YANZU mako biyu tun bayan da Gwamnatin Jihar Kano ta naɗa fitaccen mawaƙi Tijjani Hussaini Gandu a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kano kan Harkar Wallafa. Wannan shi ne karo na farko da aka taɓa yin muƙamin a tsarin tafiyar da gwamnatin Kano.
Mujallar Fim ta tattauna da Tijjani Gandu domin jin matsayin ofishin nasa da kuma ayyukan da zai riƙa gudanarwa, kamar haka:
FIM: Ka na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa a fagen siyasa a ƙasar nan kuma a ‘yan kwanakin nan aka naɗa ka a matsayin babban mataimaki ga Gwamnan Kano kan harkar wallafa. Mu na son ka yi wa masu karatun mu ƙarin bayani a game da wannan muƙami.
TIJJANI GANDU: To, alhamdu lillahi, haka ne, mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba ni matsayi na babban mataimaki na musamman kan harkar mawallafa. Wannan shi ne muƙamin da aka ba ni.
Idan aka ce “wallafa”, ta na da faɗi. Akwai waƙoƙin baka da na rubutu da littattafai, jaridu da waƙoƙin yabon Manzon Allah, da dai sauran abubuwa na wallafa masu yawa.
FIM: Kai a wanne ɓangare muƙamin ka ya tsaya?
TIJJANI GANDU: In dai a Kano ka ke ka na harkar wallafa, to a ƙarƙashin ofishi na ka ke; da ita waƙa, da labarai na soyayya da hikayoyi da tatsuniyoyi, da duk wani abu da ya shafi wallafa, to ni wakilin su ne a wajen mai girma gwamna.
FIM: To yaya tsarin gudanarwar ofishin ka zai kasance ta hanyar aiki?
TIJJANI GANDU: Na farko, ilmintar da mawallafa, musamman waɗanda ba su yi suna ba a cikin harkar, kuma su ke so su yi suna, don ana samun da yawa ba su da ilimin abin, don haka mu na son gwamnati ta yi mana gatan da za ta ba da wata dama da kowanne mawallafi zai je ya yi karatu ko da a ɓangaren sa ne ta yadda zai samu shaidar ya yi karatu a fannin sana’ar sa, da kuma wasu abubuwa da za mu fito da su na tsaftacewa da gyarawa a kan wannan harkoki namu na wallafa. Don idan ka duba, idan na ce gyara akwai waƙoƙin da bai dace a ce Hausawa ne su ke ji ko su ke wallafa wannan waƙoƙin. To dole in dai mu ka samu dama irin waɗannan abubuwan da ake yi da ba su dace ba, za mu ba da shawara ga masu yi su daina, idan kuma ba su daina ba, sai mu haɗa su da hukumar da za ta hukunta su a kan wannan aikace-aikacen nasu na ba daidai ba. A dunƙule dai mu na son mu kawo wa harkar cigaba ne, yadda ko da bayan mun gama namu, ko bayan ran mu, abin zai ɗore, na baya su ci gajiyar sa.
A yanzu an samu wani yanayi yadda harkar waƙoƙin siyasar da na soyayya da ma na yabon Manzon Allah kowanne ɓangare ana yin ƙorafin shigar da abubuwan da ba su dace ba.
To kowanne ɓangare kamar yadda mu ka tsara za mu zauna da kowace ƙungiya, kamar ɓangaren yabo su na da shugabanci, masu harkar hip hop su na da shugabanci, idan ma ba su da shi za mu sa su yi; duk za mu zauna da su, mu faɗa masu ga dama da mu ka samu, kuma su ba mu haɗin kai domin a gudu tare a tsira tare.

FIM: A yanzu da ya ke lokaci ne na soshiyal midiya za ka ga wasu waƙoƙin mutum ne shi kadai zai zauna a ɗaki ya shirya ya faɗi duk abin da ya ga dama na cin mutunci ya tura a soshiyal midiya. Wanne mataki za ku ɗauka a kan irin waɗannan?
TIJJANI GANDU: Duk dai maganar gyaran ce. Kamar yadda na faɗa a baya, ko da ba ka cikin ƙungiya, kai kaɗai a ware ka je ka yi waƙa ta rashin ɗa’a, in dai a Kano ka ke, ko kuma kai ɗan Kano ne ka fita wani waje ka yi ka ke turowa, to mu na da hanyar da za mu je mu same ka mu ja maka kunne, idan kuma ka ƙi ji, to sai mu haɗa ka da inda ya dace domin ɗaukar mataki a kan ka.
FIM: Ita harkar fasaha baiwa ce wadda da dama a yanzu ba masu baiwar ba ne, kawai dai ana yi mata taka-haye saboda ana samun kuɗi. Ta yaya za ku magance kwararowar mutane cikin ta a irin wannan yanayin?
TIJJANI GANDU: To akwai shirin da mu ke da shi na shirya taruka na ƙara wa juna sani da kuma taron sanin makamar aiki da su ƙungiyoyin. To a wannan za mu jawo masana da su ka san muhimmancin wallafa da baiwar don a sanar da mutane idan ka samu kan ka a cikin masu wannan baiwar don ya zamana ka iya tafiyar da kan ka, kada a yi ta zama barkatai, kowa ya na yin abin da ya ga dama; ta yiwu Allah ya bai wa mutum dama bai sani ba. Don haka za mu nusar da mutane cewa idan Allah ya ba ka dama sai ka yi amfani da ita.
FIM: Harkar ku ta waƙar siyasa a nan ake ganin ya fi muni wajen cin mutunci da zage-zage da kalamai dai na zafafawa. Ko wanne irin mataki za ku ɗauka?
TIJJANI GANDU: To ita waƙar siyasa ba ka raba ta da zambo, kuma shi zambo a waƙar siyasa za a iya cewa halas ne. To amma cin mutunci bai zama halas ba. Don haka masu cin mutuncin mutane a wannan gwamnatin in Allah ya yarda ba za mu yarda da wannan ba, za mu ɗauki mataki a kan su. Ko kuma za mu sa a ɗauki mataki a kan su matuƙar su ka ci gaba da yin wannan cin mutuncin. Don haka abin da zan faɗa ga su mawallafa, kowa ya yi ƙoƙari ya shiga ƙungiya; idan ɓangaren yabo ka ke ka samu ƙungiyar yabo ka shiga, idan ɓangaren soyayya ka ke ko waƙoƙin siyasa, dole ya zama ka na cikin ƙungiya dai ta mawaƙa. Masu rubuce-rubuce na san su na da ƙungiya. An fi samun matsala a wajen mawaƙa, don haka duk wanda ba shi da ƙungiya sai ya yi ƙoƙari ya yi, domin idan aiki ya zo, ba wai da ɗaiɗaikun mutane za a yi ba, za a yi ne ta ƙarƙashin ƙungiya, kuma za mu rinƙa bibiyar su don gwamnati ta san da zaman su, abin da ya kama na taimako gwamnati ta yi masu.
FIM: Ko akwai sabunta rajistar ƙungiyoyin mawallafa da ofishin ka zai yi a nan gaba?
TIJJANI GANDU: E, akwai wannan, don mu na son mu sabunta rajista, da kuma yunƙurin faɗaɗa ƙungiyar a ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano. Wannan ina yin magana ne ga ƙungiyar mawaƙa, amma sauran ƙungiyoyi ba mu ne mu ke da hurumin yin hakan ba, mu dai idan su ka zo mana a ƙungiyance za mu karɓe su, kuma abin da ya kama na gyara za mu yi masu.
FIM: To su ƙungiyoyin mawallafa za su zauna a inuwar ƙungiya ɗaya ne kamar yadda a ɓangaren ‘yan fim su ke da wannan tsarin?
TIJJANI GANDU: E to, ba mu zo da wannan ba, amma dai mu na son mu zama a dunƙule. Ka san ana yin wakilci, don haka duk wani mai harkar wallafa a yanzu ni ne wakilin sa a gwamnatin Jihar Kano, ta ƙarƙashin ofishi na za a rinƙa gudanar da wannan tsarin da ya shafi harkar wallafa. Don ka ga idan ka ɗauke ƙungiyar marubuta littattafai da ta mawallafa waƙoƙi a cikin mu dai in ban da ƙungiyar mu ta mawaƙan Kwankwasiyya ba na jin akwai wata ƙungiya ta mawaƙa ta ƙasa da ta ke da rajista. Saboda haka ta ƙarƙashin ofis ɗi na ne waɗannan ayyuka za su rinƙa fita. Don haka kowa ya mayar da hankali wajen neman ilimi, da kuma ɗaukar abubuwan da su ke da muhimmanci.
FIM: To madalla, mun gode.
TIJJANI GANDU: Ni ma na gode sosai.