HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu cewa za ta rufe rumbun ta na intanet (portal) inda ta ke tattara sunayen ‘yan takarar zaɓuɓɓukan 2023 a ranakun 17 ga Yuni da kuma 15 ga Yuli.
Ta ce za ta rufe karɓar sunayen ‘yan takarar zaɓen shugaban ƙasa da mataimakin sa, sanatoci da wakilan tarayya a ranar 17 ga Yuni, sai sunayen ‘yan takarar gwamna da na mataimakan su da kuma sunayen ‘yan takarar majalisun dokoki, waɗanda za a rufe karɓar su a ranar 15 ga Yuli.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya yi wannan gargaɗin a lokacin da ya ke ganawa da Kwamishinonin Zaɓe na Tarayya a ranar Alhamis a Abuja.
Yakubu ya tunatar da su cewa an kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani na dukkan jam’iyyun da za su shiga takarar zaɓen 2023 tun a ranar 9 ga Yuni.
Ya ce: “INEC na buƙatar a damƙa mata sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa da na sanatoci da membobin Majalisar Tarayya daga ranar 10 ga Yuni zuwa Juma’a, 17 ga Yuni.
“INEC na buƙatar sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakin sa da sunayen ‘yan majalisar dokoki daga ranar 1 ga Yuli zuwa 15 ga Yuli.
“Za a loda sunayen ne a cikin rumbun tattara sunayen ‘yan takarar zaɓen 2023 na intanet, wato ‘portal’.”
Yakubu ya ƙara da cewa INEC na buƙatar jami’ai huɗu na daga cikin kowace jam’iyya 18 da za su yi takara su loda sunan ɗan takarar su a cikin rumbun tattara sunayen.
Ya ce tuni INEC ta damƙa wa kowace jam’iyya lambobin ɗan makullin da ake buɗe rumbun da su domin su shiga su loda sunayen ‘yan takarar su.
“Mu na ƙara jaddada cewa sai sunayen ‘yan takarar da su ka yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani bisa tsarin da Sashe na 84 na Dokar Zaɓe ta 2023 ne kaɗai za a loda sunayen su a cikin rumbun,” inji shi.