A DAIDAI lokacin da saura kwana 66 ya rage a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Dattawa, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar sa za ta yi amfani da motocin sufuri 100,000 da jiragen ruwa 4,200 domin raba ma’aikata da kuma kayan zaɓen shekarar 2023.
Yakubu ya bayyana haka ne a lokacin wani ƙwarya-ƙwaryan taron rattaba hannu kan yarjejeniyar da INEC ta cimmawa tare da ƙungiyoyin motocin sufuri da na jiragen ruwa, ranar Talata a Abuja.
Ya ce INEC za ta yi amfani da su ne domin tabbatar da cewa karakainar raba kayan zaɓe da jami’an zaɓe bai samu wata tangarɗa kafin ranar zaɓe da kuma ranar zaɓen ba.
Shugabannin ƙungiyoyin sufurin da INEC ta ƙulla yarjejeniyar da su uku ne, da su ka haɗa da ƙungiyar direbobi ta NURTW, Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri, wato NARTO, da kuma Ƙungiyar Ma’aikatan Jiragen Ruwa (MWUN).
Ya ce: ,”INEC za ta yi amfani da motoci 100,000, jiragen ruwa 4,200 da kuma ma’aikatan zaɓe miliyan ɗaya.
“Hakan ne ya sa mu ka ƙulla wannan yarjejeniya da ƙungiyoyin sufuri uku domin tabbatar da komai ya tafi daidai a cikin nasara, kamar yadda aka tsara.

“Waɗannan motoci da jiragen ruwa za su yi karakainar ɗaukar jami’an zaɓe da kayan zaɓe sau biyu kenan a lokacin zaɓen ranar 25 ga Fabrairu da kuma ranar 11 ga Maris, 2023. Za su yi aikin zirga-zirgar kai kayan zaɓe da jami’an zaɓe a dukkanin ƙananan hukumomi 774, mazaɓu 8,809 da kuma rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin ƙasar nan.
“Za a riƙa yi wa jiragen ruwan da ke ɗauke da kayan aiki kariya da samun rakiyar sojoji ɗauke da makamai a cikin ƙananan jiragen ruwa na yaƙi.”
Yakubu ya ba da tabbacin cewa tun ƙarfe 8:30 na safiyar 25 ga Fabrairu, 2023 jami’an zaɓe za su fito domin fara tantance masu jefa ƙuri’a. Sannan kuma ya ce baya ga motoci da jiragen ruwa, INEC za ta yi amfani da Keke NAPEP da babura domin isar da kayan aikin zaɓe cikin kowane lungu.
Daga nan ya umarci shugabannin ƙungiyoyin motocin sufurin su sani cewa wannan yarjejeniyar da su ka sa hannu, tamkar rantsuwa ce cewa ba za su aikata ba daidai ba.
Ya ce su ja kunnen direbobin su kada su nuna son kai ko fifita wani ɗan takara ko wata jam’iyya. Kuma kada su haɗa kai da jami’an tsaron da za a riƙa haɗa su aikin kariya da tsaro su yi amfani da kayan zaɓe ta hanyar da ba ta dace ba.
Shugaban NURTW, Tajuddeen Baruwa, ya tabbatar wa INEC cewa wannan yarjejeniyar da su ka sa wa hannu sun amince alƙawari ne cewa za su yi aiki tsakani da Allah domin bai wa ƙasar su gudummawar tabbatar da an gudanar da zaɓuɓɓukan 2023 cikin kwanciyar hankali.