• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yawan masu rajistar zaɓe a Nijeriya sun haura na sauran ƙasashen Afrika ta Yamma – INEC

by DAGA WAKILIN MU
December 25, 2021
in Nijeriya
0
Yawan masu rajistar zaɓe a Nijeriya sun haura na sauran ƙasashen Afrika ta Yamma – INEC
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfasa Mahmood Yakubu, ya ce yawan masu rajistar jefa ƙuri’a a Nijeriya ya haura yawan masu rajistar jefa ƙuri’a a sauran ƙasashen Afrika guda 14 baki ɗayan su.

Yakubu ya yi wannan bayani ne kwanan baya a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a Legas.

Ya ce yawan masu jefa ƙuri’a a Nijeriya ya kai mutum 84,004,084, yayin da yawan masu jefa ƙuri’a a sauran ƙasashen Afrika ta Yamma 14 ban da Nijeriya mutum miliyan 73.6 ne. 

Ya ce, “Saboda haka yawan masu jefa ƙuri’a a Nijeriya ya haura yawan na sauran ƙasashen Afrika ta Yamma 14 gaba ɗaya da mutum har miliyan 11.

“A yanzu mu na da rumfunan zaɓe 176,846 yawan mazaɓu kuma ya kai 8,809.

“Mun yi namijin ƙoƙarin ganin mun samu ƙarin mazaɓu ne saboda la’akarin da mu ka yi cewa kusan daga 1999 zuwa 2015 ana samun ƙaruwar yawan masu jefa ƙuri’a.  Amma zuwa 2021 sun ƙaru sosai har sun kai 84,044,084. Kuma har zuwa 2015 yawan rumfunan zaɓe bai ƙaru ba.

“Dalili kenan na yin ƙoƙarin da mu ka yi na samar da ƙarin rufunan zaɓe 56,873 cikin watan Afrilu, 2021. Yanzu mu na da guda 176, 846 kenan.”

Haka nan ya yi tsokacin cewa ƙarin yawan rumfunan zaɓe ya faru ne saboda yawan masu jefa ƙuri’a da aka ƙara samu sosai. Kuma ya yi mamakin yadda wasu mutane su ka riƙa yi wa wannan ƙarin yawan rumfunan zaɓe mummunar fahimta.

Yakubu ya ce an yi rajistar masu zaɓe 57,908,945 a zaɓen 1999. A zaɓen 2003 kuma an yi wa mutum 60,823,022. Sai kuma mutum 61,567,036 a zaɓen 2007.

A zaɓen 2015 an yi wa mutum 67,422,005. A zaɓen 2019 kuma an yi wa mutum 84,004,084 rajista.

Hakan na nufin yawan masu rajista a Nijeriya za su ƙaru sosai, idan aka haɗa da yawan waɗanda ake ci gaba da yi wa rajista a yanzu.

Loading

Tags: Independent National Electoral CommissionINECProf. Mahmood Yakubuvoters registerZaɓen 2023
Previous Post

INEC na buƙatar N305b domin shirya zaɓen 2023

Next Post

Kirsimeti

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Kyaututtukan Kirsimeti

Kirsimeti

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!