• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Atiku ya sha alwashin ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin iko

by DAGA WAKILIN MU
January 19, 2023
in Nijeriya
0
Atiku tare da shugabannin PDP a taron Ibadan a ranar Alhamis

Atiku tare da shugabannin PDP a taron Ibadan a ranar Alhamis

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana ƙudirin sa na ƙara wa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin gudanar da mulkin su idan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a watan gobe.

Atiku ya faɗi haka ne a taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wanda aka yi a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, a ranar Alhamis.

A jawabin sa kan shirin da ya yi wa ƙasar nan a wajen taron, wanda aka yi a Zauren Mapo, Atiku ya ce a ƙarƙashin gwamnatin sa za a sake fasalin mulkin ƙasar nan ta yadda za a tabbatar da cewa an ƙara wa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ikon gudanar da mulki. 

Ya ce, “An san mutanen yankin Kudu-maso-yamma da neman a sauya fasalin ƙasar nan. Idan an ce sauya fasali, mu na nufin a ba da ƙarin ikon mulki ga jihohi da ƙarin kuɗi. Ko kun fahimci hakan? Ko kun amince da a yi hakan?

“Ya na daga cikin ginshiƙai biyar na shirye-shiryen mu don mu aiwatar da sauyin fasalin ƙasar nan — manufa ita ce mu ba ku ƙarin kuɗi da ƙarin ikon mulki ta yadda za ku iya haɓaka yankunan ku da jihohin ku da ƙananan hukumomin ku. Wannan shi ne mu ka sa a gaba.

.

“Haka kuma, mun ƙudiri aniyar tabbatar da ba za a ƙara yin yajin aiki a jami’o’in mu ba — manufa za mu ba jami’o’in mu isassun kuɗi tare da biyan malaman mu a kan lokaci ta yadda ba za mu samu wani cikas a  harkokin ilimin mu ba.

“Tilas mu tabbatar da cewa mun rungumi kowa da kowa. Kowane ɓangare na ƙasar nan zai samu wakilci a gwamnatin mu.

“Haka kuma mun ƙudiri aniyar tabbatar da mun samar da tsaron ƙasar mu don tabbatar da an samu kwanciyar hankali, tare da bin doka da oda a kowane ɓangare na ƙasar nan. Wannan shi ne abin da mu ka ƙudirta.”

Bugu da ƙari a jawabin nasa, Atiku ya yaba wa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo kan yadda ya tabbatar da cewa taron yaƙin neman zaɓen ya shiryu sosai. 

Dandazon magoya bayan Atiku a Ibadan a ranar Alhamis

Duk da yake gwamnan bai halarci taron ba, Atiku ya ce, “Jama’ar Jihar Oyo, bari in yi amfani da wannan damar in ƙara yin godiya ga Gwamna Makinde da jam’iyyar PDP reshen Jihar Oyo saboda yadda su ka tabbatar da cewa wannan taron ya shiryu matuƙa kuma an yayata shi sosai.”

Shi ma Shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya yaba wa Makinde saboda “nasarar da aka samu” a wajen kamfen ɗin jam’iyyar a jihar.

Makinde dai ya na cikin gwamnonin nan na PDP guda biyar waɗanda ake kira G5, wato waɗanda su ka ware kan su daga kamfen ɗin da Atiku ke yi a faɗin ƙasar nan.

Sun yi hakan ne bisa kasa samun biyan buƙatar su ta lallai sai Ayu ya yi murabus daga kujerar sa ta shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Gwamnonin su ne Nyesom Wike na Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na Inugu, Samuel Ortom na Binuwai, Seyi Makinde na Oyo, da Okezie Ikpeazu na Abiya.

Loading

Previous Post

Abin da ya sa na rage fitowa a fim – Maryam CTV

Next Post

Mutuwar Kamal Aboki darasi ce a gare mu, inji jarumin Kannywood BMB

Related Posts

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Next Post
Marigayi Kamal Aboki

Mutuwar Kamal Aboki darasi ce a gare mu, inji jarumin Kannywood BMB

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!