HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) mai ofis a Ƙaramar Hukumar Kuje da ke Gundumar Birnin Tarayya (FCT) ta bayar da tabbaci ga masu zaɓe cewa za ta tabbatar da inganci da adalci a zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a yankin kwanan nan.
Idan ba a manta ba, za a gudanar da zaɓen ciyamomi da kansiloli a gundumar ta FCT ne a ranar 12 ga wannan watan na Fabrairu.
Jami’ar Zaɓe ta INEC mai kula da yankin Kuje, Madam Zainab Gbefwi, ita ce ta bayar da wannan tabbacin a lokacin da ta yi hira da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya a ranar Alhamis, a wajen wani taron horaswa da aka shirya wa ma’aikatan wucin-gadi na zaɓen.
Zainab Gbefwi ta ce hukumar za ta yi amfani da dukkan ma’aikata da kayan aiki da kuma ƙwarewar ta wajen tabbatar da cewa an yi zaɓe fisabilillahi, mai nagarta kuma wanda kowa zai yi na’am da shi.
Ta ce, “Kamar yadda Dokar Zaɓe da kuma Tsarin Mulki na 1999 su ka tanadar, haƙƙin jama’ar ƙasa ne su samu katin zaɓe kuma su zaɓi ‘yan takarar da su ke so.
“’Yan takarar su na da babbar rawar da za su taka ta hanyar yin nagana da magoya bayan su don su yi ɗabi’a mai kyau kuma su ja kunnen su dangane da haɗari da matsalolin da ke tattare da aikata maguɗin zaɓe.
“Wannan kiran ya na da muhimmanci domin ban da ƙara ƙarfi wajen zaɓe, shi kaɗai ne kuma makamin da masu zaɓe za su iya yin amfani da shi wajen zaɓa wa kan su shugabanni.”
Haka kuma ta yi kira ga ‘yan takara da magoya bayan su da masu zaɓe da su tabbatar da cewa sun kiyaye dukkan ƙa’idojin kare kai daga cutar korona (COVID-19) a rumfunan zaɓe a lokacin zaɓen.
Kuma ta yi kira ga ‘yan takara da magoya bayan su da su kiyayi aikata duk wani abu da ya shafi maguɗin zaɓe don a tabbatar da gudanar da zaɓe mai nagarta a cikin kwanciyar hankali saboda a ciyar da mulkin dimokiraɗiyya gaba a ƙasar nan.
Wata daga cikin ma’aikatan da aka horas ɗin, Juliet Nuhu, ta faɗa wa wakilin NAN cewa za ta tabbatar da an yi ɗa’a da doka a lokacin zaɓen a Kuje.
Wakilin NAN ya ruwaito cewa yawancin ma’aikatan wucin-gadi da su ka halarci taron horaswar ‘yan bautar ƙasa ne, wato NYSC, da kuma malaman makaranta da masu neman aiki waɗanda su ka kammala karatun jami’a.