Hauwa Shehu tana ɗaya daga cikin marubutan hikaya da suke sahun gaba a soshiyal midiya.
Ta yi rubuce-rubuce masu yawa waɗanda aka buga a littafi da kuma na onlayin. Ta shiga gasannin rubutu da dama. Hasali ma dai, ita zakare ce a gasannin rubutu da ɗan dama; ita ce ta zo ɗaya a Gasar Rubutu ta Gusau Institute da aka yi a 2023, sannan ta zo ta uku a gasar marubuta ta Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da aka gudanar a bara.
Mujallar Fim ta tattauna da ita domin jin yadda ta fara rubutu da irin damar da ta samu a cikin harkar.
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.
HAUWA SHEHU: Suna na Hauwa Shehu. Ni ‘yar asalin Jihar Kano ce. Na yi makarantar firamare da ƙaramar makarantar sakandare (JSS) a nan Jihar Kano, babbar sakandare (SSS) kuma a Jihar Kaduna.
Na samu zarafin kammala digiri na farko a fannin koyar da ilimin lissafi, Bsc. Ed. Mathematics.
FIM: Ya aka yi kika samu kan ki a cikin harkar rubutu?
HAUWA SHEHU: Na samu kai na da sha’awar harkar rubutu tun daga makarantar firamare a lokacin da na fahimci zan iya kai koke na ta hanyar jera kalmomi a takarda ba tare da na furta su da baki ba. Daga nan na fahimci rubutu babbar hanya ce ta isar da saƙo, ilimantarwa, faɗakarwa tare da nuni cikin nishaɗi. Daga lokacin na fara gwada alƙalami na.
FIM: A wace shekarar kika fara rubuta littafi?
HAUWA SHEHU: A shekarar 2009 bayan kammala sakandare a lokacin ina zaman jiran sakamako. ‘Shukuriyya’ shi ne cikakken labarin da na fara rubutawa.
FIM: Ko kin taɓa buga littafi?
HAUWA SHEHU: E, na taɓa buga littafin ‘Harin Gajimare’, sai kuma ‘Tsanin Tsaro’.

FIM: A shekarar da ta gabata kin shiga gasar marubuta ta Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano inda kika zo ta uku. Ko ita ce farkon gasar da kika fara shiga?
HAUWA SHEHU: Haka ne. A’a, wannan ba shi ne karo na farko da na fara shiga gasa ba, domin a shekarar 2023 na shiga Gasar Gusau Institute kuma cikin ikon Allah ni ce na zo ta ɗaya. Na shiga gasar marubuta guruf, shi ma na zo ta huɗu da labarin ‘Tukunyar Talaka,’ na kuma shiga gasar Hikayata (inda) labari na na ‘Duniyar Sama’ ya fito a cikin jerin waɗanda suka cancanci yabo.
FIM: Wanne buri kike da shi a kan harkar rubutu?
HAUWA SHEHU: Buri na shi ne saƙonni da suke ƙunshe a rubutu na su kasance masu tasiri ga al’umma. Ina son na zama marubuciyar da ko bayan rai na za a rinƙa tunawa da saƙonnin da na isar.
FIM: Waɗanne matsaloli ne marubuta suke fuskanta a wannan lokacin?
HAUWA SHEHU: A gani na, matsalolin da marubuta suke fuskanta a wannan zamani bai wuce ƙarancin tallafi da kuma ƙarancin fahimtar hanyoyin da za su bunƙasa basirar su da yadda za su ɗaga darajar baiwar su har su ci gajiyar ta ba.

FIM: Wanne kira za ki yi ga marubuta?
HAUWA SHEHU: Kiran da zan yi ga marubuta shi ne su rungumi sauyin da zamani ya zo da shi, ba tare da sun manta da ainihin darajar da alƙalamin su ke ƙunshe da shi ba. Sannan su ci gaba da inganta basirar su ta hanyar karatu, bincike da nazari. Ƙari a kan hakan, su tsaftace rubutun su.
FIM: To, madalla, mun gode
HAUWA SHEHU: Ni ma na gode.
![]()







