HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana furodusa a Kannywood kuma marubucin Hausa, Malam Zubairu Musa Balannaji, a matsayin gwarzon gasar ta ta rubuta gajerun labarai ta shekarar 2024.
Da take bayyana sakamakon gasar a ɗakin taro na Malam Aminu Kano da ke Gidan Mambayya, Farfesa Halima Abdulƙadir Ɗangambo ta Jami’ar Bayero, Kano, wanda shugaban kwamitin gasar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana a madadin ta, ta bayyana labarin ‘Bahaushiyar Al’ada’, wanda Balannaji ɗin ya rubuta, a matsayin wanda ya zo na ɗaya cikin labarai 50 da suka fafata a gasar.
Haka kuma, ta bayyana labarin ‘Gadon Gida Sai Da Horo’ na Ɗanladi Haruna (Zakariyya) a matsayin na biyu.
Labari mai taken ‘Bahaushe Mai Arziki Ne’ na Hauwa Shehu shi ne na uku.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-mustapha, a cikin jawabin sa a taron, ya bayyana farin ciki kan yadda gasar ta gudana tare da taya zakarun murna.
A jawabin sa na godiya, Balannaji ya gode wa Allah tare nuna farin ciki dangane da wannan gagarumar nasara da ya yi na zama na farko cikin tarin marubutan da suka shiga gasar
Hukumar ta ba Balannaji kyautar N500,000; na biyu N300,000, a yayin da ta uku ta samu N200,000.
Taron ya yi armashi. Ya samu halartar marubuta da jami’an gwamnati da sauran jama’a.
![]()







