• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiya ta shirya wa Kanawa zalla gasar rubuta waƙa kan illar fyaɗe

by DAGA IRO MAMMAN
January 12, 2022
in Marubuta
0
Ƙungiya ta shirya wa Kanawa zalla gasar rubuta waƙa kan illar fyaɗe
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Gamayyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa, reshen Jihar Kano, ta shirya wa marubutan da ke jihar gasar rubuta waƙar Hausa a kan illar fyaɗe.

A yayin da ya ke bayyana fasalin duk waƙar da za a shiga gasar da ita, jam’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Yasir Kallah, ya ce tilas ne a yi wa ƙasidar da za a shiga gasar da ita take da, “Jigo: Illolin Fyaɗe da Yadda Za A Magance Shi”.

Haka kuma ana so baitin waƙar ya kama daga 10 zuwa 15.

Bugu da ƙari, a sanarwar ta Yasir wadda mujallar ta gani, an ce ana so zubi da tsarin waƙar ya kasance mai ƙwar uku ce, wato Salasiyya, ko ƙwar huɗu, Ruba’iyya.

Yasir ya bayyana cewa za a duba ƙa’idojin rubutun Hausa, sannan ana so kowane sha’iri ya sanya lambar wayar sa da adireshin unguwa da garin da ya ke a takardar sa ta shiga gasar.

“Sannan ba a yarda wani ya rubuta wa wani ba; kowa tasa ta fisshe shi!” inji shi.

Wata ƙa’idar ita ce idan an kammala rubutawa sai a tura ga lambar Whastapp kamar haka 08060651676.

Jami’in ya ce za a rufe shiga gasar a ranar 28 ga Fabrairu, 2022.

Ya yi gargaɗin cewa saɓa wa ɗaya daga cikin ƙa’idojin da aka gindaya na iya sabbaba cire mawaƙi daga gasar.

Kuma ya ce: “Akwai takardun shaida da kyaututtuka na musamman ga zakarun gasar.”

A cewar Yasir, ƙungiyar za ta riƙa shirya irin wannan gasar a duk bayan wata uku.

“Kuma gasar ta ‘yan Kano ce zalla,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa, “Dukkanin wasu karin bayanai da sanarwa a kan gasar a duba shafin ƙungiyar na Facebook.”

Loading

Tags: Adabin HausaƘungiyar Gamayyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausamarubutan Kanorubutacciyar waƙawaƙaYasir Kallah
Previous Post

Minista Sadiya ta jajanta wa ‘yan kasuwar Guru da gobara ta yi wa ɓarna

Next Post

‘Yan Kannywood za su yi taron addu’a ga mamata a ranar Juma’a

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Alhaji Kabiru Maikaba

'Yan Kannywood za su yi taron addu’a ga mamata a ranar Juma’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!