SHAHARARREN mawaƙin nan, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya yi kira ga al’umma da su guji duk wani abu da zai haifar da saɓani ko rashin jituwa tsakanin Hausawa da Fulani, yana mai cewa ya kamata a ƙarfafa abubuwan da suka haɗa al’ummomin biyu maimakon mayar da hankali kan abubuwan da za su raba su.
Ala ya faɗi hakan ne a wajen wani babban taro na ƙasa wanda Ƙungiyar Raya al’adu da Masarautun Gargajiya, wato Royal Tridiagonal Centre (RTC), ta gudanar da nufin farfaɗo da kyautata alaƙa tsakanin al’ummar Arewa, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar ƙoƙarin haifar da gaba da ƙiyayya tsakanin Hausawa da Fulani.
Taron, wanda aka gudanar a Ɗakin Taro na Rabi’u Musa Kwankwaso da ke Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano.a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, ya mayar da hankali ne kan raya al’adu, kare martabar masarautun gargajiya da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma.
Ƙungiyar ta kuma karrama wasu fitattun mutane da ta ce suna bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya da cigaban al’ummar Hausawa da Arewa baki ɗaya.
Daga cikin fitattun mutanen da aka karrama akwai shahararren mawaƙin nan, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa).
Da yake jawabi bayan karɓar karramawar, Ala ya bayyana farin ciki da godiya ga ƙungiyar bisa zaɓar sa cikin mutanen da ta ga sun cancanci a karrama su saboda gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.
Mawaƙin ya yi kira ga al’umma da su guji duk wani abu da zai haifar da saɓani ko rashin jituwa tsakanin Hausawa da Fulani, yana mai cewa ya kamata a ƙarfafa abubuwan da suka haɗa al’ummomin biyu maimakon mayar da hankali kan abubuwan da za su raba su.

A cewar sa, a halin yanzu Hausawa da Fulani sun kasance al’umma mai kusanci sosai, sakamakon abubuwan da suke da alaƙa da su, ciki har da zama a wuri guda, addini guda da kuma auratayya tsakanin juna.
Ya ƙara jaddada cewa haɗin kai da zaman lafiya su ne ginshiƙan cigaban al’umma, don haka ya kamata shugabanni da masu ruwa da tsaki, da kuma ɗaiɗaikun mutane, su taka rawar gani wajen hana duk wani yunƙuri na raba kan Hausawa da Fulani.
Ala ya ce karramawar ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da amfani da fasahar sa da matsayin sa a cikin al’umma wajen isar da saƙonnin zaman lafiya, haɗin kai da kuma kare al’adun Hausawa.
![]()





