HAUSAWA suka ce tsautsayi ba a sa maka rana. Abin da ya faru ga fitaccen jarumi a Kannywood, Malam Ɗan’azumi Baba (Kamaye) kenan kwanan nan a Kano, wato tsautsayin da ya same shi na karaya a ƙafar sa ta hagu.
Ɗan’azumi Baba Kamaye ya yi bayanin ne a lokacin da wakilin mujallar Fim ya kai masa ziyarar dubiya a gidan sa da ke Cediyar ‘Yangurasa a cikin Birnin Kano.
A cewar sa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 29 ga Yuli, 2026 a kan hanyar sa ta zuwa Ƙofar Famfo kan Titin BUK.
Ya ce: “Bayan sallar magariba ne na fita daga gida na zuwa ofishin darakta Isma’il Khalil Ja’en da ke Ƙofar Famfo. Ina tafiya a kan titin FCE, sai kawai wani mai mashin mai ƙafa uku, Adaidaita Sahun da yake gaba na, ya kauce wa wani rami. Ni kuma ban ankara ba, na zo na buge shi daga baya. A nan na faɗi gefe guda, sai kawai na ga ƙafa ta ta lanƙwashe gefe guda. Tun daga nan na san mai afkuwar ta afku.”
Ya ci gaba da cewa: “Daga nan sai aka ɗauke ni zuwa gidan Sarkin Maɗora. Bayan ya duba ni ne ya ce ɗorin ba zai yiwu ba sai da safe.”


Kamaye ya ce, “Alhamdu lillah, an yi ɗori cikin nasara, ina gida ina ci gaba da samun sauƙi. Kuma ina godiya sosai da dukkan jama’a da suka zo duba ni, da waɗanda suka aiko da saƙo da masu kiran waya.
“Sannan ina godiya ga ƙungiyoyin ‘Tripple R Kannywood’ da ‘Kannywood Family Group’ da ƙungiyar Jadda Garko da suka kawo mini ziyarar dubiya da ba da tallafin su na kuɗi a gare ni.”
![]()







