Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya gudana cikin nasara a ranar 31/12/2025 a garin Dutse, Jihar Jigawa, inda ya haɗa marubuta, manazarta, malamai, ɗalibai, da wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na Nijeriya da maƙwabtan ta. Taron ya ƙara jaddada muhimmancin rubutun Hausa a ƙarni na 21, musamman a fuskokin tsaro, tattalin arziki, al’adu, da ci gaban al’umma.
Muhimman Abubuwan da Taron ya Tattauna
1. Ƙalubalen Tsaro da Al’adar Karatu:
An jaddada cewa duk da ƙalubalen rashin tsaro, akwai babbar matsala ta raguwar al’adar karatu musamman a tsakanin matasa, wadda ke buƙatar tsayuwar daka. An ba da shawarar a fara gyara tunani tun daga makarantu, ta hanyar kafa kulob-kulob na karatu da al’adu, tare da gayyatar marubuta su riƙa yi wa ɗalibai bita kan muhimmancin rubutu da karanta littattafai.
Yadda za a yi amfani da fasahar AI domin gina rubutu mai inganci da kuma sauƙaƙa wa marubuta da amfanin hakan ta fuskar tsaro da tattalin arziki.
2. Zaurukan Tattaunawa (Panels):
- “Rubutun Zube na Hausa a Onlayin: Ina aka dosa?” inda masana suka tattauna muhimmanci da ƙalubalen rubuce-rubucen onlayin, musamman matsalar rubutun batsa.
- “Marubuta Mata a Jiya da Yau: Ina aka dosa?”
- “Rubutun Gajerun Labaran Hausa: Ina aka fito? Ina ake? Ina aka dosa?”
- “Tattaunawar waƙoƙin Hausa.”
- “Rubutun Hausa a wajen ƙasar Hausa”
Waɗannan zauruka sun samar da ilimi mai zurfi da gogewa wadda ke da wahalar samuwa a wuri guda.

3. Halarta da Wakilci:
Taron ya samu halartar marubuta sama da 250 daga faɗin Nijeriya, tare da wakilcin gwamnatocin Arewa musamman Kano, Katsina da Jigawa. Haka kuma, an samu baƙi daga ƙasashen Togo, Kamaru, Senegal da Nijar.
Ƙalubale da Abubuwan da za a Gyara
- An lura cewa Kwamitin Yaɗa Labarai na cikin gida bai samu cikakkiyar dama ba wajen aiwatar da aikin sa kamar yadda ya kamata; an yanke shawarar gyara wannan a taro na gaba.
- An kuma fuskanci matsalar kayan sauti a farkon taron, amma an shawo kan ta; za a ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa irin haka a nan gaba.
- Rashin daratta lokaci ga marubuta, wanda hakan ya haddasa rasa abubuwa da yawa masu muhimmanci. Mutum ya kwana a wajen taron kuma ta dalilin taron ya zo an fada masa za a fara taro karfe 10 amma bai shigo ɗakin taro ba sai ƙarfe 11:24 kuma yana maganar ba a ba shi damar karanta gajeren labari ba.

Abin da taron ya samar
Littafi mai ɗauke da gajerun labarai 27 kan gudunmuwar fasahar AI ga tsaro da tattalin arziki wanda aka ba suna “Ninki Biyu”.
Taron ya samu damar haifar da taron horaswa kan sanin hanyoyi da dabarun yadda ake rubuta buƙatar neman ɗaukar nauyin ko bayar da gudunmuwa daga ƙasashen waje, wadda za a zaɓi marubuta daga jihohi da kuma malaman jami’a a koma Jigawa a Ƙaramar Hukumar Kirikisamma a lokacin bikin Ƙaramar Sallah mai zuwa in-sha Allah. Wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Matasa da Wasanni da Al’adu na Jihar Jigawa zai ɗauki nauyi baki ɗaya za a zaɓi marubuta da ba su gaza 20 ba domin halartar wannan taro na bita.
Haka kuma ana kan tattaunawa mai ƙarfi tsakanin wakilan gwamnatin Jihar Jigawa da Katsina da Jamhuriyar Nijar domin samar da wani bikin baje-koli da marubuta za su taka rawa da zai haɗa Nijeriya da Nijar In sha Allah.
Shugabanci da kuma Jihar da za a yi Taron 2026
Jagororin da suka shirya taron bana wa’adin su ya ƙare ne kan taron na bana. Daga nan zuwa watan Afrilu ake sa ran marubuta su zaɓi waɗanda suke so su jagoranci taron gaba.
Maganar jihar da za a yi taro ita ma ana sa ran daga nan zuwa ƙarshen watan Fabrairu masu buƙata su nuna buƙatar su tare da dalilai masu ƙarfi na iya ɗaukar nauyin taron. Idan ba a samu waɗanda suka nuna buƙatar su ba a rubuce, wannan kwamitin kafin wa’adin sa ya ƙare a watan Afrilu zai bayyana jihar da za a yi taron gaba tare da miƙa ragamar jagorancin ga waɗanda marubuta suka zaɓa domin su jagorance su a taron 2026.
Sannan kwamiti ya amince ya fara raba takardar godiya ga waɗanda suka bayar da gudunmawa a wannan taro daga ranar Litinin, 12/1/2026.
Shawarwari
Ana bada shawara taro na gaba ya zama na kwana biyu domin yin abubuwa da yawa masu muhimmanci.
Ana bayar da shawara ga waɗanda za su jagoranci taron gaba da su kiyaye ƙalubalen da aka samu a wannan taron.
Godiya da Yabo
Taron ya miƙa godiya ta musamman ga dukkan kwamitoci bisa jajircewa da sadaukarwa. Ana jinjina wa manyan malamai da marubuta da suka bayar da gudunmawar su na ganin an yi wannan taro lafiya.
Haka kuma, ana jinjina ta musamman ga wakilan Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Sagir Ahmad Musa da muƙarraban Gwamna Umar Namadi Ɗanmoɗi, bisa irin goyon bayan da suka ba taron da kuma gasar rubutun da suka saka.
Ana kuma yaba wa wakilan Gwamnatin Jihar Katsina bisa rawar da suka taka wajen inganta taron. Jihar Katsina ta bayyana aniyar ta na ɗaukar nauyin taron na gaba, tare da ci gaba da tallafawa idan ba a samu wata jiha da ta ɗauka ba.
Kammalawa
Taron ya tabbatar da cewa rubutun Hausa ginshiƙi ne na gina tunani, tsaro, da tattalin arziki, kuma dole ne a ƙara ƙaimi wajen farfaɗo da al’adar karatu da rubutu, musamman a tsakanin matasa.
An amince da ɗaukar darussa daga ƙalubalen da aka fuskanta domin ƙara inganta taruka na gaba.
An fitar da wannan sanarwa domin amfanin al’umma da masu ruwa da tsaki.
Abdulrahman Aliyu, PhD
A madadin kwamitin shirya Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya 2025
![]()







