DUK da yake na jima ba na son saka baki a kan harkar da ta shafi masarautar Kano saboda wasu dalilai na auratayya ko na mutuntaka da kuma ganin cewa rigima ce ta cikin gida, ba ta siyasa ba, amma tuni ‘yan siyasa sun yi kutse cikin masarauta sun yi mata ɓarna da abin da su ka ga dama, a yau wajibi ne na ce wani abu bisa wasu dalilai.
Shi dai mulki na Allah ne, Shi ke bayarwa ga Wanda ya ke so kuma Shi ke karɓewa a hannun wanda ya ke so a kuma lokacin da ya so. Tabbas, in Allah zai dawo da Sarki Sanusi II ko waye a gwamnan Kano zai dawo kan karagar sa, in kuma Allah bai nufa ba daga gare Shi ne. Amma babu laifi ga duk masu kira da cewa a maida Sarki Muhammad Sanusi II wannan kira ne da murya mai amon zinare daga masoyan Sarki zuwa gwamna ko masoyan gwamna da mutanen NNPP zuwa mai girma gwamna.
Al’umma na da takaicin rushe masarautu. Babu wanda ba shi da muradin Jihar Kano ta samu cigaba, amma karkasa masarautu don fushi aka yi ba don cigaban yankunan ba. Sannan in aka dubi tsantsar zaluncin da aka yi wa Sarkin Kano Sanusi II hawa-hawa su na rubuce a wajen Allah tun daga ƙwace masa fili a yi shataletalen Gidan Zu, har zuwa raba masa masarauta gida biyar da kuma cire shi daga Gidan Dabo da shigar masa da mazajen tasha da jami’an tsaro cikin gida da kuma ɗaukar sa ya na azumi zuwa garin Awe ba tare da ya sha ruwa ba har ƙarfe ukun dare, ana tafe da shi har Abuja da jami’an tsaro da komi sai ka ce mai laifi, daga nan kuma aka shiga mota zuwa Jihar Nassarawa aka tafi Loko, kawai saboda ya ce wanda ya ci zaɓe a ba shi abin sa kuma ya karɓi baƙuncin ’yan Kwankwasiyya a fadar sa.
In da Sarki ya narke a cikin gwamnatin da ya shuɗe, ba ya gaya mata gaskiya cewa kar ta ciyo ba shi ta yi jirgin ƙasa, da kuma biye musu a kan yaƙar Kwankwasiyya, da babu abin da zai taɓa rawanin sa. To, amma tsayawar sa a kan gaskiya ya sa duk aka yi masa komai. To, amma Allah ya na sane kuma wallahi Allah ba zai bari ba.

Sannan kafin wannan sai da aka yi yunkurin ɓata masa suna da ‘yan anti-corruption duk dai don a muzanta shi. To, yau in Sarki ya tafi, ita ma gwamnatin da ta yi ɓarar ta shuɗe, kuma alhakin zaluncin da su ka yi wa Sarki ya na cikin sakamakon da su ke gani a yanzu.
Babu shakka, mutane ba za su manta da alkhairan da su ka amfana da su a zamanin mulkin Mai Martaba Sarki Sanusi II ba tun daga taimako wajen ciyarwa da ɗaukar nauyin marasa lafiya da ɗaukar nauyin karatu, zuwa taimakon gidan gajiyayyu da masu yoyon fitsari. Ita kan ta gwamnatin baya ta yi amfani da Sarki an kawo ‘yan Chaina sun zuba hannun jari.
Allah ya halicci zuciya da son mai faranta mata, kuma Khairun Nass man yanfa’un Nass. Mutane ba za su daina begen Sarki Sanusi II ba. Jagora ne tsayayye kuma jajirtacce, Sarki kuma malami, ga shi limami kuma masanin tattalin arziki. Har yau da shi ake rufe ƙofa wajen inganta tattalin arzikin duniya ba a Nijeriya kawai ba. A duk faɗin Afirka sunan sa ya yi shuhura. Allah ya ba shi ilimi tare da basira. Kadara ne babba ga al’umma.
Wajibi ne mutane su yi kewar Sarki Sanusi saboda dubun alheran sa da su ka kewaye su. Ko da kuwa maƙiyan sa sun shaida cewa shi karimi ne, bare kuma masoyan sa.
Don haka mutane babu laifi su yi ta kiraye-kiraye zuwa ga gai girma Gwamna duk da cewa babu wata gwamnati da za ta iya rama wa Sarki irin wannan ƙasƙanci da aka yi masa, sai dai ta rage masa raɗaɗin wannan rauni.
In har mai girma Gwamna Abba Kabir ya dubi maganar Madugun mu mai girma Excellency Dakta Rabi’u Kwankwaso ya waiwayi masarautu, to duk abin da Gwamna zai yi gyara ne, ba laifi ba ne, domin kuwa gwamnatin baya ta riga ta yi ɓarna a tarihin masarauta. Babu wani mai adalci da zai ga an kasa wa uba gidan sa gida biyar da ran sa a ba wa ɗan gida da agola, sannan a fitar da uban da ƙarfin son zuciya da ƙasƙanci sannan kuma a ce kar a yi kira da a gyara wannan ɓarnar. To, menene amfanin kitso da kwarkwata?
Na san babu wani abin da masoyan gwamnatin baya ba za su iya cewa ba a game da masarauta a yanzu, in dai an yanka riga ai hawa a ɗinke ta shi ne daidai!
In Allah ya amsa addu’ar mahaifiyar mai girma Gwamna ya dawo da Sarki Sanusi II Gidan Dabo, sai dai mu yi addu’ar Allah ya ba shi ikon ɗorawa daga ayyukan alherin da ya saba yi domin kuwa barin sa Kano ma babu abin da ya fasa sai ma ƙari.
Masoya masu yi wa Sarki fatan alheri ku ma ina muku albishir cewa alheri yana tafe ga Sarki. Cikin addu’o’in ku Allah ya amsa ya yi masa Khalifan Tijjaniyya, saboda haka duk abin da Allah ya rubuta kuma ya kawo wa Sarki, to addu’ar ku ce ta yi tasiri.
Allah ya zama gatan Kano da Kanawa. Allah ya tabbatar wa da Sarki Sanusi II da alheri.