JARUMI kuma mawaƙi a Kannywood, Yusuf Haruna (Baban Chinedu), ya ƙaryata wata takarda da ke yawo a soshiyal midiya da ke ɗauke da cewa gwamnatin Jihar Katsina ta ba da umarnin a ba su kyautar naira miliyan tamanin (N80,000,000) shi da mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi (Rarara).
Takardar ta nuna cewa an ba su kuɗin ne domin a rage masu raɗaɗin ɓarnar da aka yi masu a Kano a ranar da Abba Kabir Yusuf ya lashe zaɓen Jihar Kano a matsayin gwamna.
Jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai da dama sun yaɗa labarai kan takardar ba tare da sun ji ta bakin Rarara da Baban Chinedu ba.
To amma a cikin wani bidiyo da mai taimaka wa Rarara a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya wallafa a Instagram da Facebook, Baban Chinedu ya yi zazzafan martani, ya ce, “Akwai wani abu da na ga an rubuta, wai Gwamnatin Tarayya ta ba Rara da Baban Chinedu gudunmawar N500,000,000. Zan fara da wannan kafin in je na ‘yan kama su kuma da su ka yi nasu na Katsina.”
Ya ci gaba da cewa, “To na taɓa faɗi, na ce a cikin gwamnatin mai girma Shugaban Ƙasa Janar Muhammadu Buhari, idan akwai wani minista da na je gidan shi ko na buga masa waya na ce ina neman taimako ko gida na yi suna, in ya rufa min asiri, shi Allah ya tona masa asiri.
“Sannan a cikin gwamnatin mai girma Shugaban Ƙasa Janar Muhammadu Buhari, idan akwai wanda ya taɓa kira na ya taimake ni da N200,000, duka ministocin fa, ban cire kowa ba, ban da mai girma Hadi Sirika, saboda shi akwai hulɗa da ta haɗa mu da shi tun lokacin siyasa, kuma ya ɗaukar min ma’aikata, tunda shi mutun ne wanda mu na da alaƙa tsakanin mu; sai state minister ta Abuja, ita ma aiki ne ta ba ni na yi mata, sai Timi Sylver, shi ma ya taɓa ba ni aiki na yi masa; in ka cire wannan mutum biyu, duk wani minista da ke cikin gwamnatin Janar Muhammadu Buhari, wanda ni Baban Chinedu ya taɓa taimako na da N100,000, in ya rufa min asiri, shi kuma Allah ya tona asirin sa duniya da lahira.
“Jama’a, wanda ya rubuta an ba mu N500,000,000 da Federal Government, wannan maganar ƙarya ne.
“Mai girma shugaban ƙasa akwai girmamawa tsakani na da shi, wato mutanen da ke tare da shi, mutane ne wanda sai dai Allah ya kiyaye kawai. Gwamnati dai ta zo ƙarshe, ban son magana, duk da dai na kan yi magana a baya. Amma duk wanda ya ce Gwamnatin Tarayya ta taimake mu a kan abin da ya same mu, ƙarya ne.”
Baban Chinedu ya ci gaba da cewa, “Sai kuma magana na biyu, wanda shi kuma yanzu na gani, wancan na kwana biyu da ganin shi, da gaba ɗaya na ce na daina magana a kan wannan, tunda kwanaki an rubuta mota da gida an ce gwamnan Katsina ya ba Rara, ya ba ni, na zo na ƙaryata, duk da wasu su na yi ne don kada a taimake mu, wanda su ke da niyyar taimakon namu, in Allah ya taimake ka ai babu wanda ya isa ya hana a taimake ka.”
Ya ce, “To yanzu kuma wannan takarda shi kuma, wai gwamnatin Jihar Katsina, duk da dai ban ga sunan gwamnan ba, amma ina tunanin ko gwamnan ne ake so a ɓata wa suna, a’a ko kuma mu ne ake so kada mu samu wani abu, to yaushe ne za a taimake ka in ba a taimake ka yanzu ba? Ana so a tare taimakon ne don kada a taimake mu ko ana so ne a ɓata wa gwamna suna? Ni na kasa gane abin. In don ta ni ne ba zan yi magana ba, saboda na gaji da magana a kan irin wannan abin. A yi maka ƙarya a soshiyal midiya, wannan ya zama ruwan dare a Nijeriya.
“Ake yi wa malamai ma, balle ɗan dirama?! Kai da ka ke fim. Sai mu yi ta ganin ƙarya ana yi mana. Ni in don ta ni ne wallahi sai in bar wannan abin. Amma tunda akwai maganganu da na ke so in yi zan haɗa da shi.”
Baban Chinedu ya karanto takardar, ya ce, “An rubuta wai gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin ofishin akanta-janar ne, wani ya rubuta a ba Rara N50,000,000, Baban Chinedu a ba shi N30,000,000.
“Kai, oh God, Nijeriya! Wai wannan abin ma a gaske ne, ban cancanta ba ne in ma da gaske ne? Ai na kai matakin da na cancanta a yi mini ɗin, in gaske ne. Balle kuma ƙaryar banza ne. Ana yi ne don a ɓata wa gwamna mai tafiya suna, ko kuma a yi mana baƙin ciki kada wasu su taimake mu. Matsiyatan banza, matsiyatan wofi! In Allah ya taimake ka, wallahi babu wanda iya isa ya hana a taimake ka.
“Shi mai girma gwamnan Jihar Katsina mu na girmama shi, ba ya mana ƙarya, ba zai kalle ka ya yi maka ƙarya ba wallahi. Bai taɓa yi mana alƙawarin zai ba ni kuɗi ba, balle mu sa rai ma ya yi mana ƙarya. Amma ya turo an yi mana gaisuwa, kuma mutum ne wanda a baya ya taimake mu, duk mutumin da a sana’ar ka ma zai kira ka ka zo ka yi kaza ya biya ka, ai ya taimake ka. Ya na ɗaya daga cikin gwamnonin da mu ke girmamawa, don shi uba ne ma a wurin mu. So, in na ga abin da za a ɓata masa suna I will talk.
“Kuma in ma abin ma da gaske ne, idan wani matsala ya samu ɗan jiha, ya na da dama ya rubuta ya nemi taimako, to ku ɗauko takardar da mu ka rubuta mu na neman taimakon mana ku ce ga shi, ko wanda gwamna ya yi ‘approving’ da kan shi ya ce a ba da. Sai wanda za ku ƙirƙira ku yi ‘typing’, ku ce wai akanta-janar ya ce a ba da N30,000,000, ko N40,000,000, a ba mutane. Sakarcin banza!
“To wai in ka ce a ba Rara N50,000,000, ka san nawa ya yi asara? Ya yi asarar fiye da N800,000,000, ka ce a ba shi N50,000,000, wai kuma ka burge ne? Rubbish!
“Ka san nawa ne ni na yi asara? Ka je ka duba inda aka ɗauki kayan mu, aka kwashe mini, ka je ka tambayi nawa na yi asara.
“So, mai girma gwamnan Jihar Katsina ka yi haƙuri, ba wai mu na faɗa da kai ba ne ko mu na cewa ba ka isa ba, ƙaryar ne mu ka ga ya yi yawa, don a kan ka aka fi mana, a je a ce ka ba mu gida, ka ba mu mota, ka ba mu waye. Ana yi don a ɓata ko za a hana mana neman abinci.
“Ka yi haƙuri mai girma gwamna, dole mu fito mu yi magana idan mun ga abin da aka yi mana an yi ƙarya da gwamnatin ka. Amma mu in ma an yi hakan in da gaske ne ma mun cancanta, mun kai matakin a yi mana, aka yi ma banza wanda ba su kai wannan ba ma a gwamnatance ana zuwa a yi masu. Amma har wani ya ɗauki takarda ya na sakawa a Facebook, rubbish! Wallahi tallahi ina da kuɗi da kadarar da sun fi abin da aka rubuta a wannan takardar.”