ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta miƙa godiya ta musamman ga furodusa a Kannywood kuma mamallakin Makarantar Jammaje, Malam Kabir Musa Jammaje, saboda shirya azuzuwan koyon Turanci kyauta ga membobin ƙungiyar da ya yi.
Jami’in Yaɗa Labarai na MOPPAN, Malam Ibrahim Amarawa, shi ne ya bayyana haka a saƙon godiyar da ƙungiyar ta aika masa.
Ƙungiyar ta ce: “A madadin shugabancin MOPPAN da kuma ɗaukacin al’ummar Kannywood, mun rubuto wannan wasiƙa ne domin bayyana matuƙar godiyar mu bisa gagarumar gudunmawar da ka bayar ta hanyar shirya azuzuwan koyon Turanci kyauta ga membobin mu.”
MOPPAN ta ce abin da Jammaje ya yi wani ƙudiri ne na ƙarfafa jarumai, daraktoci, masu fasaha da duk masu alaƙa da masana’antar, ta ce hakan “abin burgewa ne ƙwarai kuma mai sauya al’amura.”
Ta ƙara da cewa, “A wannan zamani na dunƙulewar duniya, iya Turanci ba fasaha kaɗai ba ce, illa muhimmiyar hanya da ke buɗe ƙofofi zuwa manyan damarmaki, faɗaɗa yawan masu sauraro, da kuma haɗin gwiwar ƙirƙira mai faɗi.
“Wannan sadaukarwa ta gaskiya domin ɗaga martaba da bunƙasa ƙwarewar Kannywood na nuna irin jajircewar ka da kishin ka ga cigaba da bunƙasar masana’antar finafinan mu.
“Ba koyar da harshe kaɗai kake yi ba; kana kuma saka jari ne a makomar da kuma basirar mutane da dama waɗanda su ne ginshiƙin sinimar Hausa.”
MOPPAN ta gode ƙwarai da gaske bisa abin da ta rabon ilimin sa, lokacin sa mai daraja, da kuma kyakkyawar niyyar sa ta ganin wasu sun yi nasara.
“Wannan karamci naka zai bar gagarumin tasiri na dogon lokaci, kuma muna alfahari da samun mutum mai goyon baya da hangen nesa irin naka a cikin al’ummarmu,” inji ta.
Ƙungiyar ta yi fatan Allah ya saka masa da alheri, ya ninka masa lada.
“Muna sa ran ganin kyawawan sauye-sauyen da wannan shiri zai kawo wa masana’antar mu,” inji ta
![]()







