya sauya, aka daina sayen littafin saboda cigaban zamani da aka samu da kuma rashin kuɗi. Sannan kuma ga cigaban kimiyya; komai ya koma soshiyal midiya, don haka shi ma rubutun sai mu ka mayar da shi a shafukan YouTube, Facebook, Instagram da kuma guruf na WhatsApp inda ake biyan mu kuɗi ana karantawa.
“Wannan sai ya ba mu damar ƙulla alaƙa da masu karatun da yawa da su ka daɗe ba sa jin mu. Sai kuma mu ka samu ƙarin wasu a soshiyal midiya waɗanda ba mu san su ba sai da mu ka shiga. Wasu su na jin labarin mu a matsayin marubuta, amma dai ba su san mu ba. Wasu kuma sai a lokacin su ka san mu, su ka fara karanta rubutun mu kuma mu ka saba da su.”
Dangane da yadda ta fara kasuwancin kuwa, JUT ta ce: “To, ganin yadda mutanen da mu ke tare da su na ga su na da yawa, sai na yi amfani da wannan damar na fara tallar kayan yara, wanda da man ina sayar da su. Don haka sai na fara tallar su a shafukan da na ke amfani da su, sai mutane su ka fara turo kuɗi daga garuruwa ina tura musu, tun ina sayar da ɗaya, biyu, uku har na zo ina bayar da sari.
“Da abin ya bunƙasa sai na koma ina shigo da kaya daga Chana, Dubai da Indiya, kuma duk ta hanyar soshiyal midiya ɗin, domin ta nan za a turo mini na gani a faɗa mini farashi na biya.
“Kuma su ma waɗanda zan sayar wa ɗin, ta nan za su gani mu yi ciniki na tura musu su turo mini da kuɗi na.

“Kuma wannan ta sa na samu damar da na shiga harkar kasuwancin gidaje wanda a yanzu na ke yin ta sosai. Don a yanzu ina da manyan gidaje da su ke a garuruwan Kano, Kaduna, Abuja, duk na sayarwa. Kuma duk ta dalilin harkar rubutun littafi na samu wannan damar. Ka ga kuwa harkar rubutun littafi ta samar mini da dama a rayuwa ta.”
Mun tambayi Hajiya Jamila saƙon ta ga marubuta. Sai ta amsa: “Gaskiya ina kira a gare su, musamman ma dai mata, abin da zan ce musu shi ne su riƙe kasuwancin zamani, domin shi ne za su yi suna cikin gidan su a zaune a ɗaki ba tare da sun je ko’ina ba.
“Za su yi kasuwancin su ta waya su samu kuɗin su. Don haka mata a yi sana’a wadda za ta tsare mana mutunci da rayuwar mu.”
To, Allah ya sa sun ji.